Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Alhamis 14//05/2026

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba, da Usman Minjibir da Aisha Babangida

  1. Jami'an kwastam biyu sun mutu a fafatawa da Lakurawa

    Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi

    Asalin hoton, Nigeria Customs Service/Facebook

    Jami'an hukumar kwastam biyu sun rasa ransu a fafatawar da suka yi da mayaƙan da ake zargi Lakurawa ne a jihar Kebbi.

    Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adeniyi, ya ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'an masu muƙamin ASC da DSC, sun rasa ransu ne yayin samamen yaƙi da ƴan ta'adda da tsakiyar dare.

    Adeniyi ya faɗi hakan ne a birnin Illorin yayin da yake gabatar da jawabi a jami'ar Illorin da ke jihar Kwara.

    Rahotanni sun ce maharan sun farwa shingen binciken ababen hawa na tsaro da ke kusa da juna.

    A nan ne kuma suka harbi jami'i guda sannan suka cinna wa ɗaya jami'in wuta da ransa.

    Gwamnan jihar Kwara, AbdurRahman AbdulRazaq ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga hukumar ta kwastam kan mutuwar jami'an biyu inda ya bayyana su a matsayin ƴan kishin ƙasa da suka rasa ransu yayin hidimta wa ƙasarsu.

  2. Indiya ta gargaɗi duniya kan rikice-rikicen da ke girgiza tattalin arziki

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen BRICS ciki har da Iran da Rasha sun gana a birnin New Delhi na ƙasar Indiya, inda gwamnatin Indiya ta bayyana damuwa kan yadda rikice-rikice ke ƙara jefa duniya cikin rashin tabbas a tattalin arziki da harkokin makamashi.

    Yaƙin Iran da matsalar man fetur da ta biyo baya sun mamaye muhawarar taron na kwanaki biyu.

    A jawabin buɗe taron, ministan harkokin wajen Indiya, Subrahmanyam Jaishankar, ya ce duniya na cikin wani yanayi mai cike da sauye-sauye da tashin hankali a dangantakar ƙasa da ƙasa.

    Ya ce rikice-rikice, matsalolin tattalin arziki, ƙalubalen kasuwanci da fasaha, da kuma sauyin yanayi na ci gaba da sauya tsarin duniya.

    Jaishankar ya ƙara da cewa ƙasashe masu tasowa na sa ran BRICS za ta taimaka wajen samar da kwanciyar hankali da daidaito a duniya.

    Haka kuma ya ce ƙasashe da dama har yanzu na fuskantar matsaloli da suka haɗa da tsaron makamashi, samar da abinci da taki, harkokin lafiya da kuma samun kuɗaɗen tallafi.

  3. Ya kamata Amurka da China su zama abokan hulɗa ba na hamayya ba - Xi Jinping

    Shugaba Trump da Xi Jinping

    Asalin hoton, VGC via Getty Images

    Shugaba Xi Jinping na China ya shaida wa Donald Trump cewa, kamata ya yi ƙasashensu su kasance abokan hulɗa, ba abokan hamayya ba, a farkon tattaunawar shugabannin biyu a birnin Beijing.

    Shugaba Trump ya ce a yanzu dangantakar da ke tsakanin manyan ƙasashen biyu za ta inganta fiye da kowane lokaci a tarihi.

    Ya ce abin da mutane ba su sani ba shi ne duk lokacin da aka samu matsala muna warware ta cikin sauƙi kuma za mu ci gaba da tabbatar da danƙon zumuncin da ke tsakanin mu.

    Mista Trump yana tafiya ne tare da wata babbar tawaga da ta ƙunshi manyan jami'an gwamnati da shugabannin kamfanonin fasaha da suka haɗa da Elon Musk da kuma shugaban kamfanin Nvidia Jensen Huang.

  4. Barka da Safiya

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na yi wa ɗumbin masu kasancewa da mu barka da wannan lokaci.

    Da fatan an wayi gari cikin ƙoshin lafiya. Kamar kodayaushe, a yau ma za mu ci gaba da kawo maku rahotanni na abubuwan da suka shafi yaƙin Iran da labaran da suka danganci Najeriya da sauran ƙasashen duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labarai da ma kallon bidiyo.