Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 30/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 30/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Abdullahi Bello, da Umar Mikail

  1. Kano ta tabbatar da ɓullar cutar shan inna

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta tabbatar da gano sababbin nau’o’i guda huɗu na ƙwayar cutar shan inna a jihar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ci gaba da yin rigakafin yadda ya kamata ba, kwayar cutar na iya sake yaɗuwa bayan an kawar da ita.

    Farfesa Salisu Ahmad, wanda Daraktan hukumar ya wakilta ne ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa da jama’a domin tunawa da Ranar Polio ta Duniya a Kano, a ranar Laraba.

    Ya ce tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015, Kano ce cibiyar yaɗuwar cutar a Najeriya, amma sakamakon hadin gwiwar gwamnatin jihar da abokan hulɗa, an samu nasarar kawar da ita.

    Sai dai ya bayyana cewa aikin bai ƙare ba, domin an sake gano sababbin nau’o’i hudu na ƙwayar cutar, inda har yanzu ana binciken ɗaya daga cikinsu a ɗakin gwaje-gwaje.

    Da take bayani kan halin da ake ciki game da cutar shan inna a jihar, Jami’ar Rigakafi ta Jihar, Hajiya Sa’adatu Ibrahim, ta ce an gano sabbin nau’o’i biyu na ƙwayar cutar a wajen yara da ke yankunan karkara, yayin da sauran biyun kuma an gano su ne a cikin ruwan da ya gurɓace a wasu yankuna na birni.

    “Tsabtace muhalli shi kaɗai bai wadatar wajen kawar da cututtukan da ake iya hana su ta rigakafi ba. Dole ne mu ci gaba da tabbatar da cewa ana yi wa ’ya’yanmu allurar rigakafi,” in ji ta.

    “Dole mu kasance cikin shiri don tabbatar da cewa an kawar da cutar shan inna gaba ɗaya,” in ji jami’ar.

  2. Trump ya gana da Shugaba Xi na China

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya bayyana cewa ganawarsu da takwaransa na China Xi Jinping ta kayatar inda ya ce sun cimma matsaya akan abubuwa da dama.

    An fara ganawar ce da gaisuwa sannan kuma sun shafe sa'a ɗaya da mintina 40 suna tattaunawa.

    Da yake mayar da jawabi ga 'yan jarida a yayin da yake ƙoƙarin komawa gida Amurka, Mr Trump ya ce ya cimma yarjejeniyar dagewa China takunkuman da aka kakaba mata akan wasu albarkatun kasar da ba a fiye samunsu ba da ta ke fitar da su zuwa Amurka.

    Ya kuma ce zai ziyarci China a watan Aprilu mai zuwa, sannan kuma shi ma Xi Jinping zai ziyarci Amurkan bayan nan.

    Har yanzu ba a ji komai ba daga wajen China a game da ganawar shugabannin.

  3. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Ku kasance da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.