Daga Umar Mika'il, Aisha Babangida, Khalifa Dokaji da Ahmad Bawage
Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Sai ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na intanet bbchausa.com da kuma shafukan mu na sada zumunta domin sanin yadda za a karkare tsakanin Barca da Inter Milan a wasan daf da karshe na gasar Zakarun Turai zagaye na biyu.
Mu kwana lafiya.
Inter ta farke wasa ya koma 3-3
Asalin hoton, Getty Images
Inter ta farke kwallo - wasa ya koma 3-3.
Ɗan wasan Inter Francesco Acerbi ne ya ci kwallon a ƙarin lokaci - minti na 93.
Yanzu dai an tafi ƙarin lokaci - inda za a buga minti 30 idan babu wanda ya ci sai a je bugun fenariti.
Raphinha ya ci wa Barca kwallo ta uku
Asalin hoton, Getty Images
Raphinha ya ƙara wa Barca kwallo ta uku.
Barca ta yi ƙoƙari wajen farke kwallo biyun da aka ci ta, ta kuma ƙara ɗaya.
Rwanda ta ce an kashe dakarunta uku a harin kwanton-ɓauna
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Rwandan ta ce an kashe dakarun ta uku a wani kwanton-ɓauna da aka yi musu a Mozambique.
Kakakin rundunar ya ce wasu dakarun uku sun samu rauni a harin da aka kai masu a yankin Cabo Delgado ranar Asabar.
Yankin mai albarkatun iskar gas yana yawan fuskantar hari daga ƙungiyar IS a ƴan watannin nan.
Rwanda ta tura dubban sojoji da kuma ƴansanda zuwa Mozambique domin taimakawa ƙasar a yaƙin da take da ƙungiyoyi masu tsattsaurar ra'ayi.
Olmo ya ci wa Barca kwallo ta biyu
Asalin hoton, Getty Images
Dani Olmo ya ci wa Barcelona kwallo ta biyu.
Yanzu dai ana 2-2 a wasan da Barca ɗin take yi da Inter.
Garcia ya farke wa Barca kwallo ɗaya
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta farke kwallo ɗaya a wasan Zakarun Turai da suke fafatawa da Inter.
Eric Garcia ne ya ci kwallon a minti na 54.
Oman ta ce Amurka da Houthi sun ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta
Oman ta sanar da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da mayaƙan Houthi na Yemen.
Ministan harkokin wajen Oman, Badr Albusaidi, ya ce dukkan ɓangarorin sun amince su daina kai wa juna hari.
Wannan na zuwa ne bayan shugaba Trump ya ce Amurka za ta daina kai hari kan mayaƙan Houthin.
Mista Trump ya yi sanarwar ba-zatan ne a lokacin da ya tarbi Firaiministan Canada, Mark Carney, a fadar White House.
Wakiliyar BBC ta ce mayaƙan Houthi sun sanar da cewa ba su da ra'ayin ci gaba da faɗa, ba su son yaƙi - kuma za su mutunta hakan ta hanyar daina yi musu luguden wuta.
Tun watan Nuwamban bara mayaƙan Houthi suka ƙaddamar da hare-hare kan jiragen ruwa masu jigila a tekun Maliya, inda suka ce suna rama abin da ake yi wa Falasɗinawa a Gaza.
Çalhanoglu ya ci wa Inter kwallo ta biyu
Asalin hoton, Getty Images
Hakan Calhanoglu ya ci wa Inter Milan kwallo na biyu.
Ya ci kwallon ne a bugun fenariti - bayan da Pau Cubarsi ya yi wa Lautaro Martinez ƙeta a yadi na 18.
Inter na da babbar dama a yanzu na zuwa wasan karshe.
Sai dai komai na iya faruwa.
An tafi hutun rabin lokaci bayan fafatawa mai zafi.
Friedrich Merz ya zama sabon shugaban gwamnatin Jamus
Asalin hoton, Getty Images
Sabon shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz ya ce zai yi aiki cikin ƙwarin gwiwar cimma burinsa na bunƙasa ƙasar.
Ya zamo shugaban gwamnatin Jamus ne bayan shiga zagaye na biyu na zaɓe a zauren majalisar dokokin ƙasar, bayan ya gaza samun ƙuri'un da ake buƙata a yunƙurin farko.
Wakiliyar BBC ta ce da safiyar yau mun sa ran Friedrich Merz ya cimma nasara ba tare da wata jayayya ba, saboda yana da goyon bayan mafi rinjayen ƴan majalisar, amma kwatsam sai sakamakon ya bayar da mamaki.
Tuni dai aka rantsar da majalisar zartarwar sa, kuma shugabannin ƙasashen duniya musamman daga Turai suka fara tura saƙonnin su na taya shi murna.
Inter Milan ta zura wa Barca kwallo ɗaya a raga
Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan ta zura wa Barcelona kwallo ɗaya a raga.
Ɗan wasan Inter Lautaro Martinez ne ya ci kwallon a minti na 21.
Wasan zagaye na biyu na matakin daf da karshe na gasar Zakarun Turai ne a ke fafatawa a San Siro.
Hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a JAMB - Ministan ilimi
Asalin hoton, Tunji Alausa/X
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara.
Ya ce sakamakon zaɓen bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata.
Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a Najeriya ranar Talata, inda ya ce hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi.
Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki akamakon zaɓen na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon haka a kalle shi a matsayin yadda ɗaliban da suka ci suka nuna hazaƙa lokacin rubuta jarabawar.
"JAMB na gudanar da jarabwarta ta hanyar amfani da tsarin kwamfuta wato CBT. Sun ɗauki ƙwararan matakai da ya janyo aka samu raguwar satar amsa matuka," in ji shi.
A ranar Litinin ne JAMB ta fitar da sanawar cewa cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka rubuta jarabawa, miliyan 1,534,654 ne wanda ya kai kaso 78 cikin 100 suka samu maki ƙasa da 200.
Hukumar ta ce ƙalilan ne suka samu maki mafi girma wato ɗalibai a jimillance, ɗalibai 12,414 ne kacal suka samu maki 300 sama.
China da Masar sun kammala atisayen soji na haɗin-gwiwa a karon farko
Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen Masar da China sun kammala wani atisayin soji na haɗin-gwiwa, a karon farko tsakanin su.
Kakakin rundunar sojin Masar ya ce dakaru daga ƙasashen biyu sun yi gwajin makamai da sarrafa jiragen yaƙi, a wani horo na haɗaka.
Ya ce maƙasudin horon shi ne ƙulla ƙawance tsakanin ƙasashen da sauran abokan su, da kuma bunƙasa ƙarfin dakarun su.
China dai na ci gaba da samun karɓuwa tsakanin ƙasashen Gabas ta tsakiya, yankin da Amurka ta daɗe tana tasiri.
An dai gudanar da wannan horon ne a wani waje da hukumomi suka ƙi bayyanawa, kuma an shafe kwana 18 ana yin shi.
Najeriya na neman hanyoyin shawo kan ababen fashewa da ƴan ta'adda ke dasawa
Asalin hoton, Getty Images
Mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya yi kira da a ƙara kaimi da kuma samar da hanyoyi na kawo karshen ababen fashewa da ƙungiyoyin ƴan ta'dda a yammacin Afrika ke amfani da wasu wajen kai hare-hare.
Ribadu ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki na ganin an haɗa kai wajen daƙile amfani da ababen fashewa a yammacin Afirka da aka buɗe a Abuja, ranar Talata.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar tsaro ya ce barazanar ayyukan ƴan ta'dda ba su da iyaka, inda ya ƙara da cewa sai masu ruwa da tsaki sun haɗa kai, kafin za a samu damar magance matsalar.
Ya ƙarfafa gwiwar mahalarta taron cewa su shiga a dama da su ta hanyar tattaunawa, samar da hanyoyi da kuma aiki tare don laluɓo mafita da za ta taimaka wajen daƙile ayyukan ta'ddanci da ke yi wa al'ummomi a yammacin Afirka barazana.
"Muna shirin samar da dabaru na zamani waɗanda za su taimaka mana wajen daƙile amfani da ababen fashewa.
"Shawarwari da za a samu a wannan taro suna da muhimmanci wajen tsara yadda za mu kare al'ummomin mu daga barazanar ababen fashewa," in ji Ribadu.
Shi ma lokacin da yake magana a wajen taron - jakadan Aljeriya a Najeriya, Hocine Mezoued, ya ce dole ne ƙasashen Afirka su ɗauki matakan yaƙi da ta'addanci idan har ana so kawo karshen matsalar.
Ya ce matakan za su kuma taimaka wajen daƙile sabbin hanyoyin zamani da ƴan ta'ddan ke amfani da su wajen kai hare-hare.
A cewarsa, ababen fashewa ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyi da ƴan ta'dda suka fi amfani da su wajen far wa al'ummomi a faɗin yammacin Afirka da kuma ƙasashen da ke yankin Sahel.
MDD ta yi Alla-wadai da shirin Isra'ila na shigar da agaji ta cibiyoyin soji
Asalin hoton, EPA
Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-adai da shirin Isra'ila na amfani da cibiyoyin soji wajen shigar da kayan agaji zuwa kudancin Gaza.
Kakakin hukumar ya ce hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa na bayar da agaji ga mabuƙata a duk inda suke.
Wakiliyar BBC ta ce da alama Isra'ila ta yi shirin ne da nufin bai wa wasu zaɓaɓɓun mutane agaji, musamman a kudanci, tare kuma da hana bayar da agajin a arewaci.
Wani babban jami'in Hamas ya shaida wa BBC cewa a yanzu ƙungiyar ba ta da sha'awar shiga yarjejeniyar tsagaita wuta, idan har Isra'ila ta ci gaba da hana shigar da kayan agajin ga dukkan ɓangarorin.
Isra'ila ta kai hari filin jirgin sama a Sanaa, babban birnin Yemen
Asalin hoton, EPA
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta ƙaddamar da sabbin hare-hare ta sama a Yemen, a wani yunƙuri na lalata filin jirgin saman birnin Sanaa.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce harin martani ne a kan harin da ƙungiyar Houthi ta kai Isra'ila a ranar Lahadi.
Kawo yanzu dai ba a tantance girman ɓarnar da harin ya yi ba.
Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta gargaɗi mutanen da ke kusa da filin jirgin saman da su gaggauta yin ƙaura.
A ranar Lahadi mayaƙan Houthi suka ƙaddamar da hari a kan filin jirgin saman Ben Gurion na Isra'ila, inda suka ce suna ramuwa ne kan abin da ake yi wa Falasɗinawa a Gaza.
Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamitin kula da mulkin jihar Ribas
Asalin hoton, Nigerian Senate
Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa kwamiti mai mambobi 18 domin sanya idanu kan yadda gwamnan riƙo na jihar Ribas Vice Admiral Ibok Ete Ibas mai ritaya ke tafi da aikinsa.
Majalisar ta ce ta ɗauki matakin ne a wani yuƙuri na ƙarfafa shugabanci na gari ba tare da rufa-rufa ba a jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Shugaban Majalsiar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar yayin zaman majalisar na yau Talata cewa kafa kwamitin na da matuƙar mahimmancin wajen sa ido kan abubuwan da ke faruwa a jihar.
Shugaban masu rinjaye Opeyemi Bamidele ne shugaban kwamatin, mambobin kuma sun haɗa da Adamu Aliero, da Osita Izunaso, da Osita Ngwu, da Kaka Shehu, da Aminu Abass, da Tokunbo Abiru, Adeniyi Adebire.
A watan Maris ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas sakamakon abin da ya kira "karyewar doka da oda" wanda ya auku sanadiyyar rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara na PDP mai adawa da tsohon Gwamna WIke mai ƙawance da APC mai mulki.
'Yanbindiga sun dame mu a Shanono da Bagwai, in ji ɗanmajalisar Kano
Asalin hoton, NASS
Danmajalisar da wakiltar mazaɓar Ɓagwai da Shanono a Majalsar Wakilan Najeriya ya nemi ƙarin jami'an tsaro sakamakon abin da ya kira hare-haren 'yanfashin daji a yankin.
Yusuf Badau ya yi kiran ne yayin wani ƙudiri da ya gabatar a gaban zauren majalisar yau Talata, inda ya lissafa lokutan da aka kai musu wasu hare-haren.
"Yan bindigar sun fara kai hari ne wata kasuwa da ke garin Farin Ruwa a ƙaramar hukumar Shanono ranar 17 ga watan Afrilu, inda suka kashe mutum biyu, da raunata mutum shida kuma suka sace mutum ɗaya," in ji shi.
"Sun sake kai irin wannan hari a garin Shanono ranar 26 ga watan Afrilun, sai dai mutanen garin sun tari ƴanbindigar kuma suka kore su.
"A ranar 2 ga watan Mayu a garin Fafarawa da Sandamu na Shanono da Bagwai, sun yi garkuwa da mutum daya da sace wayoyi, da babura bakwai, sai dai ba a samu asarar rayuka ba."
Majalisar ta aika batun kwamitin majalisar na tsaro da yansanda don daukar mataki na gaba.
Trump zai bai wa baƙin haure da suka amince su koma gida da kansu ladan dala 1,000
Asalin hoton, Getty Images
Gwamantin Amurka na bai wa yanciranin da suka shiga ƙasar ta harmatacciyar hanya dala dubu ɗaya (kimanin N1,600) idan suka amince su bar ƙasar da kansu.
"Ficewa daga ƙasar Amurka da kanka ita ce hanya mafi kyau, mafi aminci kuma mafi ƙarancin kuɗi don guje wa kame," in ji Sakataren Tsaron Gida, Kristi Noem, a sanarwar da ta fitar ranar Litinin.
Shugaba Trump ya ƙara da cewa waɗanda suka zaɓi su bar ƙasar da kansu na iya samun wata hanya ta doka da za ta ba su damar dawowa Amurka a nan gaba.
Tun da Trump ya koma kan ƙaragar mulki a watan Janairu ya ƙarfafa matakan da ake ɗauka don dakile shiga ƙasar ta harmataciyar hanya, inda a wasu lokuta yake amfani da hanyoyin da ke janyo cecekuce, ciki har da amfani da wata doka ta lokacin yaƙi da aka kafa tshekaru aru-aru.
A cewar wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS), mutanen da suka yanke fshawarar icewa daga ƙasar da kansu ba za su kasance cikin jerin waɗanda hukumomin ƙasar za su kama ba.
DHS ta kuma tabbatar da cewa an riga an saya wa mutum na farko da ya amince ya fice daga Amurka tikitin jirgi daga Chicago zuwa Honduras.
Hare-haren RSF sun jefa birnin Port Sudan cikin duhu
Harin da aka kai da jirage marasa matuƙa a birnin Port Sudan ya lalata babbar tashar lantarki wanda ya haifar da katsewar wutar a faɗin birnin, a cewar kamfanin lantarki na kasar.
Harin ya haifar da fashe-fashe da gobara a kusa da babban filin jirgin saman birnin, yayin da yau ya cika kwana uku a jere da RSF na kai hari a birnin.
Rahotanni sun ce an dakatar da tashin jiragen sama sakamakon harin da kuma wani otel da ke kusa da fadar shugaban ƙasa.
Cristina Karrer, wata ‘yarjarida da ke cikin birnin ta shaida wa shirin Newsday na BBC cewa: "Na ga gobara tana bazuwa ko’ina cikin birnin... Na kuma ji wasu manyan fashe-fashe biyu."
A safiyar yau, an ga baƙin hayaki ya lullube sararin samaniyar birnin wanda aka dade ana kallon sa a matsayin mafaka ga dubban 'yan gudun hijira daga yakin da aka ɗauki shekaru biyu ana yaƙi.
Kamfanin wutar lantarkin Sudan ya ce yana ci gaba da tantance girman ɓarnar da harin ya yi wa tashar wutar lantarki, lamarin da ya shafi ruwan sha da lafiya da sauran muhimman ayyuka.
Tinubu ya bai wa ma'aikatu umarnin amfani da kayan da ake sarrafawa a Najeriya
Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya da majalisar ministoci ta ƙasar sun amince da sabon tsarin saye da kuma amfani da kayan da aka samar a cikin gida a dukkan ma'aikatun gwamnati.
Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya faɗa wa manema labarai ranar Litinin cewa nan gaba kaɗan shugaban ƙasa zai sanya hannu kan wani umarni domin goyon bayan tsarin.
"Tsarin na nufin Najeriya za a fara sakawa a gaba a dukkan kayayyakin da za a sayo, babu wasu kaya ko na'urori da ake yi a cikin gida da za a sayo daga ƙasar waje ba tare da dalili ba," in ji ministan bayan kammala taron majalisar. .
"Hakan zai sa gwamnati ta mayar da hankali kan jama'armu da masana'antunmu ta hanyar sauya yadda gwamnati ke mkashe kuɗi, da yadda muke sayo kaya, da ma yadda muke haɓaka tattalin arzikinmu."