Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 10/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Rabiatu Runka, Isiyaku Muhammad, da Umar Mikail

  1. Isra'ila ta ce ta kashe kwamandojin Hezbollah da suke kai musu hare-hare

    Dakarun sojin Isra'ila, IDF sun ce sun kashe kwamandojin ƙungiyar Hezbollah guda biyu da ke kitsa kai musu hare-hare.

    Ahmad Moustafa al-Haj Ali, wanda kwamanda ne na sojojin da ake kira da Houla na da hannu a harba ɗaruruwan makamai masu linzami zuwa Kiryat Shmona da ke arewacin Isra'ila, kamar yadda rundunar sojin na Isra'ila ta ce.

    Harwayau rundunar ta kuma ce ta kashe Mohammed Ali Hamdan, kwamandan Hezbollah na rundunar yankin Meiss El Jabal wanda shi ne ke da alhakin "faɗaɗa hare-hare zuwa yankunan arewacin Isra'ila."

    Sai dai ƙungiyar ta Hezbollah ba ta ce komai ba dangane da iƙirarin na IDF kuma BBC ba ta iya bincikawa ba dangane da mutuwar mutanen ko kuma muƙaminsu a Hezbollah.

  2. Gwamnatin Najeriya na shirin cire harajin VAT a kan magunguna

    Chemist

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Najeriya sun ce sun soma wani yunƙuri na cire harajin VAT da kuma harajin shigo da kaya a kan magunguna da kuma na'urorin lafiya.

    Sanarwar da ma'aikatar kiwon lafiyar ƙasar ta fitar, ta ce a yanzu haka an kusan kammala tsarin da yadda shugaban ƙasa zai bayar da umarni a kai.

    "Matakin zai tabbatar da cewa hukumar tara haraji ta Najeriya - FIRS da kuma hukumar kwastam sun aiwatar da umarnin na cire harajin VAT a kan magani da kuma na'urorin lafiya," in ji sanarwar.

    A tsakiyar wannan shekarar, ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya sanar da cewa shugaba Tinubu ya sanya hannu a kan dokar samar da magani da sirinji da sauran kayayyakin lafiya a ƙasar.

  3. Ba mu da hannu wajen ƙarin kuɗin mai - Gwamnatin Najeriya

    PRESIDENT BOLA AHMED TINUBU

    Asalin hoton, Tinubu/X

    Gwamnatin Najeriya ta ce ba ta da hannu wajen ƙarin kuɗin fetur a ƙasar.

    A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust, ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya ce gwamnatin tarayya ba ta da hannu wajen ƙarin kuɗin mai na baya-bayan nan.

    "Dalilan da suka kawo wannan ƙarin farashin sun haɗa da rikicin gabas ta tsakiya, saboda ya haifar da tashin farashin mai a kasuwannin duniya."

    Ministan ya yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da ba NNPCL da gwamnatin haɗin kai, "Gwamnati za ta yi amfani da kuɗin tallafin da aka cire wajen inganta fannin lafiya da ilimi, tsaro."

    Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya yi ƙarin kuɗin fetur a ranar Laraba, inda farashin ya tashi daga naira 897 zuwa 1,030 kowace lita a Abuja, yayin da a jihar Lagos ya tashi daga naira 855 zuwa 998.

    A jihohin arewa maso gabas, man ya koma naira 1,070 a yankin kudu maso yamma, naira 1,025 jihohin kudu maso gabas ya kai naira 1,045.

    Matakin ya janyo cece-kuce a tsakanin ƴan Najeriya, inda suke ci gaba da neman shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wani kan tashin farashin man.

  4. An kashe ƙarin ma'aikatan kiwon lafiya biyar a Lebanon

    Beirut

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a ƙasar Lebanon sun ce hare-haren Isra'ila sun kashe ma'aikatan kiwon lafiya guda biyar a ranar Laraba a kudancin ƙasar.

    Wannan ne ya kawo adadin ma'aikatan kiwon lafiya da aka kashe tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan jiya zuwa 115.

    Jami'an tsaron Lebanon sun ce ma'aikatan kiwon lafiyar suna tsaye ne a wani asibitin wucin gadi da ke cikin wani coci a garin Derdghaiya lokacin da harin ya riske su.

    A wannan harin, hukumomi sun ce bayan mutum biyar da suka rasu, suna cigaba da duba baraguzai domin gano wasu.

    Gwamnatin ƙasar ta yi kira ga ƙasashen duniya su yi wani abu domin kare aukuwar irin waɗannan hare-haren, waɗanda ta ce sun karya dokokin yaƙi na duniya.

    Isra'ila ta ce ita dai tana hare-hare ne a wuraren da akwai ƴan Hezbollah, sannan wurin da ake magana, ta ce yana cikin wuraren da IDF ta yi gargaɗin mutane su fice.

  5. Hotunan harin Isra'ila da ya kashe ma'aikatan kiwon lafiya

    Beirut

    Asalin hoton, AFP/Getty Images

    Waɗannan hotuna ne na harin Isra'ila da ya kashe ma'aikatan kiwon lafiya guda biyar a Beirut na Lebanon.

    Beirut

    Asalin hoton, AFP/Getty Images

    Beirut

    Asalin hoton, AFP/Getty Images

  6. UNICEF ta ce mata na fuskantar cin zarafi a yankin hamada

    UNICEF

    Asalin hoton, Reuters

    Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce yankin kudu da hamadar sahara na daga cikin wuraren da mata suka fi fuskantar cin zarafi a duniya.

    An ƙiyasta cewa kusan mata da ƴan mata miliyan tamanin a faɗin yankin ko kashi ashirin cikin ɗari sun sha fama da fyaɗe da cin zarafi kafin su cika shekara sha takwas.

    Babbar Daraktan UNICEF, Catherine Russell, ta ce wannan al'amari na cin zarafin yara ƙanana ya zamo tamkar wata barazana ga al'umma.

    Masanan sun kuma yi imanin cewa hakan na da tasiri ga bunƙasar al'umma, domin yawanci waɗanda suka fuskanci irin wannan ba sa iya yin wani tasiri a harkokin koyo.

  7. Ƴan Lebanon sun yi watsi da kiran Netanyahu na yin tawaye ga Hezbollah

    Beirut

    Asalin hoton, Reuters

    Da alama kiran Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi wa ƴan Lebanon na su haɗa kai su yi wa ƴan Hezbollah bore bai samu karɓuwa ba a wajen mutanen ƙasar.

    Netanyahu ya yi wannan kiran ne, inda ya ce ko dai su musu bore, ko kuma ya ƙara zafafa luguden wuta a ƙasar.

    A cewarsa, “Kirista da Musulmi Sunni da Shia da Druze, dukkanku kuna shan wahala a sanadiyar yaƙin Hezbollah da Isra’ila. Ku tashi tsaye ku tseratar da ƙasarku.”

    Amma a yankunan Shia da Sunni da Kirista a Beirut a ranar Laraba, da alama sun yi kunnen uwar shegu da wannan maganar.

    “Mun ji maganarsa, amma ai babu wanda zai yi amfani da maganar Netanyahu,” in ji Yusuf Habbal mai shekara 31 a daidai lokacin da yake ci gaba da sana’arsa a shagonsa da ke Tariq El jdideh da ƴan Sunni suka fi yawa.

    “Babu wanda ya ce Netanyahu ya mamaye Falasɗinu, babu wanda ya ce ya mamaye Lebanon, Isra’ila ce take assasa yaƙin.”

    Sai dai duk da haka Habbal da sauran ƴan Sunni “ba su amince da abubuwan da Hezbollah take yi ba,” in ji shi.

    Shi ma wani mai suna Mohammed Khair mai shekara 43 da BBC ta riska ana masa aski a Tariq El jdideh ya ce, “babu wanda zai juya wa Hezbollah baya a nan saboda maganar Netanyahu.”

    A yankin Achirafieh, inda mafi yawan Kirista ne a Beirut, wani mai suna Antoine mai shekara 75 da BBC ta riska yana shan sigari cewa ya yi, “Netanyahu firaiministan Isra’ila ne, ba na Lebanon ba. Ya ji da mutanensa ba mu ba.”

    Ita ma Maya Habib mai shekara 35 ta ce, “Kowa ya san Isra’ila da ƙarya.”

    Fadi Ali Kiryani mai shekara 52 ya ce, “ko da Lebanon za ta fi Gaza rugujewa, za mu ci gaba da goyon bayan Hezbollah.”

  8. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.