Labarin wasanni daga 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nuno

    Asalin hoton, Getty Images

    West Ham na tunanin daukar Nuno Espirito Santo idan ta kori kocinta Graham Potter. (Alan Nixon), external

    Arsenal da Barcelona da kuma Napoli na sha'awar dan wasan Palmeiras mai shekara 19 dan kasar Brazil Luiz Gustavo Benedetti. (Mundo Deportivo - in Spanish), external

    Manchester United na zawarcin dan wasan tsakiya na Nottingham Forest Elliot Anderson wanda darajarsa ta kai fam miliyan 70, sai dai dan wasan Ingila mai shekara 22 na son ya ci gaba da taka leda a a City Ground kuma ba shi da niyyar barin kungiyar (Football Insider), external

    Chelsea ta yi wa Juventus tayin fam miliyan 70 kan dan wasa mai kai hari, Kenan Yildiz sai dai Juventus ta yi watsi da tayin a lokacin bazara saboda tana fatan dan wasa Turkiyya mai shekara 20 zai sa hanu kan kwatiragin ci gaba da taka led na tsawon lokaci.(Calciomercato - in Italian), external

  2. Yaushe Haaland zai haura tarihin Shearer kan cin ƙwallaye a Premier League?

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Erling Haaland na kan ganiya da fara kakar bana, yana da ƙwallo biyar a raga da fara kakar bana kuma shi ne kan gaba.

    Yadda yake zazzaga ƙwallaye a raga har an fara tambayar ko yaushe zai haura Alan Shearer a tarhin cin ƙwallaye a Premier League.

    Shearer tsohon ɗan wasan tawagar Ingila da Newcastle ya zura ƙwallo 260 , shi kuwa Haaland yana da 90 a yanzu haka.

    A watan Janairu Haaland ya saka hannu kan ci gaba da taka leda a Etihad zuwa karshen kakar 2034.

    Haaland ya zura ƙwallo 101 a Premier League kawo yanzu.

  3. Robertson ya ce ba zai amince da ɗumama benci a Liverpool ba

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

    Mataimakin ƙyaftin ɗin Liverpool, Andy Robertson ya ce ba zai amince yake ɗumama benci ba a ƙungiyar, bayan da aka yi ta alakanta shi da zai koma Atletico Madrid.

    Mai shekara 31 baya samun buga wasannin sosai, tun bayan da Liverpool ta sayo Milos Kerkez kan fam miliyan 40, wanda ya girma da shekara 10.

    Ranar Laraba Liverpool za ta kara da Atletico Madrid a wasan farko a cikin rukuni a Champions League.

    Robertson ya zaɓi ci gaba da zama a Anfield zai kuma yi kokarin sake komawa buga wa Liverpool wasanni cikin ƴan 11 farko.

  4. Me ka sani kan wasan hamayya na ƙungiyoyin Manchester?, Manchester City 3-0 Manchester United

    Manchester

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta doke Manchester United 3-0 a wasan mako na huɗu a Premier League da suka fafata ranar Lahadi a Etihad - me ka sani kan wasan hamayya tsakanin ƙungiyoyin Manchester City.

    • Erling Haaland ya ci ƙwallo biyu a wasan kuma na 50 kenan a karawa 50 a Etihad, shi ne na biyu a wannan ƙwazon bayan Alan Shearer da ya zura 50 a raga a wasannin gida, amma a wasa 47.
    • Sun buga wasan hamayya na 57 a Premier League ranar Lahadi - amma karon farko da ba a bayar da katin gargaɗi ko kuma jan kati ba a wasan.
    • Wasa na 10 da Pep Guardiola ya ci a karawar hamayya a Premier League, shi ne koci na uku a wannan bajintar, bayan Sir Alex Ferguson da ya ci wasa 20 da kuma Matt Busby da ya yi nasara 15.
  5. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Watakila Crystal Palace ta amince da tayin fam miliyan 60 da aka yi wa dan wasanta Adam Wharton a watan Janairun da ke tafe inda Liverpool ta nuna sha'war daukar dan wasan tsakiyar Ingila mai shekara 21. (Teamtalk), external

    Manchester United za ta yi hammaya da Manchester City wajan dauko dan wasan Inter Milan da Netherlands Denzel Dumfries mai shekara 29-. (Football Insider), external

    Real Madrid na bibiyar ci gaban dan wasan Leicester Jeremy Monga mai shekara 16 wanda ke cikin tawagar 'yan wasan Ingila masu shekaru kasa da 19 (Fichajes - in Spanish), external

  6. Waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a Premier League

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Labarai da dumi-dumi, Duplantis ya ci gaba da yin fice a tsallen kwangwala a duniya

    Sports

    Asalin hoton, Getty Images

    Armand Duplantis ya lashe lambar yabo ta 14 a wasan tsalle tsalle da guje guje ta duniya a Tokyo, kuma na uku a jere.

    Ya yi nasara tsallaka mita 6.30 a tsallen kwangwala,

    Mai shekara 25 ɗan kasar Sweden ya lashe lambar yabo takwas a bayan nan a dukkan fafatawa a wasannin cikin rufaffen fili da na cikin buɗaɗɗen filin.

  8. Elliott ya ce ya yi kuskure da ya yanke shawarar komawa Aston Villa

    Elliot

    Asalin hoton, Getty Images

    Harvey Elliott ya ce ya yi kuskure da ya amince ya bar Liverpool ya koma Aston Villa, domin bunkasa wasanninsa na sana'ar tamaula.

    Mai shekara 22 ya fara buga wa Aston Villa wasa a canjaras da ta yi da Everton, bayan shekara shida a Anfield da ya yin karawa 149.

    To sai dai wasa 35 aka fara da shi daga karawa 93 a Premier League a ƙungiyar, wanda wasa shida Arne Slot ya fara da shi a kakar da ta wuce a dukkan fafatawa.

    Bayan da Liverpool ta kashe sama da fam miliyan 400 wajen sayen sabbin ƴan wasa a bana, hakan ya sa Elliot ya hangi ba zai ke buga wasa sosai ba a ƙungiyar Anfield - sai ya amince da komawa Villa Park domin buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana da cewar za a iiya sayar da shi kan fam miliyan 35 idan har ya taka rawar gani.

  9. Manchester United tana buga kaka mafi muni tun bayan shekara 33

    Amorim

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Lahadi Manchester United ta sha kashi a hannun Manchester City da ci 3-0 a Etihad a wasan mako na huɗu a Premier League.

    Erling Haaland ne ya ci biyu daga ciki, kenan ya zura 50 a raga daga karawa 50 a Etihad, shi ne na biyu a wannan ƙwazon bayan Alan Shearer mai ƙwallo 50 a wasa 47 a gida a Premier League.

    Da wannan sakamakon United ta yi nasara 1 da canjaras ɗaya aka doke ta fafatawa biyu, kenan wannan ce kaka mafi muni da ta fara da rashin ƙwazo tun bayan 1992/93 karkashin Sir Alex Ferguson.

  10. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea za ta fuskanci hamayya daga Bayern Munich a zawarcin dan wasan gaban Lyon dan kasar Belgium Malick Fofana mai shekaru 20. . (Caught Offside, via Christian Falk), external

    Dan wasan bayan Liverpool dan kasar Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 26, ya yanke shawarar kin sabunta kwantiraginsa a Anfield, kuma zai rattaba hannu a Real Madrid a bazara mai zuwa. (Fichajes - in Spanish), external

    Manchester United ta ci gaba da zawarcin dan wasan Brighton dan kasar Kamaru Carlos Baleba bayan ta rasa dan wasan mai shekara 21 a bazarar bana.(Football Insider), external

    Dan wasan Manchester United Sam Mather, mai shekara 21, zai nemi barin Old Trafford a watan Janairu, bayan wa'adin komawar sa Kayserispor ya zo karshe.(Manchester Evening News), external

    Chelsea ta aike da 'wakilanta don kallon dan wasan Juventus dan kasar Turkiyya Kenan Yildiz mai shekaru 20.(Caught Offside), external

  11. Sakamakon wasannin Premier ta Najeriya mako na huɗu

    • Bendel Insurance 1-0 Niger Tornadoes
    • Abia Warriors 1-0 Katsina United
    • Bayelsa Utd 0-2 Enyimba
    • Kano Pillars 1-0 Enugu Rangers International
    • Kun Khalifat 3-1El Kanemi Warriors
    • Nasarawa Utd 1-0 Wikki Tourists FC
    • Plateau Utd 2-0 Remo Stars
    • Rivers Utd 1-0 Shooting Stars
    • Warri Wolves 0-0 Kwara United
    • Ikorodu 2-0 Barau FC
  12. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayern Munich na son a biyata fam miliyan 100 a kan dan wasan tsakiya na Faransa Micheal Olise mai shekara 23 wanda ya ja hankalin Liverpool da wasu manyan kungiyoyin turai (Football Insider), external

    Chelsea na son daukar dan wasan Crystal Palace da kuma Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, da golan AC Milan dan Faransa Mike Maignan,mai shekara 30, a bazarar bana. (TBR Football), external

    Da wuya Manchester City ta sabunta kwantiragin dan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva , wanda zai share fagen barin dan wasan mai shekara 31 daga kungiyar a bazarar badi , inda Juventus da Benfica suka nuna sha'awarsu (AS - in Spanish), external

    Liverpool da Arsenal da Manchester United na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiyar Lille, dan kasar Faransa Ayyoub Bouaddi mai shekaru 17. (Teamtalk), external

  13. Kano Pillars ta samu maki uku a karon farko a bana a Premier ta Najeriya

    Ahmed Musa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kano Pillars ta yi nasarar cin Enugu Rangers 1-0 a wasan mako na huɗu a Premier League ta Najeriya ranar Lahadi a filin wasa na Sani Abacha dake kofar Mata.

    Pillars ta ci ƙwallon ta hannun Ahmed Musa a minti na 65, hakan ya sa ta samu maki ukun da take bukata a karon farko da fara wasannin bana a babbar gasar tamaula ta Najeriya.

    Wasannin da ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta yi da fara kakar nan

    • Makon farko: Abia Warriors 1-0 Kano Pillars
    • Mako na biyu: Kano Pillars 1-1 Wikki Tourist
    • Mako na uku: Katsina United 1-0 Kano Pillars
    • Mako na huɗu; Kano Pillars 1-0 Enugu Rangers

    Kawo yanzu Pillars tana da haɗa maki huɗu daga wasa huɗu da fara kakar nan.

  14. Manchester City ta doke Manchester United a Premier League

    Haaland

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester City ta doke Manchester United 3-0 a wasan mako na huɗu a Premier League da suka buga ranar Lahadi a Etihad.

    City ta fara zura ƙwallo a raga ta hannun Phil Foden a minti na 18 da take leda, bayan da aka koma zagaye na biyu ne ƙungiyar Etihad ta kara biyu ta hannun Erling Haaland.

    Kenan Haaland ya ci ƙwallo na 50 a karawa 50 a Etihad a Premier League, Alan Sherer ne a gabansa da ya zura ƙwallo 50 a fafatawa 47 a gida.

    Tun daga kakar 2015/16 wadda take gida ta yi nasara bakwai daga karawa 21 a Premier League.

    Kuma City ta yi nasara shida daga wasa tara baya da ta fuskanci United da canjaras ɗaya ka doke ta biyu daga ciki.

    A makon gobe City za ta karbi bakuncin Napoli a wasan farko a rukuni na Champions League dana nan ta je gidan Arsenal a Premier League a karshen makon.

    Ita kuwa United za ta fafata da Chelsea a Premier League a karshen makon nan a Old Trafford.

  15. Madueke ya ja kunnen ƙungiyoyin Premier su yi hankali da ƴan gaban Arsenal uku, Arsenal 3-0 Nottingham Forest

    Arsenal

    Asalin hoton, get

    Sabon ɗan wasa, Noni Madueke ya ja kunnen ƙungiyoyin Premier League su yi hankali da ƴan gaban Arsenal uku a kakar nan.

    Ya faɗi hakan ne bayan tashi wasan da Gunners ta doke Nottingham Forest 3-0 ranar Asabar a Premier League da suka kara a Emirates.

    Arsenal ta yi amfani da ƴan ƙwallo uku a gurbin masu cin ƙwallaye, wato Noni Madueke da Eberechi Eze da kuma Viktor Gyokeres.

    Martin Zubimendi ne ya ci biyu da kuma Victor Gyokeres da ya kara na uku a raga da ta kai Gunners ta haɗa maki ukun da take bukata.

    Madueke, wanda ya buga gurbin Bukayo Saka wanda ke jinya ya kara da cewar ya kamata sun cin ƙwallaye da yawa a ragar Forest, ''To amma yanzu aka fara gasar bana, za kuma mu buga Champions League, saboda haka za muke cin ƙwallaye da yawa.

  16. Kane ya ci ƙwalo biyu a wasan da Bayern ta ɗura 5-0 a ragar Hamburg

    Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Harry Kane ya zura ƙwallo biyu a raga a wasan da Bayern Munich ta ɗura 5-0 a ragar Hamburg ta kuma ci gaba da jan ragamar Bundesliga a kakar nan.

    Serge Gnabry ne ya fara cin ƙwallo, sai Aleksandar Pavlovic ya ci na biyu daga biya Kane ya zura na uku a raga a bugun fenariti sannan ya ci na huɗu na biyu a fafatawar.

    Daga baya ne Luis Diaz ya ci na huɗu, an kuma sa Nicolas Jackson, wanda ya koma Bayern domin buga mata wasannin aro zuwa karshen kakar na.

    Jimulla Kane ya ci ƙwallo 67 a wasa 65 a Bayern Munich, kuma mai shekara 32 shi ne na biyar a jerin masu cin ƙwallaye a tarihin Bundesliga.

  17. Hojlund ya ci ƙwallo a wasansa na farko a Napoli, Fiorentina 1-3 Napoli

    Hojlund

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Asabar Napoli ta je ta doke Fiorentina 3-1 a gasar Serie A, inda sabon ɗan wasan da ta ɗauka a bana daga Manchester United, Rasmus Hojlund ya fara da zura ƙwallo a raga.

    Kevin de Bryne ne ya fara cin ƙwallo farko a minti na shida a bugun fenariti, sai Hojlund ya kara na biyu minti takwas tsakani, sannan Beukema ya kara na uku.

    Mai masaukin baƙi, Fiorentina ta zare ɗaya ta hannun Ranieri.

    Ɗan wasan tawagar Denmark ya koma buga wasannin aro a babbar gasar tamaula ta Italiya daga Manchester United ranar 1 ga watan Satumba da cewar za a iya sayensa kan fam miliyan 38 a kakar baɗi.

  18. Liverpool ta lashe dukkan wasa huɗu da fara kakar bana

    Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta yi nasara a gidan Burnley 1-0 a wasan mako na huɗu a Premier League ranar Lahadi.

    Ƙungiyar Anfield ta yi nasara ne daf da za a tashi a bugun fenariti, bayan da Hannibal Mejbri ya taɓa ƙwallo da hannu, kuma Mohamed Salah ne ya buga ya kuma zura a raga.

    Burnley ta karasa karawar da ƴan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Lesley Ugochukwu jan kati.

    Da wannan sakamakon Liverpool ta lashe dukkan wasa huɗu da fara Premier League kuma karo na uku da ta yi wannan bajintar.

    Ta taɓa hin haka a 2018/19, sannan ta kare a mataki na biyu a teburi da kuma a 2019/20, amma ta lashe kofin Premier League na kakar nan.

    Kawo yanzu Liverpool ta zura ƙwallo a wasa 38 a jere a Premier League, kenan Tottenham ce ke gabanta a wannan ƙwazon mai wasa 39 a jere daga Maris ɗin 2003 zuwa Maris 2004 da kuma Arsenal mai karawa 55 a jere tana zura ƙwallo a raga daga Mayun 2001 zuwa Nuwambar 2002.

    Burnley ta yi rashin nasara karo na 15 daga wasa 19 baya da ta fuskanci Liverpool daga ciki ta yi nasara biyu da canjaras biyu - rabon da ta doke Liverpool tun 1-0 a Janairun 2021 a Anfield.

  19. Flick ya caccaki Sifaniya kan nuna halin ko in kula da raunin Yamal

    Flick

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Barcelona, Hansi Flick ya ce ya kamata hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta ɗauki matakin kula mafi inganci, bayan da Lamine Yamal ya ji rauni lokacin da yake buga wa kasar tamaula.

    Mai shekara 18 ba zai buga wa Barcelona wasa da Valencia ranar Lahadi a gasar La Liga ba, watakila ba zai yi fafatawar da za ta fuskanci Newcastle United ba a makon gobe a Champions League.

    Haka shima Frenkie de Jong ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Netherlands tamaula, kenan shima ba zai buga wasan Valencia ba.

    Sai dai Marc Bernal, mai shekara 18 zai koma taka leda, bayan wata 13 da ya sha jinya.

    Barcelona za ta karɓi bakuncin Valenci a filin wasa na Johan Cruyff ranar Lahadi, sakamakon da ake ta gyaran Camp Nou.

  20. Maresca ya ce tun da aka fara kakar bana bai ga Sterling da Disasi ba

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Chelsea, Enzo Maresca ya ce bai ga Raheem Sterling ko Axel Disasi ba, tun da aka fara kakar bana.

    Ya sanar da cewar ƴan wasan suna atisaye a wani fili na daban ko wurin motsa jiki ba wanda sauran ƴan ƙwallon ƙungiyar ke amfani da su ba.

    Sterling da Disasi sun sa ran barin Chelsea a bana domin gwada sa'a a wata ƙungiyar, amma hakan bai yiwuwa.

    Sai dai ya ce har yanzu Sterling da Disasi ƴan wasan Chelsea.