Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Haruna Kakangi

  1. Trump ya soki Kamala Harris a dandalin yaƙin neman zaɓe

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya soki Kamala Harris a yaƙin neman zaɓensa na farko tun bayan da ta zama ƴar takarar da ake kyautata zaton za ta yi wa jam'iyar Democrat takara a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba.

    Yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayansa a jihar California, ɗan takarar jam'iyar Republican ɗin, ya kira abokiyar hamayyar tasa da mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka mafi rashin cancanta a tarihi.

    Ya kuma soki manufofinta na ƴancin zubar da ciki da kuma haƙƙin mallakar bindiga, ya kuma ce ta gaza a ɓangaren baƙin haure.

    Ya ce Kamala Harris ta kasance a matsayin jigon bala'o'in da Biden ya haddasa.

  2. Jirgin dakon mai ya nutse a Philippines

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Wani jirgin dakon mai, ɗauke da kusan lita miliyan ɗaya da rabi ya nutse a ƙasar Philippines.

    Masu bayar da agajin gaggawa na ci gaba da ƙoƙarin dakatar da malalar man.

    Hukumomin ƙasar sun ce malalar man ta kai tsawon kilomita huɗu, yayin da aka samu nasarar ceto mutum 16 daga cikin ma'aikata 17 da ke cikin jirgin.

    Iska mai ƙarfi da ake yi a ƙasar na kawo tsaiko ga aikin ceton.

    Kawo yanzu dai ba a gano dalilin nutsewar jirgin ba.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya fatan kun wayi gari lafiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a wannans safiya, domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa wa a shafukanmu na sada zumunta.