Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammad

  1. Labarai da dumi-dumi, Iran ta ce aƙalla mutum 430 aka kashe tun fara yaƙi

    Aƙalla mutum 430 ne aka kashe, sannan an jikkata 3,500 a Iran tun soma yaƙi da Isra'ila ranar 13 ga watan Yuni, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar - kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Nour ya ruwaito.

    Wannan ne sabon bayani da hukumomi suka fitar cikin kwanaki a Iran na alkaluman waɗanda suka mutu.

    A baya, ma'aikatar lafiyar ƙasar ta bayyana a ranar Lahadi cewa aƙalla mutum 224 ne aka kashe, yayin da wata ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta saka alkaluman zuwa 657 a ranar Juma'a.

  2. Labarai da dumi-dumi, Babban haɗari ne idan Amurka ta shiga yaƙin mu da Isra'ila - Iran

    Abbas Araghchi

    Asalin hoton, EPA

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya faɗa wa manema labarai cewa ƙasarsa "ba za ta ta shiga tattaunawa ba da Amurka muddin ana ci gaba da kai wa mutanenta hari".

    Abbas wanda yae Turkiyya a halin yanzu don tattaunawa da wakilan ƙasashen Larabawa, ya iƙirarin cewa "Amurka tana da hannu a far mana tun ranar farko", duk da cewa bai bayar da hujjoji kan haka ba.

    Ya yi gargaɗin cewa shigar Amurka a rikici tsakanin Isra'ila da Iran "zai zama babban hatsari".

    Idan za a iya tunawa dai, a farkon makon nan ne shugaba Donald Trump ya amince da shirin kai wa Iran hari, sai dai ya ce idan ta yi watsi da shirinta na nukiliya babu batun kai hari.

    Ministan harkokin wajen Iran ɗin ya ce "A shirye muke wajen shiga tattaunawa don samar da mafita kan shirin nukiliyar mu".

  3. Kotu ta samu tela da laifin gurɓata muhalli da karan keken ɗinki a Kano

    KEKEN ƊINKI

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata kotu a Kano ta samu wani tela da laifin gurɓata muhalli da karan da kekensa ke yi.

    Ma'aikatar kula da muhalli ta jihar ce ta kai ƙarar telan mai suna Mubarak Yusuf, kan yadda keken ɗinkinsa da kuma injin janareto ke damun mutanen anguwa da daddare.

    Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce duk da cewa ya musanta zargin, amma ta gabatar da hujjoji da suka gamsar da kotun.

    Har ila yau, kotun ta kai ziyarar gani da ido shagon da telan yake aiki, inda kuma ta tabbatar da cewa karan kekensa yana hana mutane barci da daddare, abin da ya saɓa wa sashi na 7 na dokar kare lafiyar al'umma ta 2019.

    "Don haka ne kotun ta yanke hukuncin taƙaita masa lokutan yin aiki, inda yanzu zai riƙa aiki daga karfe 6:00 na safe zuwa 9:00 na dare," in ji sanarwar.

    Kwamishinan muhalli na jihar ta Kano, Dakta Dahir Hashim ya yaba wa kotun bisa wannan hukunci, inda ya ƙara nanata zimmar ma'aikatar na ganin ta tabbatar da cewa kowane mutum ko kuma wuraren kasuwanci sun bi matakan kare lafiyar al'ummar da kuma muhalli.

  4. Yadda al'ummar gari guda suka tserewa hare haren 'yan bindiga a Sokoto

    Ƴan bindiga

    Asalin hoton, OTHER

    Rahotanni daga garin Tozai a karamar hukumar Isa da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Najeriya na cewa baki-ɗayan al'ummar garin sun tsere zuwa jihohi makwafta saboda hare-haren 'ƴan bindiga da suka addabi yankin.

    Rahotannin sun bayyana cewa a ƴan kwanakin da suka gabata, ƴan bindigar sun halaka mutane da dama, tare da sace wasu, ciki har da wata Amarya.

    Wani mazaunin garin na Tozai da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa a baya-bayannan 'yan bindigar sun sace mutum 10 tare da halaka bakwai a garin.

    Ya ce," A yanzu duk baki dayan mutanen garin sun gudu saboda hare haren 'yan bindiga inda wasu suka koma garin Isa wasu sun koma Zamfara, akwai wanda suka koma jihar Ondo wasu kuma sun gudu zuwa Auchi da ke jihar Edo."

  5. 'A yanzu Iran za ta iya ƙera makamin nukiliya cikin makonni idan ta so'

    US-IRAN

    Asalin hoton, Getty Images

    Daraktar leƙen asirin Amurka, Tulsi Gabbard ta ce Amurka na da bayanan sirri da ke nuna cewa Iran a yanzu ta kai wani mataki da za ta iya ƙera makamin nukiliya cikin makonni idan ta so hakan.

    A cikin watan Maris ne Tulsi Gabbard ta shaida wa kwamitin majalisar dattawan Amurka cewa Iran ba ta ƙera makamin nukiliya.

    Kalamanta na baya-bayan nan na zuwa ne bayan da shugaba Trump ya ƙaryata ta sau biyu - ya ce ta yi kuskure game da aniyar Iran.

    Iran dai ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kuma tana da ikon ta inganta sinadarin Uranium.

  6. Iran za ta tattauna da wakilan ƙasashen Larabawa a Istanbul

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya isa Santambul na Turkiyya domin tattaunawa da wakilan ƙasashen Larabawa game da yaƙin da ƙasarsa take yi da Isra'ila.

    Kusan jami'an diflomasiyya 40 ne daga ƙungiyar haɗin kan ƙasashen Musulmi za su halarci taron a ƙarshen makon nan.

    A ranar Juma'a ne Mista Araghchi ya gana da takwarorinsa na Birtaniya da Faransa da Jamus a birnin Geneva domin tattaunawa wadda Trump ke cewa ba ta da ma'ana.

    Mista Trump ya shaida wa ƴan jarida cewa Iran tana son tattaunawa da Amurka kuma babu taimakon da Turai za ta iya yi kan hakan.

    A jawabinsa na ƙarshe a taron, ministan harkokin wajen Iran ɗin ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta koma teburin tattaunawa da Amurka ba har sai Isra'ila ta daina kai mata hare-hare.

  7. Iran da Isra'ila na ci gaba da yi wa juna ruwan wuta

    Isra'ila-Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ce hare-haren Isra'ila sun sake faɗa wa kan cibiyar nukiliyarta da ke birnin Isfahan.

    Wata sanarwa da aka wallafa a shafukan sada zumunta ta ce Isra'ila ta kai hari kan ma'ajiyar makamai masu linzami na Iran da kuma cibiyar da take harba su kuma a cewarta, hakan ya yi ajalin kwamandan juyin-juya halin Iran da ke kula da ɓangaren jirage marasa matuƙa.

    Tun farko kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito wani hari da Isra'ila ta kai kan wani gini a birnin Qom da ya halaka ɗan shekara 16 tare da jikkata wasu biyu.

    A nata ɓangaren Iran ta harba makamai masu linzami kan wasu sassan Isra'ila cikin dare har da birnin Tel Aviv da kuma yankin gaɓar yamma da kogin Jordan.

  8. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Asabar.

    Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai jagoranci kawo muku labaran a wannan safiya.