An gano gawa biyu a Isra'ila bayan harin Iran kan wani gida

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomin Isra'ila sun ce an gano gawarwakin wasu mutum biyu a cikin ɓaraguzai, bayan wani harin makami mai linzami na Iran a kan wani gida a birnin Haifa na arewacin Isra'ilar.
Har yanzu kuma ba a san inda wasu mutum biyu suke ba.
Can a Iran ɗin kuwa kafofin yaɗa labaran Iran sun ce wani harin sama da aka kai kan wani gini da jama'a ke zama a ciki a babban birnin ƙasar, Tehran ya kashe mutum 13.
Wasu ƙarin hare-haren da aka kai a babban birnin sun faɗa kan wata jami'a da kuma wani wajen rarraba iskar gas, abin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a birnin.
Jami'an Iran sun ce hare-haren Amurka da Isra'ila a birnin Qom na tsakiyar ƙasar, sun kashe aƙalla mutum biyar.

