Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 07/10/2024
Taƙaitattu
- Harin Hezbollah ya jikkata mutum 10 a arewacin Isra'ila
- Gwamnati za ta kashe naira miliyan 366 domin cike ramukan hanyar Abuja zuwa Kaduna
- China ta gargaɗi ƴan ƙasarta da ke Pakistan
- 'Hare-haren Isra'ila sun mayar da Beirut fagen daga'
- Ƴan Kannywood bakwai da suka samu muƙamin gwamnati
- Madrid za ta sayi Alexander-Arnold, City za ta yi cefane a Janairu, Utd na son Xavi
- Abin da ya sa ƙabilar Ijaw ke tsunduma jarirai a kogi bayan haihuwarsu
Rahoto kai-tsaye
Usman Minjibir, Rabiatu Kabir da Isiyaku Muhammed
Harin Hamas ya raunata mutane biyu a Tel Aviv
Dakarun tsaron Isra'ila sun ce an harba makamai masu linzami biyar daga yankin Khan Younis na Gaza zuwa Tel Aviv.
Hamas ta tabbatar da cewa ita ce ta kai harin.
Tawagar BBC ta ce ta jiyo ƙarar fashe-fashe, yayin da motoci suka ciro-cirko a kan babbar hanyar Ayalon.
Sashen bada agajin gaggawa na Isra'ila sun ce mata biyu matasa da makaman suka faɗawa sun jikkata a tsakiyar Isra'ila, an kuma garzaya da su asibiti.
Tunda farko dai, sojojin Isra'ila sun ce sun daƙile duk wata barazana ta Hamas, inda suka ce sun kakkaɓo makamai masu linzami uku da Hamas din ta harba.
An kama mutum uku bisa zargin kashe ƴanuwan juna 18 a Afirka ta Kudu
Rundunar ƴansandan Afirka ta Kudu ta sanar da kama mutum uku bisa zarginsu da kashe wasu mutum 18 ƴanuwan juna a wani ƙauye bayan samamen da jami'anta suka kai.
Ministan ƴansandan ƙasar, Senzo Mchunu ne ya tabbatar da kamen a lokacin da ake addu'ar tunawa da mamatan 18 a ranar Lahadi a garin Lusikisikki da ke gabashin Cape inda aka yi kashe-kashen.
" Akwai mutum na huɗu da ake zargi da shi ma za su sanar da kama shi nan ba da jimawa ba"
An shiga damuwa ne a yankin bayan wasu ƴanbindiga sun buɗe wuta a wasu gidaje guda biyu, suka kashe mata 15 da maza uku, sannan ya jikkata wasu da dama.
Yawancin waɗanda harin ya shafa masu shekaru ne tsakanin 14 zuwa 64, kamar yadda jaridar Dispatch Live ta ruwaito.
Mchunu ya ƙara da cewa "har yanzu ƴansanda na ƙoƙarin gano musababbabin kisan".
An kashe sojan Isra’ila kan iyakar Lebanon
Rundunar sojin Isra’ila ta ce an kashe sojanta guda a yayin gumurzu a kan iyakar Lebanon da Isra’ila, yayin da sojoji biyu suka samu mugayen raunuka.
Sojojin Isra’ila sun soma kai farmaki ta kasa kan Hezbollah a Lebanon a ranar Litinin din makon da ya gabata, lamarin da ya haifar da barkewar rikici.
Shugabanni ba su da rigar kariya a Musulunci - Pantami
Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, farfesa Isa Ali Pantami ya yi kira da a yi watsi da tsarin ba shugabanni rigar kariya.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Pantami ya yi wannan kiran ne a ranar Lahadi a Abuja a wajen taron shekara-shekara na cibiyar Musulmi wato the Muslim Congress (TMC) mai taken; 'Gina ingantacciyar ƙasa: Nauyi ne kan shugabanni da mabiya domin tuna ranar ƴancin Najeriya na 64.
"A Musulunci, babu wata rigar kariya domin kariyar za ta ba mutum wata dama ce kawai a lokacin da yake shugabanci, wanda ba za ka samu ba, bayan ka bar ofis. Wasu lokutan kariyar na da kyau, amma a wasu lokutan hakan na jawo maka matsaloli da yawa ne," in ji shi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa, "da zarar ka bar ofis bayan shekara huɗu ko takwas sai ka ga ana ƙalubalantakarka da tuhume-tuhume da dama, wasu har guda 120 ma. Don haka kariyar ba ta hana mutum fuskantar shari'a, kawai tana jawo kawo jinkiri ne da kuma ba mutum damar ƙara aikata wasu laifukan.
"A shari'ar Musulunci babu wata rigar kariya. Da shugaba da mabiya kowa zai iya fuskantar shari'a, kuma dole ya je ya kare kansa. An yi wa Ali ibn Abi Talib da Umar ibn Khatab suna Khalifanci. Don haka yana da kyau a samar da daidaito a wajen shari'a," in ji Pantami.
Muna da ƙwarin guiwar samun nasara kan Isra'ila - Hezbollah
A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar kan cikar harin da Hamas ta kai Isra'ila shekara guda, Hezbollah ta ce tana da ƙwarin guiwar samun nasara a yaƙinta da Isra'ila, inda ta ce za ta ci gaba da gwabzawa da Isra'ilar.
Iran ce ke ɗaukar nauyiin Ƙungiyoyin Hezbollah da ke da mazauni a Lebanon da kuma Hamas.
Hezbollah ta bayyana harin da Hamas ɗin ta kai da na jarumtaka wanda tarihi ba zai manta da shi ba a yankin.
"Ba wajen zaman Isra'ila ba ne, saboda haka dole mu kawar da ta duk tsawon lokacin da za a ɗauka"
Hezbollah ta kuma ɗora alhakin yakin Gaza da Lebanon kan Amurka da ƙawayenta.
China ta gargaɗi ƴan ƙasarta da ke Pakistan
China ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke Pakistan da su yi taka-tsan-tsan game da tsaronsu bayan wani harin ta’addanci da aka kai a kusa da filin jirgin saman Karachi inda wasu ƴan China biyu suka mutu.
Ofishin jakadancin China ya buƙaci hukumomin Pakistan da su gudanar da cikakken bincike kan fashewar wani abu da ya lalata wasu motoci.
Ghulam Azhar Mahesar shi ne Mataimakin Sufeto Janar na ƴansandan yankin ya ce “Muna bincike kuma ba za mu iya cikakken bayani kan lamarin ba a halin yanzu.
Abubuwa da dama sun lalace sakamakon fashewar da ta auku.
Wata ƙungiyar ƴan aware mai suna Balochistan Liberation Army, ta fitar da wata sanarwa da ke cewa ta kai hari kan ayarin motocin injiniyoyi da masu zuba jari na ƙasar China.
Gwamnati za ta kashe naira miliyan 366 domin cike ramukan hanyar Abuja zuwa Kaduna
Gwamnatin Najeriya ta ce ta amince da kashe naira miliyan 366 domin gudanar da gyare-gyare a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Babbar hanyar, wadda ake sake ginawa kusan shekara shida da suka gabata, Julius Berger ne ke yi, amma yana fama da ramuka da sauran matsaloli da suke tayar da hankalin direbobi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A wata sanarwa da ma'aikatar aikace-aikace ta sanar, za a fara ne da sashe na 1 na titin daga Zuba zuwa ƙaramar hukumar Tafa ta jihar Neja, inda aka ba masu kwangilar mako biyu.
"Za a cike ramuka da kuma sabunta wasu wuraren da suka lalace, inda za a kashe naira miliyan 366."
Wannan sanarwa dai ta fito ne ƴan sa'o'i bayan da sashen Hausa BBC ya yi wani rahoto kan yadda aikin ya ƙi ci yaƙi cinweya a safiyar ranar Lahadi >>>> Yadda aikin titin Abuja zuwa Kaduna ya ƙi ci ya ƙi cinyewa
Harin Hezbollah ya jikkata mutum 10 a arewacin Isra'ila
Harin makamai masu linzami da Hezbollah ta harba daga Lebanon zuwa biranen Haifa da Tiberian na arewacin Isra'ila a cikin dare ya jikkata mutum goma, kamar yadda hukumar ko ta kwana ta Isra'ila.
Hukumar ta ce yawancin waɗanda suka jikkata, sun samu raunuka ne a sanadiyar fashewar gilasai da tagogi da sauran abubuwa.
Makamai masu linzamin sun sauka ne a gidaje da wani wajen cin abinci, kamar yadda rundunar sojin Isra'ila ta bayyana, inda ta ƙara da cewa za ta ƙaddamar da bincike domin gano yadda hare-haren makaman suka kauce wa tsaron ƙasar ba tare an kakkaɓo su ba.
Ita dai Hezbollah ta ce ta ƙaddamar da harin ne da niyyar tarwatsa makaman Isra'ila.
Assalamu Alaikum
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Za ku iya lekawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.
Ku kasance tare da mu.