Bankwana.
Da haka muka kawo ƙarshen rahotannin shafinmu na kai tsaye a yau.
Sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 07/10/2024
Usman Minjibir, Rabiatu Kabir da Isiyaku Muhammed
Da haka muka kawo ƙarshen rahotannin shafinmu na kai tsaye a yau.
Sai kuma gobe Talata idan Allah Ya kai mu.
Yayin da aka cika shekara ɗaya da harin ƙungiyar Hmas a Isra'ila, firaiministan Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da aikin tabbatar da ganin ba a ƙara samun irin wannan harin ba.
Ya kuma jaddada matsayar sa ta kawar da ƙungiyr Hamas daga doron ƙasa, da kuma ceto dukkan mutanen da ta yi garkuwa da su.
Netanyahu ya ce "Za mu yi duk abin da ya dace domin dawo da mutanen mu da aka yi garkuwa da su''
A jawabin da ya yi domin tuna ranar bakwai ga watan oktoba da Hams ta ƙaddamar da hari a Isra'ila a shekara da ta gabata, Netanyahu ya ce akwai buƙatar ''Ci gaba da yaƙin har sai an kawar da duk wata barazana ga Isra'ila''
Jim kaɗan bayan jawabin nasa ne kuma rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa Hamas ta ƙaddamar da harin roka daga Gaza zuwa cikin Isra'ila.
Rundunar ta kuma ce an harba wasu makamai cikin Isra'ila daga Yemen, amma na'urarta ta kama makaman.
Wata kotun tarayya a birnin Abuja ta bayar da belin wasu daga cikin masu zanga-zangar matsin rayuwa a Najeriya.
Mai shari'a Emeka Nwite, na kotun ya bayar da belin mutanen biyar a kan kudi naira miliyan biyar kowannen su.
A ranar 11 ga watan Satumba ne mai shari;a Emeka Nwite, ya bayar da belin masu zanga-zangar guda 10, a kan naira miliyan 10 kowannen su.
Sai dai wasu daga cikinsu sun gaza cika ƙa'idar belin nasu wadda ta ƙumshi samun wanda zai tsaya masu, wanda ya mallaki gida a cikin birnin Abuja, bayan kuɗin da aka gindaya masu.
Bayan samun wannan cikas ne lauyan waɗanda ake ƙarar ya sake komawa kotun domin nema wa biyar daga cikin su sassauci, kasancewar su ne suka gaza cika sharaɗin belin.
Daga baya kuma mai shari'a Nwite ya amince da buƙatar yi wa masu zanga-zangar sassauci, inda ya mayar da belin nasu naira miliyan biyar kowannen su.
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da waɗanda ake ƙarar ne su 10 a bisa zargin aikata laifuka da suka haɗa da cin amanar ƙasa, da neman tayar da rikici da kuma yin bore ga hukuma.
Ana kuma zagin su da yunƙurin afkawa fadar gwamnatin Najeriya da ƙona ofishin ƴan sanda da kuma raunata jami'an ƴan sandan.
Sai dai mutanen goma sun musanta dukkan zargin da ake masu.
Mataimakin shugaban ƙasar Kenya ya sha alwashin kare kansa a gaban majalisar dokoki inda za a fara zaman tsige shi a ranarTalata.
Yunƙurin tsige Rigathi Gachagua daga muƙaminsa na da alaƙa da saɓanin da ya samu da shugana William Ruto.
Yan majalisar dokokin da ke goyon bayan kudurin na zarginsa da tara dukiya ba kan ƙaida ba tun hawansa mulki shekaru biyu da suka gabata.
Haka kuma ana zarginsa da hannu a zanza zangar nuna rashin amincewa da gwamnatin da aka yi a watan Yunin da ya gabata tare da yi wa gwamnati zagon ƙasa da kuma goyon bayan siyasar ƙabilanci.
Sai dai Mista Gachagua ya musanta dukannin zarge zargen.
An yi taron addu'oi domin zagayowar ranar bakwai ga watan Oktoba, ranar da ƙungiyar Hamas ta kai hari Isra'ila.
Akwai kuma shirye-shiyen taruka a sassan duniya domin tunawa da ranar.
Ƙungiyar malaman jami'a ta Najeriya ta ce ƴanƴanta 84 suka mutu saboda matsin rayuwa da suka shiga bayan an riƙe masu albashi daga watan Mayu zuwa Ogustan 2024.
“Saboda matsanancin halin da mambobinmu suka shiga daga watan Mayu zuwa Ogustan 2024 ya sa 84 daga cikin su sun mutu.
“Duk da matsalolin da ake ciki, ace ana riƙewa mutane albashin wata uku da sunan 'ba aiki ba biyan albashi'. Mutane na faɗi-tashin yadda za su rayu amma kuna ƙara farashin mai da na lantarki, yanzu gashi nan komai ya yi tsada''
Farfesa Osodeke ya yi kiran ware ƙarin kudi domin gudanarwar jam'oin Najeriya, musamman wajen ƙarfafa gwiwar malaman jami'a.
A shekarar 2022 malaman jami'a suka shiga yajin aikin watanni takwas domin neman gwamnati ta cika alƙawurran da ta yi masu, na inganta walwala da gudanarwar jami'oi, lamarin da ya sa gwamnati ta aiwatar da tsarin babu aiki babu albashi a kan su.
A watan Oktoban 2023 shugaba Bola Tinubu ya amince da biyan su kuɗaɗen nasu na wata takwas, amma kuma malaman jami'ar sun yi ƙorafin cewa albashin wata huɗu kacal aka biya su daga cikin wanda suke bi.
Farfesa Osodeke ya ce ƙungiyar tana nan kan bakar ta cewa dole sai an biyan malaman dukkan albashin da suke bi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi kiran a zauna lafiya a jihar Rivers, inda zaɓen ƙananan hukumomi ya janyo zaman fargaba.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci ƴansanda su tabbatar da tsaro da zaman lafiya a dukkan sakatariyar ƙananan hukumomin jihar.
Wata sanarwa da mai ba shugaba Tinubu shawara kan watsa labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce shugaban ƙasan ya buƙaci gwamna Siminalayi Fubara da sauran ƴan siyasar jihar Rivers zauna lafiya domin ci gaban jihar.
Shugaban ya yi wannan kiran ne bayan rikice-rikicen da suka biyo bayan zaɓen ƙananan hukumomi da aka yi a jihar a ranar Asabar da ta gabata, inda aka samu rahoton fashewar wasu abubuwa da ƙone-ƙone bayan zaɓen.
Tinubu ya buƙaci ƴansiyasar jihar su yayyafa wa rikicin ruwa, sannan su yi kira ga magoya bayansu su zauna jihar.
"Ɗaukar doka a hannu ba tsarin dimokuraɗiyya ba ne, domin akwai kotuna da za su warware duk wata matsala." inji sanarwar.
Sannu a hankali rayuwa na komawa yadda take a baya a birnin Tel Aviv na Isra'ila. Sai dai kuma kaɗuwar hare-haren ranar 7 ga watan Oktoba ba ta kauce daga zukatan mutane ba.
Har yanzu akwai gomman Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a Zirin Gaza, inda dubun dubatar Isra'ilawan suka gudu daga gidajensu
Har yanzu akwai gomman waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, sannan dubban ƴan Isra'ila ba su koma gidajensu ba, sannan kuma a daidai yanzu da ake cigaba da gwabza yaƙi da Hezbollah, da alama yaƙin zai ɗauki lokaci sama da yadda aka yi tsammani.
Yawancin waɗanda suke gudanar da zanga-zangar, Yahudawa ne masu sauƙin ra'ayi, waɗanda suke adawa da mulkin firaiministan Netanyahu da gwmantinsa.
An tura dubban sojojin jiran ko ta kwana fagen daga, sannan tattalin arzikin ƙasar ya shiga tasku.
Mutane da dama suna cikin damuwa da fushi, sannan ana samun rabuwar kai a tsakanin ƴan ƙasar, inda ake cigaba da gudanar da zanga-zangar neman a tsagaita wuta tare da sako waɗanda aka yi garkuwa da su.
Shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden ya ce fararen hula da dama sun shiga taskuwa a cikin shekara ɗaya da aka yi ana gwabza yaƙi a Gaza.
A cewarsa, "a wannan yaƙin da aka fara tun a ranar 7 ga Oktoba, an jefa fararen hula da dama cikin tasku," in ji shi.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar, inda ya bayyana yadda yaƙin ya raba mutane da rayuwa mai daɗi, sannan ya ƙara bayyana saƙon da ya aike wa Isra'ila a bara cewa, "muna tare da ku."
"Yau ma kamar kullum, ina tuna waɗanda ake yi garkuwa da su da iyalansu," in ji Biden.
Ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba har sai ya tabbatar an samu yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, domin dawo da waɗanda aka sace, sannan ya bayyana cewa, sulhun diflomasiyya ne ya fi dacewa a Lebanon.
A ƙarshe ya ce tarihi ba zai manta da ranar 7 ga Oktoba ba a matsayin rana mai muni ga mutanen Falasɗinu.
Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce an kashe masu aikin kashe gobara guda 10 a hari da Isra'ila ta kai.
Ma'aikatar lafiyar ta Lebanon ce ta sanar da hakan, inda ta ce harin ya auku ne a kudancin Lebanon, a wani gida da ke Baraachit.
Ma'aikatar ta ƙara da cewa ta daddale kashe ma'aikatan guda goma.
A jumhuriyar Nijar duk da barnar da ruwan sama ya hadasa a damunar bana ,manoma daga wasu yankunan ƙasar sun nuna farincikinsu da albarkar daminar ta bana.
Sai dai duk da wannan yanayi da ake ciki, wasu yan kasar na kokawa cewa har yanzu farashin abinci bai yi kasa ba kamar yadda ake sa rai.
Kan haka ne, BBC ta tattauna da Mahamane Lawali, wani manomi da ya shafe shakaru sama da 20 ya na sana’ar noma a jihar Katsinar Maradi.
"Kusan shekara ta 23 ina sana'ar noma, amman daminar bana an jima ba a ga irinta ba, koda yake ta zo da na ta yanayi na ambaliyar ruwa , amman damina ta yi albarka duk ruwa ya tafi da wasu amfanin gonar, an yi abinci wanda ya wadata," cewar malam Lawali.
Manomin ya ce masu kuɗi na saye kayan amfanin gona tun kafin a girbe shiyasa abincin ke saurin yin tsada.
"Idan ana son kawo ƙarshen wannan matsalar, ya kamata gwamnati ta shigo ciki ta hanyar kafa kwamiti kafin zuwan damina domin duba buƙatun manoma, tare da biya masu buƙatunsu, daga baya sai a anshi amfain gona daga wajensu."
Shugabannin ƙasashen duniya sun gudanar ranar tunawa da hare-haren da mayaƙan ƙungiyar Hamas suka kai wa Israila inda aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Shugaban Faransa Emmaneuel Macron ya ce ba za a taɓa mantawa da waɗanda abin ya shafa ba.
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya kira ranar bakwai ga watan Oktoba a matsayin ranar bakin ciki da ba a taɓa ganin irinta ba a tarihin Yahudawa tun bayan kisan da aka yi musu a zamanin mulkin ƴan Nazi.
Shi kuma Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya lashi takobin dawo da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su "A wannan rana kuma a wannan wuri da kuma wurare da dama a ƙasarmu muna tunawa da waɗanda aka kashe da kuma waɗanda aka yi garkuwa da su."
Tun bayan wannan rana da aka kai hare-haren, Falasɗinawa kusan 42,000 aka kashe a zirin Gaza a cewa ma'aikatar lafiyar Hamas
Shugaba Biden na Amurka ya ba da umarnin tura ƙarin sojoji 500 zuwa jihar North Carolina domin taimakawa jihar murmurewa daga ɓarnar da guguwar Helene ta haddasa.
Adadin sojojin da aka tura jihar yanzu ya kai 1500.
Gwamnatin Mista Biden ta amince da kusan dala miliyan ɗari da arba'in domin bayar da agajin gaggawa yayin da ake hasashen cewa wata iska mai ƙarfi da aka yi wa lakabi da MIlton za ta afkawa yankin a cikin wannan makon.
Hezbollah ta ce ta kai sabbin hare-haren rokoki zuwa Haifa.
An kai hari a Haifa a cikin daren jiya, harin da Hezbollah ta ɗauki nauyin kai wa.
Tunda farko mun bada rahoton cewa mutane 10 sun jikkata sakamakon harin makamai mai linzami da Hezbollah ta kai.
Ƙungiyar ta ce ta kuma kai harin makamai masu linzami zuwa Karmiel da ke yankin Galilee a arewacin Isra'ila.
Rundunar Sojin Isra'ila ta fara gudanar da bincike kan yadda na'urorin tsaronta suka gaza daƙile wasu rokoki biyar da kungiyar Hezbollah ta harba zuwa birnin Haifa a daren jiya Lahadi.
Rokokin dai sun fada kan wani gidan abinci da kuma wata babbar hanya inda mutane 10 suka jikkata.
Tal Rosen ma'akacin agajin gaggawa ne a birnin Haifa ya ce: ''Ina zaune a gidana da bai da nisa sosai daga nan, da na ji karar fashewa sai na fita na ci karo da mutane hudu da suka jikkata, sai na kira hukumomi suka zo suka kai su asibiti Hezbollah dai ta ce tana kai hari ne kan cibiyoyin sojin Isra'ila
Ministar fasaha da raya al'adu ta Najeriya, Hannatu Musawa, ta ce ba ta damu da batun shirin da shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ke yi ba na yin garambawul a majalisar zartarwarsa.
Ministar ta bayyana haka ne a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a jiya Lahadi.
An tambayi ministar ko tana fargabar Shugaba Tinubu zai iya cire ta idan aka yi la'akari da cecekucen da ya mamaye ta bayan ba ta muƙamin minista?
Sai ta ce: "Ba ni tunanin akwai wani cecekuce da ya dabaibaye naɗina da kuma ofishina. Abin da za ni ce shi ne, na yi wa Shugaba Tinubu kamfe domin ya zama shugaban ƙasa, saboda haka na amince da duk matakin da zai ɗauka.
"Ban damu ba saboda na san cewa ci gaban ƙasa ne a gaban shugaba Bola Ahmed Tinubu, don haka duk matakin da zai ɗauka wajen yin garambawul a gwamnatinsa zai zama mai amfani ga ƴan Najeriya.
An daɗe ana kiraye-kiraye ga shugaban Najeriya da ya sauya wasu daga cikin ministocinsa saboda ana ganin ba su yin abin da ya dace.
A ƙarshen watan da ya gabata, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya ce shugaban ya bayyana kudurinsa na yin garambawul ga majalisar zartarwarsa, sai dai ba a bayyana lokaci ba.
Ƴan takara masu ra'ayin mazan jiya sun lashe zaɓen ƙananan hukumomi a wasu manyan biranen ƙasar Brazil, a wani lamari da ya yi wa siyasar shugaba Luiz Inácio Lula da Silva illa.
Yanzu dai hankali zai karkata zuwa zagaye na biyu na zaɓen da za a yi a birni mafi girma na kasar wato Sao paolo a karshen wannan watan.
Wakilin BBC ya ce Magajin garin São Paulo na yanzu, Ricardo Nunes, mai samun goyon bayan tsohon shugaban kasa Jair Bolsonaro.
Ya kasance a gaban dan takarar shugaba Lula -- Guilherme Boulos -- da tazarar da ba ta taka kara ta karya ba a zagaye na farko.
Amma Da ya ke babu wanda ya samu sama da kashi hamsin cikin dari na ƙuri'un da aka kaɗa, yanzu za su kara da juna a zagaye na biyu na zaben.
Rundunar ƴan sandar jihar Rivers ta janye jami'anta daga dukkan sakatariyar ƙananan hukumomi 23 da ke jihar, hakan na zuwa ne bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomin tare da rantsar da wadanda suka yi nasara.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar ƴansandar, Grace Iringe-Koko , ta fitar da safiyar yau Litinin ta tabbatar da hakan.
Ta ce kwamishinan ƴansanda na jihar ya bayar da umarnin ne ƙarƙashin umarnin Sifeto Janar, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci a janye jami'an da ke samar da tsaro a dukkan hedikwatar ƙananan hukumomin jihar nan take.
Jam'iyar APP ce ta samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 a cikin 23, yayin da jam'iyar AA ta samu nasarar lashe zaɓen ƙaramar hukumar, Etche.
Jami'an ƴansandan dai sun ƙarɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomin jihar Rivers a watan Yuni sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin Kantomomi masu goyon bayan gwamnan jihar mai ci Siminalayi Fubara da kuma tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi na gwamnatin da ta gabata da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.
Gwamna Siminalayi Fubara na takun saƙa da tsohon uban gidansa, ministan Abuja, Nyesom Wike, inda kowanensu ke son samun rinjaye a siyasance a jihar.
Rikicin ya sanya yaran gwamna Fubara barin jam'iyar PDP, inda suka yi takara a jam'iyar APP.
Sama da mutum 350 ne cutar kwalera ta kashe a Najeriya a wata tara na farkon wannan shekara, wanda ke nuna ruɓamyar lamarin da kashi 239 idan aka kwatanta da ƙididdigar cutar ta daidai wannan lokacin na bara kamar yadda ƙididdigar hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa, NCDC ta nuna a yau Litinin.
Kwalera wadda cuta ce da ke yaɗuwa ta cikin gurɓataccen ruwan, ba sabuwar cuta ba ce a Najeriya, kuma jami'an kiwon lafiya sun ce tana ta'azzara ne saboda ƙarancin tsabtataccen ruwan sha a ƙasar.
NCDC ta ce mutum 359 sun rasu a tsakanin Janairu zuwa Satumba, amma a daidai wannan lokacin a bara, mutum 106 ne suka rasu.
Haka kuma waɗanda ake tunanin sun kamu da cutar sun hauhawa daga 3,387 a bara, zuwa 10,837 a bana, inda cutar ta fi kama ƙananan yara masu shekara ƙasa da biyar.
Jihar Legas ce kan gaba wajen kamuwa da cutar.