Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 4/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 4/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Yau ake zaɓen Magajin New York

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Donald Trump ya amince da daya daga cikin wadanda suka dade suna sukarsa, Andrew Cuomo, ya zama magajin garin New York.

    Shugaban ya ce masu kada kuri'a ba su da zabi illa su goyi bayan Mista Cuomo a zaben na yau Talata, don hana dantakarar Democrat, Zohran Mamdani lashe zaben Mista Trump ya yi barazanar hana wa New York miliyoyin daloli na kudaden tarayya idan har Mista Mamdani ya yi nasara.

    Mista Cuomo ya gargadi ga masu zabe inda ya ce sun san abin da Trump zai yi idan har aka zabi abokin hamayyarsa Mamdani Mista Cuomo ya tsaya ne dai a matsayin dantakarar indefenda wato da ba shi da jam'iyya

  2. Babu shugaban da zai bari ana kashe mutanensa - Wike

    Wike

    Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce ba zai yiwu ba a ce suna cikin gwamnati, amma kuma a riƙa yi wa kiristoci kisan kiyashi, sannan su yi shiru.

    Wike ya bayyana haka ne a zantawarsa da tashar Channels a daren jiya Litinin, inda ya alaƙanta zargin da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump da siyasa da aka ɗauka da zafi.

    "Ta yaya za a ce gwamnati da nake ciki ne ake zargi da goyon bayan yi wa kiristoci kisan kiyashi. Wannan siyasa ce kawai da aka ɗauka da zafi," in ji shi.

    Ya ce sufeto janar na ƴansandan Najeriya kirista ne, shugaban hukumar tsaron kaya kirista ne, "sannan babban hafsan tsaron Najeriya ma kirista ne. Faɗa min, ta yaya mutum mai hankali zai yarda cewa za mu zauna a cikin gwamnatin da ke goyon bayan kashe mutanenmu."

    Wike ya ƙara da cewa babu shugaban da zai ji daɗi a riƙa kashe mutane a zamanin mulkinsa ko da kuwa daga ɓanngaren ƙasar.

    Trump dai ya yi barazanar tura sojojin Amurka zuwa Najeriya ne domin yaƙi da ta'addanci, inda ya ce ko dai gwamnatin ƙasar ta ɗauki mataki, ko kuma shi ya yi aikinsa da kansa.

    Sai dai gwamnatin Najeriya ta mayar da martani, inda ta nanata cewa kiristoci ba sa fuskantar wata barazana a ƙasar

  3. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata. Yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu.