Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/01/2026.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/01/2026.

Taƙaitattu

  • An karya dokar ƙasa da ƙasa a Venezuela - MDD
  • Sojojin Naeriya tara sun mutu bayan taka nakiya a jihar Borno
  • Uwa da yara huɗu sun mutu bayan ruftawar gini a Maiduguri
  • Ban aikata laifin komai ba - Maduro
  • Gobara ta yi mummunar ɓarna a kasuwar Buzaye a Sokoto
  • An kashe Falasɗinawa biyu a wani harin Isra'ila, in ji jami'an asibiti
  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Ana ce-ce-ku-ce kan zargin ƙirƙirar hoton Tinubu da fasahar AI
  • Hotunan yadda aka kai Maduro da matarsa kotu da ke New York
  • Iran da China sun yi kiran gaggauta sakin Maduro
  • Harin jiragen sama marasa matuƙa ya lalata tashar wutar lantarki a Sudan
  • Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga tare da ceto wasu da aka sace a Borno
  • Trump ya gargaɗi sabuwar shugabar Venezuela ta yi 'abin da ya dace'
  • Trump ya gargaɗi Iran kan kashe masu zanga-zangar tsadar rayuwa
  • Manyan al'amuran siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin 2026
  • Afcon 2025: Ko Najeriya za ta iya zuwa mataki na gaba?

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Harin jiragen sama marasa matuƙa ya lalata tashar wutar lantarki a Sudan

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin wutar lantarkin ƙasar Sudan ya ce harin jiragen sama marasa matuƙa da dakarun RSF suka kai ya lalata tashar wutar lantarki a birnin El-Obeid da ke tsakiyar kudu maso tsakiyan Sudan, wanda rundunar sojin ƙasar ke kula da shi.

    Wannan lamarin dai ya ya janyo rashin wutar lantarki mafi girma a faɗin yankin.

    El-Obeid ta kasance ita ce babban birnin jihar Kordofan ta Arewa, ita ce sabon fagen daga a rikicin da ya daɗe tsakanin sojojin ƙasar da RSF.

    Rundunar sojin ƙasar ta sanar a karshen watan da ya gabata cewa ta sake karɓar wasu birane da ke kudu da El-Obeid daga hannun RSF, wadda ta kaddamar da yunkurin mamaye manyan wurare a Kordofan.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da halin jin kai ke ƙara tabarbarewa yayin da yaƙin da aka daɗe ana fama da ita ke ci gaba da haddasa wahala ga fararen hula inda wasu kuma ke tserewa.

    Fiye da fararen hula 100 ne suka rasa rayukansu a hare-haren jiragen sama mara matuƙa, yayin da dubban mutane suka tsere a faɗin Kordofan tun farkon Disamba 2025.

    Dukkan ɓangarorin da ke yaƙi da juna na kallon Kordofan a matsayin muhimmin wuri na gwada ƙwanji don raba ikon ƙasar, saboda inda jihar take. Jihar na matsayin hanyar zuwa Yammacin Darfur, inda RSF ke da ƙarfi.

  2. Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga tare da ceto wasu da aka sace a Borno

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation Haɗin Kai sun samu nasarar kashe ƴanbindiga tare da ceto wasu fararen hula da aka sace a wani samame da suka kai a karamar hukumar Konduga, Jihar Borno.

    Sojojin, tare da haɗin gwiwar dakarun ƴan sa kai ta CJTF, sun yaƙi ƴanbindigar ne a kan hanyar Sojiri a safiyar ranar 4 ga Janairu, 2026.

    Rundunar ce ta bayyana hakan a shafinta na X.

    A yayin samamen, an kashe ƴanbindiga guda biyar yayin da suka ceto mtum 3 da aka sace ba tare da asarar rai daga bangaren sojoji ba.

    Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindigogi na AK-47 da wasu kayan yaki daban-daban.

    Rundunar ta ce wannan aiki ya nuna jajircewar sojojin Najeriya wajen kai farmaki kan ƴanbindiga, yayin da suke mai da hankali wajen kare rayukan fararen hula da tabbatar da tsaro a yankin.

  3. Najeriya ta kama Indiyawa 22 kan zargin safarar hodar ibilis

    ...

    Asalin hoton, NDLEA/X

    Hukumar yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta sanar da cewa ta kama wasu ƴan ƙasar Indiya 22, bisa zargin su da hannu a safarar hodar ibilis wadda nauyinta ya kai kilo 31.5, wadda aka gano a wani jirgin ruwa a ranar 2 ga Janairu.

    Mai magana da yawun NDLEA ya ce jirgin, wanda aka kama a babbar tashar jiragen ruwa ta Legas, "ya fito ne daga Tsibirin Marshall".

    Ya ƙara da cewa waɗanda aka kama sun haɗa da matuƙin jirgin da kuma ma’aikata 21.

    Mai magana da yawun hukumar bai bayar da wani ƙarin bayani kan lamarin ba.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana Najeriya a matsayin wata babbar cibiya ta safarar miyagun ƙwayoyi zuwa kasashen Turai.

    A watan Nuwamba 2025, NDLEA ta kama ma’aikatan jirgi 20 ƴan ƙasar Philippines kan wani jirgi da ke ɗauke da kilogram 20 na hodar ibilis a tashar birnin Legas, wadda ta fito daga daga Brazil.

    Wata ɗaya kafin haka, hukumar ta tarwatsa ƙungiyoyi biyu na masu safarar ƙwayoyi da ke da hannu wajen jigilar hodar ibilis zuwa Biritaniya.

  4. ECOWAS ta nuna damuwa kan harin da Trump ya kai a Venezuela

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta bayyana matuƙar damuwa kan harin sojin Amurka da gwamnatin Shugaba Donald Trump ta kai a Venezuela, tare da kira ga dukkan ɓangarori da su yi hattara da kuma mutunta dokokin ƙasashen duniya.

    A wata sanarwa da ta fitar a Abuja, ECOWAS ta amince da haƙƙin kowace ƙasa na yaƙi da manyan laifukan ƙasa da ƙasa kamar ta’addanci da safarar miyagun ƙwayoyi, amma ta jaddada cewa dole ne a aiwatar da hakan bisa ƙa’idojin dokar ƙasashen duniya da kuma mutunta ikon ƙasashe masu cin gashin kansu.

    Kungiyar ta tunatar da al’ummar duniya wajibcin mutunta cikakken ikon ƙasa da yancinta, kamar yadda Sashe na 2(4) na Kundin Tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya ya tanada, wanda ke hana amfani da ƙarfi ko barazanar amfani da ƙarfi kan wata ƙasa.

    ECOWAS ta ce ta goyi bayan matsayar Tarayyar Afirka, wadda ta bayyana matuƙar damuwa kan abin da ke faruwa, tare da jaddada cewa tattaunawa cikin lumana ce kawai za ta iya samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin da ke addabar Venezuela.

    A halin da ake cik, Afirka ta Kudu ta buƙaci Majalisar Tsaron MDD ta gaggauta zama, tana kiran harin da Amurka ta kai da kuma kama Nicolas Maduro a matsayin ƙeta dokokin ƙasashen duniya.

    Namibia ma ta yi Allah-wadai da matakin, tana cewa kama Maduro da matarsa ya saba wa ikon ƙasa da ‘yancin Venezuela.

    Wadannan martani na zuwa ne yayin da rikici ke ƙara tsananta a Venezuela, wadda ta shafe shekaru tana fama da matsanancin rikicin siyasa da durkushewar tattalin arziki.

  5. Trump ya gargaɗi sabuwar shugabar Venezuela ta yi 'abin da ya dace'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya gargaɗi sabuwar shugabar riƙo ƙwariyar Venezuela, Delcy Rodríguez, da cewa za ta iya “fuskantar mummunan sakamako, mai yiyuwa ma ya fi wanda Nicolas Maduro ya fuskanta,” idan ba ta yi abin da ya dace ba.

    Trump ya yi wannan furuci ne a wata hira da mujallar Amurka The Atlantic, a daidai lokacin da ake sa ran hamɓararren shugaban Venezuela, Nicolas Maduro, zai bayyana a gaban wata kotu a birnin New York ranar Litinin.

    Gwamnatin Amurka na zargin Maduro da laifukan safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba — zargin da Maduro ya musanta.

    Delcy Rodriguez wadda ta taɓa zama mataimakiyar shugaban ƙasa a zamanin Maduro dai ta nemi haɗin kai da Shugaban Amurka Donald Trump, a wani saƙon sasantawa da ta fitar bayan taron majalisar ministocinta na farko.

    Rodriguez ta bayyana cewa gwamnatinta na neman kyakkyawar alaƙa da Amurka wadda za ta kasance bisa fahimtar juna, haɗin kai da mutunta juna.

    Rodríguez, wadda ke da goyon bayan Kotun Koli ta Venezuela da kuma rundunar sojin ƙasar, ana sa ran za a rantsar da ita a matsayin shugabar ƙasa a ranar Litinin a Caracas.

  6. Trump ya gargaɗi Iran kan kashe masu zanga-zangar tsadar rayuwa

    ...

    Asalin hoton, AFP VIA GETTY

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗi ga Iran cewa za ta fuskanci mummunan sakamako idan aka ci gaba da kashe masu zanga-zanga a ƙasar.

    Gargaɗin ya zo ne yayin da Amurka ke ɗaukar matakai kan Venezuela tare da bayyana cewa tana sanya ido sosai kan abin da ke faruwa a Tehran, duk da cewa babu wata sanarwa ƙarara kan matakin da za ta ɗauka.

    Trump ya yi wannan barazanar ne a daidai lokacin da zanga-zangar tsadar rayuwa ke ci gaba da girgiza Iran, wadda ta shafe sama da mako guda tana gudana.

    A ƙoƙarin kwantar da hankulan jama’a, gwamnatin Iran ta sanar da shirin fara bai wa ‘yan ƙasar wani sabon alawus na wata-wata, kimanin dala bakwai, domin rage raɗaɗin matsalar durkushewar tattalin arziki da ta haddasa tarzoma a ƙasar.

    Rahotanni sun nuna cewa aƙalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar zanga-zangar a Iran.

  7. Manyan al'amuran siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin 2026

    ...

    Asalin hoton, Social Media handles

    Shekarar 2026 shekara ce da Najeriya za ta fuskanci manyan al'amura masu ɗaukar hankali.

    Kama daga na siyasa da tattalin arziki, da sauran fannonin rayuwar ƴan ƙasar da dama.

    A fagen siyasar ƙasar ana ra ran ganin abubuwa da dama kama daga kaɗa kugen babban zaɓen ƙasar na baɗi zuwa tsayar da ƴan takara da sauran abubuwa.

    Dokta Yakubu Haruna Ja'e shugaban Malami a jami'ar jihar Kaduna ya ce gaba-ɗayan wannan shekara za ta karkata ne kan al'amuran siyasa a Najeriya, ''ta yadda in ba a yi hankali ba duka zaɓaɓɓu za su mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓe maimakon aiki''.

    Cikin wannan muƙala mun rairayo wasu daga cikin abubuwa na siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin wannan sabuwar shekara ta 2026.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyarmu, Barkanmu da war haka, da fatan muna cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar kullum, a yau ma wannan shafi na Kai Tsaye zai kawo rahotanni da labarai na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran kasashe makwabta.

    Sai ku ci gaba da bibiyar mu domin sanin halin da duniya take ciki a yau Litinin.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.