Putin zai gana da ƙawayen Rasha domin nuna wa ƙasashen yamma ƙwanji
Ka kwatanta kanka a matsayin Vladimir Putin.
Ƙasashen yamma suna maka ƙiyayya saboda ƙaddamar da yaƙi a Ukraine. Sannan an ƙaƙaba maka wasu takunkumi domin hana tattalin arzikin ƙasarka takaɓus a kasuwannin duniya.
Sannan kotun manyan laifuka ta bayar da umarnin a kama ka da zarar ka bar ƙasarka.
Ta yaya ne za ka iya nuna wa ƙasashen nan ƙwanji? sai kawai ka gwada shirya wani babban taro.