Amurka ta wallafa jerin haraje-haraje kan kayayyakin ƙasashe 70
Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta wallafa jerin sabbin haraje-haraje kan kayayyakin da ake shigar da su ƙasar da ta lafta wa ƙasashe kusan 70 da har yanzu ba su cimma yarjejeniyar kasuwanci da ita ba.
Nan da kwanaki bakwai ake sa ran sabbin matakan za su soma aiki, amma akwai zaɓin tattaunawa.
Ƙayayyaki daga ƙasashen da Amurka ke cin gajiyar kasuwanci an sa musu harajin kashi 10 cikin 100.
Sannan inda Amurka ke ɗan kashe kuɗaɗenta za su ke biyan kashi 15 cikin 100, amma akwai ƙasashe da dama da harajin ya yi tsauri, domin akwai mai kashi sama da 40 cikin 100.
Harajin Brazil ya kai kashi 50, sannan kashi 15 kan Japan, Koriya ta Kudu da Turai, sannan Syria da Myanmar kashi 40 zuwa 41
