Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a, 01/08/2025

Wannan shafi ne da ke muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a, 01/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello, da Umar Mikail

  1. Sai da safe

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a.

    Muna tafe da wasu rahotonnin gobe da safe.

  2. An kashe mutane da dama a Burkina Faso bayan harin masu iƙirarin jihadi

    Sojojin Burkina Faso

    Asalin hoton, Reuters

    Rahotanni daga arewacin Burkina Faso na cewa wasu hare-hare biyu sun yi sanadin mutuwar gomman mutane, ciki har da mayaƙa masu ikrarin jihadi da sojoji da kuma fararen hula.

    Majiyoyin tsaro sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Faransa AFP cewa mayaƙan sun kai wa wani sansanin soji hari a ƙauyen Dargo na lardin Namentenga ranar Litinin.

    Haka kuma akwai rahotannin da ke cewa kimanin direbobin manyan motoci 20 ne aka kashe lokacin da aka yi wa jerin gwanon motocinsu da ke ɗauke da kayayyakin kwanton ɓauna.

    Burkina Faso na fuskantar ƙaruwar hare-hare daga ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda.

  3. Faransa ta dakatar da shirin karɓar Falasɗinawa daga Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Faransa ta dakatar da shirinta na karɓar Falasɗinawan da ke tserewa daga Zirin Gaza.

    Dakatarwar za ta ci gaba da aiki yayin da hukumomin ƙasar ke binciken wata ɗaliba 'Bafalasɗiniya da ake zargi da yin kalaman ƙiyayya kan Yahudawa a intanet.

    Ɗalibar mai shekara 25 ta samu tallafin karatu ne a arewacin Faransa, inda yanzu dole ta bar ƙasar saboda jami'ar ta janye tallafin da ta ba ta.

    Faransa ta taimaka wa fiye da mutum 500 barin Gaza tun bayan ɓarkewar yaƙi a watan Oktoban 2023.

  4. Ina so na taimaka wa Falasɗinawa a Gaza - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son taimaka wa mutanen Gaza domin su ci gaba da rayuwa.

    Ya yi kalaman ne bayan ziyarar da jakadansa na musamman Steve Witkof ya kai a cibiyoyin rabon kayan agaji da Amurka da Isra'ila ke gudanarwa a yankin.

    Mista Trump ya ƙara da cewa zai sanar da wani sabon tsari na ayyukan jin kai domin inganta samar da abinci a Gaza bayan samun bayani daga jakadan nasa.

    Da ma dai Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta bayyana shirin na bayar da agaji karkashin gidauniyar Gaza Humanitarian Foundation da tarkon mutuwa.

    Ta ce kimamin Falasdinawa 1,400 aka kashe wajen karɓar abinci a cibiyoyin gidauniyar tun daga watan Mayu da aka soma shirin.

  5. Muradunmu a yaƙin Ukraine ba su sauya ba - Putin

    Vladmir Putin

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Vladmir Putin na Rasha ya ce har yanzu sharaɗinsa na samun zaman lafiya a Ukraine bai sauya ba.

    Mista Putin bai ambaci wa'adin kwanaki 10 da Donald Trump ya diba na cimma yarjejeniya ba, amma ya ce ɓacin rai na tare da wanda ya sa ran cimma abin ba a iya cimmawa.

    Ya zargi ƙasashen Yamma da mayar da hankali kacokan ga dakatar da dannawar dakarun Rasha cikin Ukraine.

    Yana wannan magana ne lokacin da yake tare da Shugaban Belarus Alexandar Lukashenko a wani tsibiri da ke ƙarƙashin ikon Belarus ɗin.

  6. Trump ya ba da umarnin kai makaman nukiliya don martani ga Rasha

    Makaman nukiliya

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin kai makaman nukiliya wasu yankuna "da suka dace" a matsayin martani ga kalaman tsohon Shugaban Rasha Dmitry Medvedev.

    Trump ya ce ya yi hakan ne "ko da a ce kalaman na tsokana ba iya kalamai ba ne". Ya ce "kalamai na da matuƙar muhimmanci kuma za su iya kaiwa ga abubuwan da ba a yi tsammani".

    Bai fadi wuraren da ya umarci a kai makaman ba wanda jiragen ƙarƙashin ruwa ke ɗauke da su.

    Medvedev ya yi wa Aurka barazana a kwanan nan saboda wa'adin da ya bai wa Moscow ta kawo ƙarshen yaƙin da take yi a Ukraine ko kuma ta fuskanci takunkumai.

  7. Kasuwannin hannun jari na duniya na faɗuwa saboda harajin Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Manyan kasuwannin hannun jari na Amurka sun buɗe ba tare da wani tagomashi ba sakamakon harajin da Shugaba Donald Trump ya ƙaƙaba wa ƙasashen duniya.

    Hannayen jari a Dow Jones da S&P 500 sun yi ƙasa da kashi 1 cikin 100, yayin da suka faɗi da kashi 1.5 a Nasdaq.

    Faɗuwar na zuwa ne bayan kasuwannin nahiyar Asiya da Turai sun fadi tun da farko.

    Ana tunanin masu zuba jarin na fargabar abin da ka iya faruwa ne musamman saboda yadda alƙaluma suka nuna cewa ayyukan yi sun ragu a Amurka, wanda mummunar alama ce ga tattalin arzikin ƙasar.

  8. Liverpool na shirin haƙura da sayen Isak

    Isak

    Asalin hoton, PA Media

    Liverpool na shirin ficewa daga cinikin ɗanwasan gaba na Newcastle Alexander Isak bayan an ƙi karɓar tayin farko da ta bayar.

    Newcastle ta yi wa ɗanƙwallon farashi kan fan miliyan 150, inda ta ƙi amincewa da tayin 110 daga Liverpool kan ɗan ƙasar Sweden ɗin.

    BBC Sport ta fahimci cewa Liverpool ba ta tunanin cinikin zai faɗa a wannan bazarar saboda yadda al'amura suke a yanzu.

    Ɗanwasan mai shekara 25 bai shiga tawagar Newcastle da ta je nahiyar Asiya ba saboda ƙaramin raunin da ya ji a cinyarsa, kamar yadda kulob ɗin ya bayyana.

    Tuni ya bayyana wa kulob ɗin cewa yana son ya koma taka leda a wani wuri. Ya koma filin wasa na St James' Park a 2022 kan fan miliyan 60 daga Real Scieded ta Sifaniya.

  9. Ma'aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya, in ji ministan lafiya

    Ma'aikatan lafiya a Najeriya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan lafiya a Najeriya ya ce ma'aikatan jinya da ungozoma ƙarƙashin ƙungiyar National Association of Nigerian Nurses and Midwives (NANNM) sun janye yajin aikin da suka fara yi.

    Da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Juma'a, Ali Pate ya ce sun ɗauki matakin janye yajin ne saboda yarjejeniyar da suka cimmma da gwamnatin tarayya bayan wata ganawa a yau ɗin.

    A ranar Talata ne ma'aikatan jinyar suka fara yajin aikin saboda abin da ƙungiyar tasu ta bayyana da "gazawar gwamanti wajen biyan buƙatunsu cikin wa'adin kwana 15 da ta bayar" ranar 14 ga watan Yuli.

    Akaasrin buƙatun sun jiɓanci walwalar ma'aikata, da alawus-alawus a asibitocin gwamnatin tarayyar Najeriya.

  10. Amurka ta sanya wa kayayyakin Afirka ta Kudu harajin kashi 30

    Trump da Ramaphosa na zaune suna tattaunawa a fadar gwamnatin Amurka  kowa na nuna yatsa

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ƙara wa kayayyakin Afirka ta Kudu da ake shiga da su ƙasarta harajin kashi 30 cikin 100.

    Dangantaka tsakanin Mista Trump da Shugaba Cyril Ramaphosa ta taɓarɓare a cikin 'yan watannin nan.

    Shugaban Amurka ya dakatar da dukkan tallafi kan Afirka ta Kudu, bisa zargin nuna wariya kan fararen fata tsiraru.

    Amurka ta kuma rage haraji kan kayayyakin ƙasar Lesotho daga kashi 50 cikin 100 zuwa kashi 15, wani abu da ka iya taimakawa wajen tsare kamfanonin tufafi.

  11. INEC ta saka ranar fara rajistar masu zaɓe a faɗin Najeriya

    INEC

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya ta ce nan gaba cikin wannan wata za ta fara yin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar gabanin zaɓukan 2027.

    Cikin wata sanarwa da INEC ta wallafa a shafinta na X ranar Juma'a, ta ce za ta fara rajistar masu zaɓen ta yanar gizo a ranar 18 gawatn Agustan da muke ciki.

    Hukumar zaɓen ta kuma saka ranar Litinin 25 ga watan Agustan a matsayin ranar fara rajistar a ofisoshinta da ke ƙananan hukumomi da sauran wuraren da ta ware don gudanar da aikin.

    INEC ta ce za a riƙa gudanar da aikin ne daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana a ranakun Litinin zuwa Juma'a.

    Kan hakan ne hukumar ta buƙaci waɗanda ba su da rajistar su yi amfani da damar wajen mallakar rajistar.

    Hukumar ta ƙayyade shekara 18 a matsayin mafi ƙanƙantar shekarun yin rajistar zaɓe a Najeriya.

  12. Tsohon shugaban Koriya ta Kudu ya ƙi yarda a fitar da shi daga kurkuku

    Tsohon shugaban kasar Koriya ta Kudu, wanda a yanzu haka ke tsare a kurkuku - ya ƙi yarda a fitar da shi daga gidan yari, inda ya kwanta baje a kasa daga shi sai ɗan kamfai.

    Masu shigar da ƙara sun nemi yi wa Yoon Suk Yeol tambayoyi ne kan yiwuwar saba ƙa'idojin zaɓe.

    Masu bincike sun ce watakila su yi amfani da ƙarfin tuwo wajen fitar da shi, nan gaba idan suka sake komawa kurkukun.

    Lauyan Mr Yoon ya ce yin bayanin filla-filla kan yadda lamarin ya faru, tamkar cin mutunci tsohon shugaban ƙasar ne.

    An kama Mista Yoon ne bisa tuhumarsa da ƙoƙarin kafa dokar soji a Koriya ta Kudu.

  13. Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta kafa sansani a Kebbi

    Jami'an sojin ruwan Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Navy/X

    Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta a garin Yauri na jihar Kebbi a wani mataki na bunƙasa harkokin tsaron iyakokin ruwa.

    Matakin na zuwa ne bayan da wata tawagar manyan jami'an sojojin ruwan suka kai ziyara gidan gwamnatin jihar Kebbi a ranar Alhamis.

    Tawagar ƙarƙashin jagorancin Rear Admiral Patrick Nwatu - wanda ya wakilci babban hafsan sojin ruwan ƙasar ta ziyarci Kebbi ne domin duba yadda za ta samar da sansaninta a jihar.

    Rundunar ta ce ta ɗauki matakin ne domin faɗaɗa ayyukanta zuwa sauran yankunan ƙasar, musamman domin samar da tsaro a kan iyakokin ƙasar na tudu da na ruwa domin magance ayyukan ɓata-gari a kogin Niger.

    “Duk da irin muhimmanci da kogin Niger ke da shi wajen haɓaka ayyukan noma da samar da lantarki da kamun kifi da sauran sana'o'i, sannu a hankali ɓata-gari na mafani da shi wajen aiwatar da muggan ayyukansu'', in ji Nwatu.

  14. Jakadan Trump ya ziyarci wuraren rabon tallafi a Gaza

    Jakadan Shugaba Trump na musamman, Steve Witkoff ya kai ziyara domin duba wuraren da ake rabon tallafi a Gaza masu samun goyon bayan Isra'ila da Amurka da ke shan suka.

    Mista Witkoff na tare da jakadan Amurka a Isra'ila, Mike Huckerbee, wanda ya wallafa hotunan wuraren rabon tallafin.

    Ziyarar tasu na zuwa ne a daidai lokacin da ake jefa wa mazauna Gaza agaji ta sama irinsa mafi girma.

    Ƙasashen Jamus da Sifaniya da Belgium da Faransa da kuma Bahrain ne ke jefa tallafin tare da haɗin gwiwar ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Jordan.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan Falasɗinawa 1,400 aka kashe a ƙoƙarinsu na karɓar tallafi a Gaza tun ƙarshen watan Mayu, inda mafi yawansu aka harbe su a kusa da wuraren rabon tallafin.

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta bayyana kashe-kashen da laifukan yaƙi.

    Isra'ila na zargin Hamas haifar da yamutsi a kusa da wuraren rabon tallafin, inda ta ce ba da gayya jami'anta ke buɗe wuta kan fararen hula ba.

  15. Ƴansandan Kaduna sun kama mai kwaikwayon muryoyin gwamnoni

    jami'an ƴansanda

    Asalin hoton, Ƴansanda

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta kama wani matashi da ya ƙware wajen kwaikwayon muryoyin wasu gwamnonin Najeriya.

    Ƴansandan na zargin matashin da amfani da muryoyin wajen damfarar mutane maƙudan ƙuɗaɗe.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar ASP Mansur Hassan, ya shaida wa BBC cewa dama rundunar ƴansandan jihar ta jima tana neman matashin ruwa a jallo.

    ''Bayan kama shi mun same shi da lambobin waya da dama ciki har da na manyan mutane a ƙasar nan'', in ji kakakin ƴansandan.

    ''Mutumin ya ƙware sosai wajen kwaikwayon muryoyin mutane, duk wani mutum da ba ka tunani zai iya yi maka muryarsa'', in ji shi.

  16. Dakarunmu na fuskatar matsalar ƙarashin muhalli - Sojojin Najeriya

    Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya ke tsaye yana jawabi

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya yi kiran ƙara wa rundunarsa kuɗi domin tabbatar da ayyuka da walwalar dakarun rundunarsa.

    Janar Oluyede ya bayyana hakan ne lokacin ganawa da kwamitin majalisar dattawan ƙasar kan sojojin ƙasa a lokacin wata ziyara da tawagar kwamitin ya kai shalkwatar sojojin ƙasa na ƙasar da ke Abuja.

    Baban hafsan ya yaba wa ayyuka da taimakon da kwamitin majalisar dattawan ke bai wa rundunarsa.

    Sai dai ya sake jaddada cewa kuɗin da ake ware wa rundunar ba sa biya wa rundunar buƙatunta, kamar yadda rudunar ta wallafa a shafinta na X.

    Janar Oluyede ya kuma bayanin wasu manyan matsalolin da rundunar ke fuskanta, musamman wajen gudanar da ayyukanta da ƙarancin muhalli ga dakarun rundunar.

    Haka kuma ya yi kira ga ƴan majalisar su su duba yiwuwar ƙara wa rundunar ƙudi a kasafin kuɗi domin magance matsalolin da take fuskanta.

    Shugaban kwamitin majalisar dattawan, Sanata Abdulaziz Yar’Adua ya yaba wa rundunar sojin ƙasan kan jajircewar da suke yi wajen samar da tsaro a faɗin ƙasar.

  17. Malawi ta rage yawan masu kamuwa da HIV a ƙasar

    Jami'ai a Malawi sun ce ƙasar ta samu nasarar cimma abin da Majalisar Dinkin Duniya ta gindaya wajen yaƙi da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.

    A baya ƙasar ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da cutar HIV ta fi muni, inda mutum guda cikin bakwai na ƴan ƙasar ke ɗauke da cutar a shekarun 1990.

    Lamarin da ya sa tsawon shekarun ƴan ƙasar ya ragu daga 56 zuwa 38 a shekarun na 1990.

    Shugabar hukumar yaƙi da cutar a ƙasar, Beatrice Matanje ta ce ƙasar ta yi ƙoƙari wajen dagewa kan matakan rage yawan masu ɗauke da cutar.

    Cikin ƙa'idojin yaƙi da cutar da MDD ta gindaya, kuma ƙasar ke son cimmawa a wannan shekara har da tabbatar da aƙalla kashi 95 cikin ɗari na masu ɗauke da cutar su san matsayinsu.

    Ms Matanje ta kuma ce akwai buƙatar ɗaukar matakai kan ƴan mata da sauran mata domin kare su daga kamuwa da cutar.

    ''Akwai buƙatar ƙarin wayar da kai da ilimantarwa da kuma bayar da tallafin rage raɗaɗin talauci'', in ji ta.

  18. 'Masu tsegunta wa ƴanbindiga ne ke kitsa mafi yawan hare-haren Katsina'

    Gwamnan Katsina ke magana a zaune sanye da shuɗayen tufafi

    Asalin hoton, Dikko Radda/Facebook

    Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga bayanai ne ke haddasa kashi 80 cikin 100 na hare-haren yanbindiga a faɗin jihar.

    Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar, Nasir Mua'azu ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a jihar.

    Nasir Mu'azu ya ce masu kwarmata wa ƴanbindigar bayanai da ke kai musu abinci da sauran abubuwa ne ke ba su bayanan da suke buƙata domin ƙaddamar da hare-hare.

    Kwamishinan ya ce hakan kuma na matuƙar kawo wa gwamnati tsaiko wajen yaƙi da matsalar ƴan fashin daji a faɗin jihar.

    Ya ƙara da cewa wasu daga cikin irin waɗannan mutane kan kai wa ƴanbindigar abubuwan da suke buƙata har dazuka su kuma sayar musu a farashi mai tsada.

    “A ɗaya daga cikin waɗannan garuruwa an taɓa kama wani mutum na sayar da kwalbar lemo naira 3,000 ga ƴan bindiga, wani kuma na sayar musu man fetur kan naira 5,000 kowace lita'', kamar yadda ya bayyana.

    “Haka ma akwai masu kai miyagun ƙwayoyi su sayar musu a farashi mai yawa, sun mayar da hakan sana'ar da suke samun kuɗi masu yawa'', in ji shi.

    Kwamishinan ya yi zargin cewa wasu ma daga ciki kan haɗa baki da ƴanbindigar wajen sace mutanen da suke so a sace ciki kuwa har da danginsu.

  19. Tinubu ya nemi gwamnoni su haɗa hannu don yaƙi da talauci a ƙauyuka

    Bola Tinubu sanye da shuɗin tufafi da shuɗiyar riga, tsaye sanye da tubarau, yayin da aka maƙala abin ɗaukar magana a rigarsa

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Bayanan hoto, Tinubu ya ce akwai buƙatar ƙara ƙaimi wajen inganta tattalin arzikin mutanen ƙauyukan ƙasar

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci gwamnonin ƙasar su fifita walwalar ƴan Najeriya ta hanyar zuba jari a ƙauyuka da yankunan karkara, ta hanyar bunƙasa wutar lantarki da ayyukan noma domin kawar da talauci.

    Kiran na zuwa ne bayan gabatar da wani shirin gwamnati na musamman kan bunƙasa tattalin arziki a matakin mazaɓu da aka yi wa laƙabi da 'Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP)' da ministan kasafi da tsare-tsare na ƙasar ya yi a lokacin taron majalisar tattalin arzikin ƙasar.

    Manufar sabon shirin na RHWDP shi ne tabbatar da bunƙasar tattalin arziki ta hanyar taimaka wa mazaɓun ƙasar 8,809 a faɗin jihohin ƙasar 36, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

    Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin ƙasar su yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa rayukan ƴan ƙasar daga tushe.

    ''Ina kira a gare ku, mu ƙara ƙaimi wajen sauya halin da mutanenmu ke ciki a yankunan karkara'', in ji Tinubu, kamar yadda sanarwar ta ambato.

    “Tsare-tsaren tattalin arzikinmu na tafiya yadda ya kamata. Mun kama hanyar farfaɗowa, amma muna buƙatar ƙara ƙaimi a yankunan karkara. Mun san halin da ƙauyukanmu ke ciki, don haka mu haɗa hannu wajen yin abin da zai tallafa musu,'' in ji shi.

  20. Jakadan Trump na musamman zai ziyarci Gaza

    Wasu mata uku na kuka

    Asalin hoton, Reuters

    Jakadan gwamnati Amurka na musamman, Steve Witkoff zai ziyarci Gaza a yau Juma'a domin ganin ainihin abubuwan da ke faruwa ido da ido.

    Mai magana da yawun gwamnati, Tammy Bruce ta faɗa wa BBC cewa, ziyarar da Mista Witkoff zai kai na sake tabbatar wa duniya irin ƙoƙarin da gwamnatin Trump ke yi wajen ganin an kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Mista Witkoff zai sa ido kan yadda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyin da ake ce-ce-ku-ce a kai na gidauniyar da Amurka da Isra'ila ke goyon-baya.

    Claire Manera ta Médecins Sans Frontières ta ce ko a wannan makon sun karɓi ɗaruruwan mutanen da aka jikkata a asibitocinsu bayan harbin bindiga da sojojin Isra'ila ke yi a inda ake rabon tallafin.

    Majalaisar Dinkin Duniya ta ce an kashe Falasɗinawa fiye da 1,000 da ke fita karbar abinci a Gaza kawo yanzu daga watan Mayu.