Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 05/11/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Laraba 05/11/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Umar Mikail

  1. Duniya ta manta da yaƙin basasar Sudan - MDD

    Hayaƙi na tashi sama a wani yanki a Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce duniya ta manta da yaƙin basasar da ake yi a Sudan.

    Volker Turk ya ce akwai buƙatar ɗaukar matakin da ya dace domin kawo ƙarshen kisan ƙare dangin da ake a can.

    Mista Turk, ya shaida wa BBC cewa ana aikata cin zarafi da take haƙƙin ɗan'adam a faɗan da ake tsakanin sojojin ƙasar da kuma mayaƙan RSF.

    Ya bayyana ƙawanyar da aka yi wa birnin El Fasher tsawon watanni 18 a matsayin abin tashin hankali.

    Mista Turk ya ce akwai buƙatar ƙasashen duniya su matsa wa mayaƙan RSF lamba domin kawo ƙarshen kisan ƙare dangi da fyade da ɓatan mutanen da ake gani a Sudan.

  2. Musulmi na farko ya lashe zaɓen magajin garin New York a Amurka

    Zohran Mamdani

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin

    Zohran Mamdani ɗan jam'iyyar Democrat ya lashe zaɓen magajin garin birnin New York.

    Mista Mamdani shi ne musulmi na farko da ya lashe zaɓen maganin garin a tarihin birnin.

    Ɗan asalin Asiyan shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da ya zama magajin garin birnin mai muhimmanci a Amurka.

    Hakan na zuwa ne a ranar da ake ganin jam'iyyarsu ta yi rawar gani a sauran zaɓukan da aka yi a wasu wurare a Amurka.

    Mista Mamdani ya yi nasara a kan Andrew Cuomo na jam'iyyar Indifenda da kuma Curtis Sliwa na jam'iyyar Republican wanda ake gani shi ne zai zo na uku a zaɓen.

    Waɗannan zaɓuka su ne na farko da ake gani kamar wani ƙalubale ne ga gwamnatin Trump.

    Tuni dai Trump ya bayyana cewa ai ba da shi aka yi takara ba a zaɓen.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar ranar Laraba.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.