Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan ranar ta Juma'a.
Allah ya nuna mana gobe, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 18/07/2025
Ibrahim Haruna Kakangi da Abdullahi Bello Diginza
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin na labaran kai-tsaye na wannan ranar ta Juma'a.
Allah ya nuna mana gobe, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.
Rikici tsakanin Larabawan Bedouin da mayaƙan Druze ya sake ɓarkewa a kudancin Lardin Sweida da ke Syria.
Rikicin ya ƙara ɓarkewa kwana ɗaya bayan dakarun gwamnatin ƙasar sun janye bayan ruwan bama-bamai daga Isra'ila.
Kusan mutum 600 aka kashe tun daga lokacin da aka fara rikicin ranar Lahadi.
Rikicin ya janyo Isra'ila wadda ta ce tana goyon bayan mabiya addinin Druze.
Wata cibiyar bibiyar yaƙi a duniya ta ce yaƙin yana ƙara ƙazancewa a garuruwan da suke kusa da birnin Druze na Sweida.
Wani Alƙali a Brazil ya umarci tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro ya sanya na'urar bibiya a jikinsa domin bibiyarsa, wanda aka yi domin hana shi ficewa daga ƙasar.
An zarge shi ne da shirya gangami da nufin janyo Amurka ta sanya baki a shari'ar da ake masa.
Ana tuhumarsa da shirya juyin mulkin da zai hana shugaba Lula da Silva kama aiki.
A makon da ya gabata Mista Trump ya yi wa Brazil barazanar ƙarin haraji da kashi hamsin idan ba a dakatar da shari'ar ba.
Hukumomi a arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da wani hari da ƴanbindiga suka kai a wani ƙauye da ke jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce maharan sun kashe mutum shida, sannan suka yi garkuwa da sama da mutum 100.
Mazauna garin cu ce maharan sun kai harin ne a garinsu da ake kira Kairu a ranar Juma'a, inda suka buɗe wuta suka firgita mutane, inda suka yi wa garin ƙawanya har tsawon awa biyu.
Daga bisani ne suka kwashe mutane, ciki har da mata da ƙananan yara.
A watan Fabrailun da ya gabata ma mahara sun kai hari a ƙauyen, inda suka kashe mutum huɗu.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya bayyana Marigayi Aminu Ɗantata a matsayin mutum mai nagarta da kyautatawa, wanda ya ƙarar da rayuwarsa wajen hidimta wa al'umma.
Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyayar gaisuwa ga iyalan mamacin a Kano a yau Juma'a.
Ɗantata ya rasu ne a ranar Talata, ga watan Yulin shekarar 2025 a Dubai, sannan aka binne shi a birnin Madina.
"Rasuwar Ɗantata ta matuƙar taɓa ni, wannan ya sa na zo domin in muku ta'aziyar wannan babban rashin," in ji shi.
Tinubu ya ce a lokacin da yake neman zaɓen shekarar 2025, ya je har gida ya samu marigayin domin neman albarka, "sannan na yi alƙawarin komawa bayan zaɓe, amma maimakon haka, sai shi ya kawo mani ziyarar a Abuja. Wannan ya nuna irin sauƙin kansa."
Shugaban ya yaba da irin taimakon al'umma da Ɗantata ya yi a lokacin rayuwarsa, inda ya ce, "da a ce ana cigaba da taimakon a lahira, da za a samu Ɗantata ne a kasuwa yana ciyar da mabuƙata abinci, yana kula da marasa lafiya ta hanyar ɗaukar nauyin kuɗin jinyarsu. Ya mayar da hankali sosai wajen kula da mutane da ma ƙasarmu baki ɗaya."
Tinubu ya miƙa ta'aziyarsa ga iyalan Ɗantata da gwamnati da mutanen jihar Kano da ma ƙasar baki ɗaya. "Muna addu'ar Allah ya jikansa, ya gafarta masa."
A nasa jawabin a madadin al'umar jihar Kano, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf godiya ga Shugaba Tinubu bisa ta'aziyar da kai musu.
Likitoci a kudancin Gaza sun ce Falasɗinawa masu fama da yunwa da suke tururuwa zuwa cibiyoyin lafiya a yankin suna ƙaruwa.
Daraktan asibitin Kuwaiti da ke Khan Younis ya ce marasa lafiya suna zuwa da alamun tsananin yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Sobaib Al-Hums ya yi gargaɗin cewa ɗaruruwan mutane suna fuskantar barazanar mutuwa saboda yunwar.
Cibiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Gaza ta ce ma'aikatan agaji tara ne Isra'ila ta kashe a lokacin da suke yunƙurin karɓar abinci mai gina jiki a kusa da Rafah a ranar Juma'a.
Abinci ƙadan ne kawai Isra'ila take bari yana shiga ziri Gaza - yawanci kuma ta Amurka kuma ake rabawa ƙarƙashin kulawar Isra'ila.
Gwamnatin Kano tare da wakilcin jam'iyyar APC a Kano da wasu muƙarraban gwamnatin tarayya ne suka tarbi Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a jihar Kano, inda ya je domin gaisuwar rasuwar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Gwamnatin Birtaniya ta sanya wa hukumar leƙen asirin soji ta Rasha, da wasu mutane da ta zarga da haifar da yamutsi bisa umarnin Kremlin takunkumi.
Ta ce wani sashe ya taimaka wajen kai hari wani matsugunin farar hula a Mariupol da ke Kudancin Ukraine inda ɗaruruwan mutane suka rasa rayukansu.
Sai dai Rasha ta sake nanata ƙaryata kai wa farar hula hari.
Burtaniya ta bayyana suna 20 na mutanen da ta ce jami'an leƙen asiri ne. Ta zarge su da aiyuka a Turai da wasu yankunan, akwai wani sashen da ta ce ya mayar da hankali kan yammacin Afrika.
Ta bayar da misalan da suka hada da satar bayanai ta intanet da kutse da kuma yaɗa bayanan bogi a lokutan zaɓe.
Ɗaya daga cikin jami'an ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Hakeem Baba-Ahmed ya ce duk da cewa kowa ya amince cewa marigayi Muhammadu Buhari mutum ne mai gaskiya amma yana da nasa kura-kuran ta fuskar jagoranci.
Kamar kowane shugaba da ya bar mulki, masu lura da al'amura da ma ɗaiɗaikun 'yan Najeriya na ci gaba da waiwaye kan salon mulkin da marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gudanar.
Buhari ne mutum na farko da ya doke shugaban ƙasa mai-ci a Najeriya bayan samun nasara kan Goodluck Jonathan na PDP a zaɓen 2015 ƙarƙashin jam'iyyar APC, kuma ya yi wa'adi biyu har zuwa 2023.
Ɗaya daga cikin abubuwan da 'yan'adawa suka dinga siffanta salon mulkinsa shi ne "baba go slow" wato shugaba mai yin abubuwa sannu a hankali.
"Lokacin da Buhari ya sake dawowa ya nemi a zaɓe shi karo na biyu, wasu daga cikinmu mun ce kada a zaɓe shi. Dalili shi ne mun ce ba mu ga alamun sauyi ba na wahalhalun da aka sha," kamar yadda Hakeem ya bayyana.
Karanta cikakken labarin a nan cikakken labarin
Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya ta fitar da sabuwar gargaɗi kan yaduwar cututtuka masu saurin kisa a fadin ƙasar.
Hukumar ta ce ana fuskantar yaduwar cututtuka da suka haɗa da kwalara da cutar zazzabin cizon sauro da zazzaɓin dengue da cutar ƙyandar biri da kuma cutar mashaƙo a jihohi da dama.
Rahoton ya nuna cewa cholera ta bulla a jihohi 34, inda Jihar Zamfara ke da kaso mafi yawa. Sauran jihohin da abin ya shafa sun hada da Bayelsa da Adamawa da Delta da Lagos da kuma Rivers.
An kuma tabbatar da bullar zazzaɓin dengue a Jihar Edo, daga 9 zuwa 13 ga watan Yuni kamar yadda sakamakon binciken dakin gwaje-gwaje ya nuna.
Cutar shawara kuma ya bayyana a Abia da Anambra da Edo da Ekiti da Lagos da kuma Rivers, inda aka tabbatar da mutum bakwai sun kamu.
NCDC dai ta yi kira ga jama’a da su ƙara kula da tsafta, tare da karfafa rigakafi, musamman na cutar shawara domin kare lafiyars.
Wani jirgin Jamus ɗauke da ƴan Afghanistan 81 da aka samu da laifuka daban-daban a ƙasar.
Mutanen waɗanda za a mayar da su Kabul sun kasance rukuni na biyu da za a mayar Afghanistan tun bayan da Taliban da koma mulkin ƙasar a 2021.
Ministan harkokin cikin gidan Jamus, Alexander Dobrindt ya ce waɗanda ke cikin jirgin sun haɗar da masu manyan laifuka, yana mai cewa ƴan ƙasar ne suka bukaci komawarsu.
Ofishin kula da kare haƙƙin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce bai kamata a tilasta wa kowa zuwa Afghanistan ba, inda rayuwarsu ka iya shiga cikin hatsari.
Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei Bona Malwal da Kakakin Majalisar Dokoki ta riƙon ƙwarya ta Sudan ta Kudu, Rt. Hon. Jemma Nunu Kumba da kuma wakili na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Guang Cong sun ziyarci ofishin jakadancin Najeriya da ke Juba domin miƙa gaisuwar ta'aziyya da bayyana jimami da alhininsu kan rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.
Ambasada Akuei Bona Malwal ya miƙa wasikar ta’aziyyar ne a madadin shugaban ƙasar, Salva Kiir Mayardit, zuwa ga Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu.
Mista Guang Cong ya kuma cewa za a riƙa tunawa da Buhari a matsayin wanda ya tsaya tsayin daka wajen haɗin kai tsakanin ƙasashe da kuma yaƙi da cin hanci.
A nasa ɓangaren, muƙaddashin Jakadan Najeriya a Sudan ta Kudu, Tukur Yahaya Maigari, ya nuna godiya bisa nuna tausayawa da zumunci, yana mai cewa Buhari jagora ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima ga ƙasa, kuma wannan ziyara ta nuna kyakkyawar dangantaka da mutunta juna tsakanin ƙasashen biyu.
A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar da cewa shugaba Donald Trump na fama da rashin lafiya a jijiyoyinsa na ƙafa da ke haddasa jiyoyin gaza aikewa da jini zuwa zuciya, abin da ke sa jini ya taru a ƙafar ta kuma kumbura.
A yayin taron manema labarai da aka saba yi, sakataren watsa labaran fadar ta White House ya ce mista Trump mai shekaru 79 ya fahimci kumburi a ƙafafunsa abin da ya sa likitansa yin nazari kuma ya gano cewa cutar ɗaukar jini zuciya da jiyoyin ƙafafun suka gaza ce.
Hotunan baya-bayan nan sun nuna yadda aka ga Trump da ɗaure-ɗaure a bayan hannunsa. Fadar White House ta ce ɗaure-ɗauren da aka gani a bayan hannun shugaban ba su da alaƙa da cutar gaza kai jini zuciya da jiyoyin nasa ke fuskanta, inda fadar ta ce hakan ya faru ne sakamakon yawon gaisawa da jama'a.
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama da tsawa a wasu sassan ƙasar daga ranar Juma'a 18 ga watan Yuli zuwa Lahadi.
Cikin wani saƙon gargaɗi da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce za a fuskanci yanayi na saukar ruwan sama a wasu jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Borno da Yobe da Kaduna da Bauchi da kuma jihar Gombe.
Haka kuma hukumar ta ce za a samu matsakaicin ruwan sama da tsawa a wasu sassan jihohin Adamawa da Yobe da Sokoto da Zamfara da Bauchi da Borno da Gombe da Jigawa da Kaduna da kuma jihar Taraba.
Hukuma ta NiMet ta kuma yi hasashen samun ruwan saman a wasu sassan jihohin Plateau da Nasarawa da Abuja da kuma Benue.
Ma'aikatar ilimin Najeriya ta ce shugaban ƙasar ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa sunan tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari saboda jajircewa da ƙoƙarin da ya yi a ɓangaren ilimin ƙasar.
Jaridar Punch a Najeriya ta ambato wata sanarwa da ma'aikatar ilimin ta fitar ta hannun daraktan yaɗa labaranta, Folasade Boriowo na cewa Shugaba Tinubu ya amince da matakin ne saboda sauye-sauyen da Tinubu ya kawo wa fannonin ƙasar da dama.
A ranar Alhamis ne Tinubu ya sanar da sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa Jami'ar Muhamamdu Buhari a lokacin taron addu'o'i da karramawa ga tsohon shugaban da aka gudanar a fadar gwamnatin ƙasar.
Sanarwar ta ce Tinubu ya bayyana Buhari a matsayin dattijon ƙasa wanda gwamnatinsa ta fifita batutuwan tsaro da ceto tattalin arziki da yaƙi da rashawa da kuma sauye-sauyen yadda ake gudanar da hukumomi.
Ma'aikatar Ilimin ƙasar ta bayyana sauya sunan jami'ar a matsayin karramawa ga tsohon shugaban ƙasar, musamman yadda gwamnatinsa ta samar da manyan ayyukan gina ƙasa da al'umma.
Rikici mai nasaba da addini ya sake barkewa tsakanin Larabawa mazauna karkara da mayaƙan ƙabilar Druze a lardin Sweida da ke Kudancin Siriya, kwana guda bayan dakarun gwamnati sun ce Isra'ila ta yi luguden wuta.
Rahotannin sun bayyana yadda Larabawa mazauna karkara suke yi wa yankunan Sweida ƙawanya.
Bidiyon da BBC ta tantance ya nuna Larabawan Siriya mazauna karkaka na zagayawa cikin gine-ginen da suka kone.
Kusan mutum 600 aka kashe daga fara rikicin a ranar Lahadi.
Rikicin ya janyo Isra'ila, wadda ta ce tana goyon bayan mabiya addinin Druze tare da buƙatar sojin Syria su janye daga Yammaci.
Hukumar kula da ƴangudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargaɗin cewa mutum miliyan 11 da suka rasa muhallansu na cikin hatsarin rasa kayan agaji a wannan shekara saboda rage bayar da tallafi daga ƙetare.
Wannan adadi shi ne kusan kashi ɗaya bisa uku da mutanen da hukumar ke tallafawa.
Wani babban jami'in hukumar ya faɗa wa taron manema labarai a Geneva cewa abin da take da shi ba zai wadatar ba.
Ƙasashen Amurka da Faransa da Sweden da kuma Japan duk sun sanar da yin gagarumin ragi a tallafin da suke bai wa hukumar.
Ƙasa da kashi ɗaya cikin huɗu na abin da hukumar ke buƙata ne na dala biliyan 10.6 kawai ta samu zuwa yanzu.
Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce tsohon shugaban ƙasar, Marigayi Muhammadu Buhari ya hore shi da riƙe amanar talakawan ƙasar.
Yayin da yake jawabi a wajen ta'aziyar rasuwar Buhari a garin Daura, mahaifar marigayin, Peter Obi ya ce yana tuna kalaman da Buhari ya faɗa masa lokacin da yake raye.
''A lokacin da nake yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, na kai masa ziyara, kuma kiran da ya yi min shi ne, ya ce Peter ka kula da talakawan Najeriya, ni kuma na faɗa masa wannan shi ne babban muradina''.
Peter Obi ya ce babban abin da shugabanni za su koya daga halin Buhari shi ne sauƙin kansa.