Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Donald Trump na fama da lalurar jijiyoyin jini
- Marubuci, Bernd Debusmann Jr
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, White House
- Marubuci, Kwasi Gyamfi Asiedu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington DC
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Fadar shugaban Amurka ta White House ta sanar cewa Shugaban Donald Trump na fama da wata matsananciyar lalurar jijiya. Hakan na zuwa ne bayan kwashe kwanaki ana raɗe-raɗi, bayan da hotuna suka nuna wani abu tamkar koɗewa a fatar hannun shugaban.
Bayan samun wani kumburi a ƙafafunsa a kwanakin nan "An yi wa Trump binciken lafiya na ƙwaƙwaf" ciki har da gwajin jijiyoyin jini, kamar yadda sakatariyar ƴaɗa labarun fadar shugaban ƙasar, Karoline Leavitt ta bayyana.
Leavitt ta ce alamun da aka gani a fatar hannun Trump ya faru ne dalilin "koɗewar fata sanadiyyar shan hannu da mutane akai-akai" inda yake yawan shan ƙwayar maganin aspirin, wanda ta ce na daga cikin "matakan da aka saba amfani da su wajen kare cutukan hanyoyin jini".
Trump mai shekara 79 ya sha yin tutiya game da lafiyarsa, inda yakan bayyana kansa a matsayin "shugaban ƙasa mafi lafiya a tarihin Amurka".
Cutar da aka gano Trump na fama da ita, wato 'chronic venous insufficiency', wadda ke faruwa yawanci a lokacin da jijiyoyin da ke ƙafafu suka gaza harba jini zuwa zuciya, lamarin da ke sanyawa jini ya taru a ƙafa, kuma ya haifar da kumburi.
Jijiyoyi da bawul-bawul ɗin da ke cikinsu ne "suke tura jini sama zuwa wasu wuraren daga ƙafa" zuwa zuciya, in ji Dakta Meryl Logan, farfesar ilimin lafiya jijiyoyi a Jami'ar Texas da ke Austin.
Jinin da ke tasowa daga ƙafa suna yin sama na buƙatar harbawa, kuma wani lokaci abin na da wahala.
"Saboda haka ana samun 'chronic venous insufficiency' idan jijiyoyin da kuma bawul-bawul da ke cikinsu suka gaza yin aiki, sai jini ya koma ƙasa zuwa ƙafafu," kamar yadda ta shaida wa BBC.
Shugaban Amurka mafi tsufa a tarihi
Leavitt ta ce "ba a ga wata alama ta cutar dunƙulewar jini ko kuma na jijiyoyin da ke ɗaukar jini daga jijiya zuwa sassan jiki ba", sannan kuma duk wasu gwaje-gwaje da aka gudanar ba su nuna cewa akwai hatsari sosai ba.
Wani bayani da likitan fadar shugaban Amurka Sean Barbella ya fitar ga manema labarai, ya ce yanayin "bai da hatsari kuma abu ne da aka saba gani", musamman a mutanen da suka zarce shekara 70 a duniya.
Wasu ƙarin gwaje-gwaje da aka gudanar sun nuna cewa "babu alamun matsalar zuciya, ko na ƙoda ko kuma wanda ya shafi jiki" a tattare da Trump", kamar yadda Barbella ya bayyana a bayanin da ya fitar wanda ke tabbatar da bayanin Leavitt.
Hoton da aka ɗauka ya nuna kumburin da ke a ƙafar Trump a lokacin wasan ƙarshe na gasar cin kofin zakarun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na duniya da aka gudanar ranar 13 ga watan Yuli a jihar New Jersy da ke Amurka.
Haka nan wasu hotunan da aka ɗauka daga baya sun nuna yadda fatar hannunsa ta koɗe, musamman a lokacin ganawarsa da Firaiministan Bahrain Salman bin Isa Al Khalifa a fadar White House.
Haka nan an taɓa ganin irin wannan koɗewar fata a hoton da aka ɗauki Trump lokacin da ya gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron a watan Fabarairu.
Kumburin da aka gani a ƙafar tasa da kuma koɗewar wani ɓangare na fatar hannunsa sun janyo cece-ku-ce kan cewa akwai yiwuwar shugaban ƙasar na fama da wata cuta wadda ba a bayyana wa al'umma ba.
Trump na da shekara 78 da wata bakwai a duniya a lokacin da aka rantsar da shi a wa'adi na biyu na shugaban ƙasa a cikin watan Janairu, wannan ya Sanya ya zama mutum mafi yawan shekaru da aka rantsar a matsayin shugaban ƙasa a tarihin Amurka.
Mece ce lalurar jijiyoyin jini?
Likitoci sun faɗa wa BBC cewa sun gamsu da bayanin da likitan fadar White House ya yi kan lalurar jijiyoyin jini.
"Ana iya alaƙanta lalurar da da wasu cutuka masu hatsari, to amma ita kanta lalurar ba wata babbar matsala ba ce, kuma ana yawan samun mutane masu fama da ita," kamar yadda Dakta Matthew Edwards na Jami'ar Wake Forest ya shaida wa BBC.
"Mutane masu irin shekarunsa, zan iya cewa kamar kashi 10 zuwa 35% kan yi fama da irin wannan lalura."
Masana sun ce wasu abubuwan da kan haddasa irin wannan lalura su ne ƙiba fiye da kima, kasantuwar mutane masu lalurar dunƙulewar jini tsakanin iyaye da kuma yin aiki wanda ke buƙatar yawan tsayuwa.
Masana sun ce sukan shawarci masu irin wannan lalurar su riƙa ɗaga ƙafarsu a cikin dare domin rage illar da za ta iya yi musu.
"Nakan faɗa wa masu irin wannan lalaurar su riƙa amfani da wani man shafawa a ƙafarsu da tafin ƙafa a kullum, sannan su kauce wa wasu abubuwa da ke iya ƙara hatsarin samun lalurar, kamar yin ƙiba mai yawa," in ji Dakta Logan.
Me ya sa hannun Trump ya koɗe?
Lalurar jijiyoyin jinni na shafar ɓangaren jikin ɗan'adam na ƙasa-ƙasa ne, saboda haka koɗewar da aka gani a hannun Donald Trump ba ta da alaƙa da lalurar.
Likitan shugaban ƙasar ya ce koɗewar da aka gani a fatarsa ta samo asali ne daga yawan gaisawa da mutane da kuma yawan shan maganin aspirin, wanda ke kare mutum daga kamuwa da bugun zuciya ko dunƙulewar jini.
"Na san cewa idan wani ya matse maka hannu da ƙarfi, (za ka iya samun ƙujewa)," in ji Dakta Edwards