Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/08/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Aisha Babangida

  1. Rufewa

    Jama'a a nan muka kawo ƙarshen wannan shafin namu na labaran kai-tsaye daga BBC Hausa.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya.

    Da fata kun ji daɗin kasancewa tare da mu.

    A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana.

  2. WHO ta yi gargaɗin ta'azzarar cutar kwalara a duniya

    WHO

    Asalin hoton, AFP

    Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadi kan ƙara ta’azzarar matsalar cutar kwalara a duniya, inda aka samu bullar cutar a ƙasashe 31, wanda ke nuna cewa adadin mace-macen da aka samu ya ƙaru sosai.

    Matsalar tafi ƙamari a Sudan, inda sama da mutum 100,000 suka kamu da cutar, tare da kusan mutum 2,500 da suka mutu, tun daga watan Agustan bara zuwa yanzu.

    Sai dai WHO ta ce ƙasashen da ba su dade da samun bullar cutar ba, ciki har da Chadi da Jamhuriyar Kongo, suma yanzu na kan gaba wajen fuskantar ta.

    Hukumar ta ce jimilla sama da mutum 400,000 ne suka kamu da cutar, tare da kusan mutum 5,000 da suka mutu a bana, sakamakon rikice-rikice da talauci da kuma ambaliya.

  3. Aƙalla mutum 500,000 suka ɓace a duniya - Red Cross

    Red cross

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Red Cross ta ce kawo yanzu mutum fiye da dubu dari biyar ta yi wa rigista a matsayin waɗanda suka ɓace a duniya, adadi da ya ƙaru da kusan kashi 70 cikin 100 a tsawon shekaru biyar.

    Ƙungiyar ta ce yaƙin Sudan da Gaza da kuma Ukraine sune manyan dalilan ƙaruwar adadin, duk da cewa ainihin adadin ƙa iya zarta haka.

    Shugaban gudanarwar Kungiyar Agaji Ta Red Cross, Pierre Krahenbuhl, ya ce wannan hauhawar adadin babban tunatarwar ce akan yadda yaƙi da masu goyon bayansa suka kasa kare fararen hula.

    Hukumar dake da Hedikwata a Geneva, a bara ta ce adadin mutanen da suka ɓace sun kai dubu goma sha shida.

  4. Trump zai rage dala biliyan biyar daga kasafin kuɗin ƙasar

    Shugaba Donald Trump ya ce zai rage kusan dala biliyan biyar na tallafin ƙasashen waje da Majalisar Dokokin Amurka ta riga ta amince da su.

    Ya bayyana sabuwar niyya ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dokokin Amurkar.

    Jam’iyyar Democrats tayi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na sake dawowa da kudaɗen da aka riga aka amince da su ba tare da amincewar majalisar ba, zai kawo ƙarshen tattaunawar da ake yi akan sabon kasafin kuɗi kafin ƙarshen watan gobe, wanda zai iya kawo tsaiko ga harkokin gwamnati.

    Gwamnatin Trump ta riga ta dakatar da tallafin ƙasashen waje da dama, abin da ya haifar da tsaiko ga muhimman ayyuka tallafi a sassa daban-daban na duniya.

  5. Amurka ta tura baƙin haure bakwai na wasu ƙasashen zuwa Rwanda

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Rwanda ta sanar da karɓar mutum bakwai da aka mayar da su daga Amurka a cikin yarjejeniyar da ƙasar ta shiga da Washington kan karɓar baƙin haure na wasu ƙasashe da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda kafar jarida ta The New Times ta ruwaito.

    Kafar ta ruwaito daga mai magana da yawun ƙasar Yolande Makolo, cewa mutum bakwai sun isa ƙasar a cikin watan Agusta bayan tantancewa.

    Makolo ya ce uku daga cikin mutanen sun amince a mayar da su ƙasarsu ta asali, sauran kuma sun ce suna sha'awar zama a ƙasar Rwanda.

    Mutum bakwai ɗin suna cikin aƙalla mutum 250 da ake tunanin Amurka za ta mayar Rwanda a yarjejeniyar da suka shiga a watan Yuni.

  6. Amurka na yunƙurin hana Falasɗinawa halartar babban taron MDD

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta ce za ta hana jami'an Falasɗinawa izinin shiga ƙasar domin halartar babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da za a yi a watan gobe.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi mutanen Falasɗinu da ɓata yunƙurin samar da maslaha "domin dagewa wajen tabbatar da ƙasar Falasɗinu ƴantacciya."

    Kasancewar a Amurka ake gudanar da taron, tana da damar hana duk wanda ta ga-dama shiga ƙasar domin halartar taron.

    Hanawar na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke jagorantar tabbatar da kafa ƙasar Falasɗinu a taron na Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma Donald Trump na goyon bayan Isra'ila na yaƙi da tabbatar da aukuwar hakan.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyhu ya daɗe yana fafutikar hana kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin hanya ɗaya ta sasanci a rikicin Gaza, kamar yadda wasu ƙasashen duniya ke fata.

    Netanyahu ya ce tabbatar da ƙasar Falasɗinu tamkar lada zai zama "ga ayyukan Hamas na ta'addanci."

  7. Rikicin gona ya yi ajalin mutum 26 a Ghana

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 26 ne suka rasu a dalilin rikicin ƙabilanci kan filin gona a wani garin manoma a yankin Savannah na ƙasar Ghana.

    Daga cikin waɗanda suka rasu akwai mutum takwas da suka rasu a kifewar kwale-kwale a ranar Alhamis, duk da an samu sanarar ceto wasu mutum 20.

    An fara rikicin ne saboda rigimar filin gonaki tsakanin ɓangarorin biyu a garin Gbinyiri a ranar Lahadin, lamarin da ya sa sama da mutum 14,000 suka rabu da muhallinsu.

    Wasu ma tuni suka tsere zuwa ƙasar Côte d'Ivoire da ke maƙwabtaka da ƙasar.

    Rundunar ƴansandan Ghana tare da haɗin gwiwar jami'an tsaron ƙasar sun tura jami'an tsaro zuwa yankin domin kwantar da tarzomar.

  8. Borno ta ga bala'o'i kala-kala - Zulum

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Gwamnan jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya ce al'ummar jihar na ci gaba da gode wa Allah duk da irin bala'o'in da jihar ta fuskanta.

    "Abin akwai wahala, sai dai Allah ba ya ɗora wa mutum abin da ba zai iya ba.

    "Ga rashin kuɗi ga masifa da muka gani kala-kala, ga ambaliyar da aka yi fama da ita."

    Gwamnan ya fadi hakan ne a tattaunawar da ya yi da BBC shekara ɗaya bayan wata mummunar ambaliyar ruwa da ta faru a birnin Maiduguri.

    Ambaliyar ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu a babban birnin jihar, Maiduguri sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau, kuma lamarin ya haifdar da asarar rayuka da dama.

    Shekara ɗaya bayan haka, Babagana Zulum ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan ganin cewa irin haka ba ta faru ba a wannan shekara.

    Borno na cikin jihohin da hukumar lutra da yanayi ta Najeriya, Nimet ta yi gargadin cewa za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a daminar 2025.

    A yanzu gwamnatin jihar Borno ta gudanar da aikin faɗaɗawa da yashe madatsar ruwa ta Alau, inda daga can ne ruwan ya yi ambaliya a 2024.

    Borno ce cibiyar rikicin Boko Haram, wanda aka kwashe kimanin shekara 15 ana fama da shi.

    Rikicin ya haddasa asarar dubban rayuka tare da tarwatsa miliyoyi daga muhallansu.

  9. An tsige Firaminista Thailand Shinawatra

    Thailand

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun tsarin mulkin Thailand ta tsige Firaminista Petothan Shinawatra, bisa yadda ta tafiyar da rikicin kan iyaka da Cambodia.

    Ana zarginta da kasa tsayawa tsohon shugaban Cambodia, Hun Sayen.

    A wata tattaunawa ta wayar tarho da aka fallasa, ta yi magana da shi cikin kalami na soyayya tare da sukar wani janar ɗin Thailand.

    Alƙalan kotun tsarin mulkin sun yanke hukuncin an samu rashin ƙawarin gwiwa akanta.

    Sai dai Ms Petothan ta dage cewa ta yi iya ƙoƙarinta wajen kare muradun ƙasar ta.

  10. Za a ɓullo da sabbin dokokin yaƙi da tsattsauran ra’ayi a Kenya

    Kenya

    Asalin hoton, Reuters

    Wani jami’in gwamnatin Kenya ya ce za a kawo sabbin ƙa’idoji masu tsauri don yaki da tsattsauran ra’ayin addini da kuma kai mutane ga ɗabi’un ta’addanci, yayin da hukumomi ke fargabar wata mummunar kungiyar asiri da ake kira Doomsday ke ƙokarin dawowa.

    An gano gawarwaki kusan 30 a kwanakin baya a kusa da dajin Shakahola, an kuma gano wasu kaburburan rami da ke ɗauke da gawarwakin daruruwan mutane a tsawon shekaru biyu da suka gabata.

    Wakiliyar BBC ta ce hukumomin ƙasar sun kama mutum 11 da ake zargi inda uku daga ciki ake zargin tsaffin mabiyan Makanzi ne.

    An gano cewa sabbin 'yan kungiyar na hallaka kansu ta hanyar yunwa, abin da hukumomi ke fargabar na iya zama hanyar dawowar ƙungiyar asiri da ake kira Doomsday da Paul Maakanzi ke jagoranta, wanda ke fuskantar shari’a yanzu.

  11. Isra'ila ta gano gawar ɗaya daga cikin waɗanda ke hannun Hamas

    Isra'ila

    Asalin hoton, Israeli President

    Sojojin Isra'ila sun sanar da gano gawar wani dan Isra'ila da aka kashe ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta ƙaddamar da hari a ƙasar.

    An tafi da gawar Ilan Weiss, zuwa Gaza bayan an kashe shi lokacin da ya ke kokarin kare kibbutz.

    Sojojin Isra’ila sun ce sun ayyana birnin Gaza a matsayin filin Daa-ga, yayin da suke ƙara shirin kwace mafi girman wuraren da jama’a suka fi zama a yankin.

    Sojojin sun ƙara da cewa an ɗan dakatar da umarnin hana aiyukan jinƙai na ɗan lokaci a birnin Gaza, ko da yake mazauna yankin na cewa har yanzu abububa basu sauya ba a yanki.

    Isra’ila'r ta kuma ce ta gano gawar wani ɗan ƙasar ta da aka kashe a harin da Hamas ta kai na 7 ga watan Oktoba. Gawar Ilan Weiss, wanda aka kashe yayin ƙoƙarin kare yankinsu na Kabbutz.

  12. Ambaliyar ruwa a Sudan ta yi ajalin mutum 32

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Adadin mutanen da suka mutu sakamakon arambaliya da sama mai ƙarfi ta haddasa a sassa daban-daban na Sudan ya haura zuwa 32, yayin da dubban mutane suka rasa matsugunninsu, kamar yadda shafin Sudan Tribune mai zaman kansa ya ruwaito.

    Ruwan saman da ya fara a ranar 27 ga watan Agusta ya shafi jihohin arewa da ta tsakiya da gabas na ƙasar, inda jihar Kogin Nilu ta arewa maso gabas ta fi fuskantar asara da mutuwar mutane 23.

    An kuma ruwaito cewa ambaliyar ta tilasta wa kusan mutane 4,000 barin gidajensu tare da lalata dubban gidaje.

    Matsalar ta fi tsanani ga al’ummomin da suka fi rauni, ciki har da ‘yan gudun hijira da yaƙin basasa ya shafa, waɗanda galibi ke rayuwa a buɗe ko cikin ɗan tantin wucin gadi.

    A Sudan, lokacin ruwan sama na farawa ne daga ƙarshen watan Yuli har zuwa Oktoba, inda kusan mutane 500,000 suka fuskanci ambaliya a bara.

    A watan Yuli, Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa ambaliya na iya katse hanyoyin sufuri, ta hana isar da tallafi, tare da ƙara barazanar yaɗuwar cututtuka.

  13. Sojoji da DSS sun kashe ƴan bindiga 50 a jihar Neja

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Najeriya tare da jami’an tsaron farin kaya (DSS) sun kashe aƙalla ƴan bindiga 50 sannan kuma suka kuɓutar da wasu daga cikin mutanen ake garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mariga ta jihar Neja.

    Jami’an tsaron sun ce sun yi arangama da kusan ƴan bindiga 300 ɗauke makamai a ranar 26 ga Agusta, bayan sun yi ƙoƙarin kai hari a ƙauyen da kuma kai farmaki a sansanin DSS.

    Shugaban ƙaramar hukumar Mariga, Abbas Adamu ya tabbatar wa BBC cewa an kashe ƴan bindigan.

    "Gaskiya ne, shekaran jiya ne muka samu rahoton fitowar ‘yan bindiga daga jihar Zamfara suna tunkarar yankunanmu daga Katonkoro zuwa Kumbashi har zuwa Gulbin Boka."

    "Amma kafin su isa, mun sanar da jami’an tsaro da muke da su, ciki har da sojoji da ‘yansanda, da DSS, waɗanda suka yi iyakar ƙoƙarinsu wajen tare su domin hana su kai farmaki wuraren da suka saba."

    Amma kuma ya ce ƴan bindigan sun samu hanyar shiga Gulbin Boka inda suka yi garkuwa da mutane da dama.

    "Amma a hanyarsu ta komawa Zamfara, mun haɗa hannu da jami’an DSS a Kumbashi, inda muka fatattake su kuma muka kuɓutar da mutanen da aka sace, tare da ƙwato wasu dukiyoyin da suka sace"

    Abbas ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai daga ɓangaren mutanen gari ba, amma jami’ai sun hallaka kusan ‘yan bindiga 50 tare da ƙona dukkan baburansu.

    "Sai dai kuma an samu hasarar rayuka a cikin jami’anmu." in ji shi.

    Wannan lamari ya biyo bayan kama Abubakar Abba, shugaban kungiyar dabar Mahmuda a yankin Wawa na jihar, wanda DSS ta yi a kwanan nan.

  14. Cutar kwalara ta hallaka mutum 8 a Zamfara

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɓarkewar cutar cholera a gundumar Bukkuyum da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, ta yi sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas.

    Cutar ta kuma kama fiye da mutum 200 a cikin ƙauyuka 11, kamar yadda mazauna yankin da hukumomin ƙasa suka tabbatar a ranar Alhamis.

    Cutar kwalara cuta ce da ke yaɗuwa ta hanyar ruwa a Najeriya, inda hukumomin lafiya ke danganta yawaitar ta da ƙarancin tsaftataccen ruwa musamman a yankunan karkara da kuma unguwannin marasa galihu a birane.

  15. Gwamnatin Najeriya za ta sasanta rikici tsakanin jihohi da kamfanonin lantarki

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da rikici ke ƙara taɓarɓarewa tsakanin jihohi da kamfanonin rarraba wuta (Discos) kan wanda ke da ikon tsara farashin wutar lantarki, gwamnatin ta shiga tsakani ta hanyar hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC), inda ta gayyaci duk masu ruwa da tsaki zuwa taro a mako mai zuwa a Legas domin sasanta rikicin kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

    Kwamishinonin makamashi na jihohi sun jaddada cewa dokar wutar lantarki ta 2023 ta ba su ikon tsara kasuwannin wuta a yankunansu.

    Amma kamfanonin rarraba wutar lantarki sun yi iƙirarin cewa, duk da cewa dokar ta ba jihohi damar tsara kasuwannin wutar lantarki, ba su da ikon sanya farashin wutar da ke ketare iyakokin jihohi.

    Sakamakon haka, babu jihohi ko Discos da suke son sassauta matsayinsu kan wanda ke da ikon tsara farashin wutar lantarki.

  16. ASUU na barazanar shiga yajin aiki a jami’o’in Najeriya

    ...

    Asalin hoton, ASUU

    Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta bayyana cewa dukkan jami’o’in gwamnati kusan 150 da ke ƙarƙashin kulawar ta na iya shiga yajin aiki, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Wannan lamari ya biyo bayan da gwamnati ta musanta cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da ASUU, inda ta bayyana takardun da ƙungiyar ke magana a kansu a matsayin shawarwari ne kawai.

    Daga ranar Litinin din wannan makon, rassan ASUU daban-daban sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da ƙungiyar ko kuma a fuskanci yajin aikin da zai shafi ɗalibai kusan miliyan biyu a faɗin ƙasar.

    Manyan matsalolin sun haɗa da rashin biyan albashin watanni uku da rabi da aka hana da rashin biyan cikon kuɗin albashi na ƙarin matsayi da rashin sakin kuɗaɗen inganta jami’o’i da sauya sunan Jami’ar Maiduguri, da batun kudin ritaya ga malaman jami’a.

  17. Tinubu ya yi watsi da waɗanda suka taimake shi - Sanata Marafa

    Sanata Kabiru Marafa
    Bayanan hoto, Sanata Kabiru Marafa

    Yayin da siyasar Najeriya ke ɗaukar zafi gabannin zaben 2027, tsohon daraktan yakin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a jihar Zamfara, Senata Kabiru Marafa, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC mai mulki.

    A tattaunawarsu da BBC bayan taro da ɗaukacin magoya bayansa, Marafa ya bayyana cewa rashin magance matsalolin tsaro da wulaƙanta wasu jihohi na daga cikin manyan dalilan da suka sa ya bar jam’iyyar.

    “Babban matsayar da muka cimma ita ce mu yi watsi da APC a matakin jiha da ƙasa bisa dalilai na zaluntarmu da aka yi da na karya alƙawura da aka ɗauka a lokacin kamfen, wanda na jagoranta a jihar Zamfara kuma muka samu nasara,” in ji shi.

    Marafa ya ƙara da cewa, “Ɗaukacin jihohi bakwai na Arewa maso Yamma, jihar Zamfara da Jigawa, su kaɗai ne Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓe a lokacin, amma babu jihoin da aka wulaƙanta kamar Zamfara da Jigawa.'

    Ya ƙara da cewa "Duk waɗanda suka wahala da shi, su ne aka wulakanta, ba a yin komai da su, kamar mu a Zamfara, inda aka ba mu ƙasƙantaccen muƙami.”

    “Alƙawari a harkar tsaro har yanzu ba a aiwatar ba. Misali, an samu wasu kisan gilla a wani yanki da aka gudanar da zaɓen cike gurbi sati biyu da suka wuce, amma ba a ɗauki mataki ba. Amma lokacin zaɓen sai ga shi an kawo jami’an tsaro da yawa.” in ji Marafa.

    Ya ƙara da cewa, babu wani muƙami da aka bai wa magoya baya na ko ƙwaya ɗaya, abin da ya kara ƙarfafa dalilinsa na ficewa daga jam’iyyar.

  18. Amurka ta naɗa sabon shugaban hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar gwamnatin Amurka ta zaɓi sabon shugaban hukumar kula da cutuka masu yaɗuwa na kasar kwana guda bayan an tursasawa shugabar hukumar ta baya barin aikin.

    Jim O'Neil, wanda kwararre ne a ɓangaren fasaha, kuma shi ne mataimakain sakataren kula da harkokin lafiya na kasar zai maye gurbin Susan Monarez.

    Tsohuwar shugabar hukumar sun samu saɓani da sakataren harkokin kula da lafiyar ƙasar Robert F Kennedy akan wata manufa da ya ɓullo da ita game da wata rigafi da ake son samar da ita.

    Lauyoyinta sun ce Robert F Kennedy ne ya saka ta gaba bayan taƙi sanya hannu akan wata takardar umarni daga Mista Kenney wanda ta ce sam abin da ke kunshe cikin takardar ya saɓawa harkokin kiwon lafiya.

    Barin nata aiki ya janyo yawancin manyan jami'ai a hukumar barin aiki su ma.

  19. Kwastam ta kama tabar wiwi ta naira miliyan 48.5 a Kaduna

    ...

    Asalin hoton, Ngeria custom service

    Hukumar Kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa jami'anta sun kama tabar wiwi mai darajar naira miliyan 48.5 da wasu kayan da aka haramta na naira miliyan 220 a Jihar Kaduna kamar yadda Gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    Kwamandan hukumar ya ce an kama kayayyakin ne a ayyuka daban-daban da aka gudanar ranar 21 ga Agusta, 2025.

    Ya ce jami’an sashen bisa ingattatun bayanan da suka samu ne suka tsayar da mota a Zaria kan babbar hanyar zuwa Kano inda suka yi nasarar kama tabar wiwi ɗin da sauran kayan da aka haramta.

    Mai magana da yawun hukumar kwastam ya ce an miƙa wanda ake zargin da kayan ga jami’an hukumar yaki da ƙwayoyi ta Nigeria (NDLEA) don ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban shari’a bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomi.

  20. Amurka ta ƙara haraji kan ƙananan kayayyakin da ake shigo dasu daga ƙasashen waje

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta bullo da wani sabon haraji akan kayayyakin da ake shiga da su kasar ta akwatin gidan waya waɗanda ba su da tsada sosai.

    Tuni aka ɗora irin wannan haraji akan kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga China da kuma Hong Kong, yanzu kuma harajin zai fara aiki a kan kayan sauran ƙasashen duniya.

    Mai bai wa shugaba Trump shawara akan harkokin kasuwanci, Peter Navorro, ya ce sabon harajin zai rage shigar da ƙwayoyi cikin ƙasar ta Amurka da kuma samar da ayyukan yi.

    Masu suka dai sun ce wannan mataki zai shafi masu amfani da kaya a Amurkan ne, to amma Navorro, ya ce yanzu sai al'ummar ƙasar su koma siyan kayayyakin da aka yi daga ƙasarsu.