Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/07/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Badamasi Abdulkadir Mukhtar

  1. IMF ta rage hasashen bunƙasar tattalin arzikin Najeriya

    Naira

    Asalin hoton, Getty Images

    Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya rage hasashen da ya yi a kan bunƙasar tattalin arzikin Najeriya na 2024 zuwa kashi 3.1.

    Wannan na ƙunshe ne a cikin sabon rahoton asusun a kan tattalin arzikin duniya na watan Yulin 2024, wanda aka wallafa a ranar Talata.

    IMF ya ce an samu wannan koma baya ne saboda rashin bunƙasar tattalin arzikin a zangon farko na wannan shekarar.

    A bisa sabon hasashen, an samu raguwar kashi 0.2 a bunƙasar tattali arzikin Najeriya, wanda a baya aka yi hasashen zai tashi da kashi 3.3 cikin ɗari.

    Amma IMF ta ce tattalin arzikin Najeriyar zaii bunƙasa da kashi 3.0 a cikin 2025.

    Dama dai hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar da wasu alƙalumma da ke nuna cewa tattalin arzikin ƙasar da ake samarwa a cikin gida zai ragu zuwa kashi 2.98, a zangon farko na 2024, daga kashi 3.46 da aka samu a zangon ƙarshe na 2023.

  2. Sudan ta yi watsi da buƙatar jibge sojin Iran a gaɓar tekun Maliya

    Sudan ta ƙi amincewa da buƙatar Iran ta kafa cibiyar dakarunta na ruwa ta dindindin a gaɓar tekun Sudan.

    Iran ta buƙaci hakan ne a wani ɓangare na yarjejeniyar tallafawa dakarun Sudan wajen yaƙi da mayaƙan RSF.

    Sudan ta ce ta ƙi amincewa da buƙatar ne saboda damuwar da ake da ita cewa yin hakan zai iya janyo martani daga Saudiyya da Masar da kuma ƙasashen Yamma.

    Daga baya Iran ta canza buƙatar zuwa neman kafa wata tashar ruwa domin hada-hadar kasuwanci da kuma ayyukan soji, amma jami'an Sudan sun ƙara yin turjiya ga hakan.

    Sai dai akwai rahotannin cewa duk da rashin amincewa da wannan buƙata, Iran ta ci gaba da bai wa Sudan jiragen yaƙi marasa matuƙi.

    A watan Fabrairu tsohon ministan harkokin wajen Sudan, Ali al-Sadiq ya gana da shugaban Iran, marigayi Ebrahim Raisi da kuma tsohon ministan harkokin wajen Iran, marigayi Hossein Amir-Abdollahian, a birnin Tehran inda suka tattauna batun ƙulla yarjejeniyar ikin soji tsakanin ƙasashen biyu.

  3. Ƙungiyar IS ta ɗauki nauyin kai harin masallacin Oman

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ƙungiyar IS ta ɗauki nauyin kai harin masallacin Oman da ya yi sanadiyar mutuwar mutum shida da jikkata wasu talatin a ranar lititnin.

    Ƴan ƙungiyar uku ne suka mutu a wajen kai harin.

    Ƙungiyar dai ta kai harin ne a masallacin ƴan shi'a a ranar Ashura, wato ranar da suke taron tinawa da kisan da aka yi wa ɗaya daga cikin jikokin Annabi Muhammad SAW.

    Harin dai ya haifar da fargabar sake samun wasu sabbin hare-haren ƙungiyar a ƙasar.

  4. Biden zai yi sauye-sauye a kotun ƙolin Amurka

    Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Biden na tunanin goyon bayan wasu sauye-sauye ga kotun ƙolin Amurka ciki har da kawo ƙarshen naɗe-naɗen muƙamai na dindindin kamar yadda kafofin yaɗa labaran Amurka suka ruwaito.

    Shugaba Biden ya yi jinkirin ɗaukar matakin kawo sauye-sauyen, saboda irin wannan yunƙurin ba lallai ya yi nasarar tsallake majalisar da ke ɗauke da ƴanmajalisar jam'iyu daban-daban ba.

    Fadar White house dai ta ƙi cewa komai kan batun.

    Tsohon shugaban ƙasar Donald Trump ne ya naɗa uku daga cikin shugabannin kotun, kuma sune suka gabatar da jerin hukunce hukunce kan gwamnatin Biden da suka haɗa da dokar ma'aikatun gwamnati da dokar bindiga da bashin karatu da kuma shari'ar da ake yi waTrump.

  5. Turkiyya da Nijar suna tattaunawar ƙulla ƙawancen soji da tattalin arziki

    Tchiani

    Asalin hoton, Reuters

    Wata tawagar manyan jami'an gwamnatin Turkiyya ƙarƙashin jagorancin ministan harkokin wajen ƙasar, Hakan Fidan ta iya hamhuriyar Nijar gabanin taron tattaunawar bunƙasa tattalin arziki da haɗakar aikin soji.

    Tawagar ta ƙunshi ministocin tsaro da makamashi da albarkatun ƙasa da kuma shugaban hukumar leƙen asirin Turkiyya.

    Wata kafar yaɗa labarai mai zaman kanta, ActuNiger wadda ta fitar da labarin ta ce wannan ne karon farko da manyan jami'an Turkiyya ke ziyartar Nijar tun bayan da sojoji suka ƙwace mulkin ƙasar a cikin watan Yulin bara.

    ActuNiger ta ruwaito cewa ziyarar ta jami'an Turkiyya bibiya ce game da wata irin ta da firaiministan Nijar, Ali Lamine Zeine ya kai birnin Ankara a farkon wannan shekarar.

    Turkiyya ta kasance jigo wajen haɗakar aikin soji da ƙasashen yankin Sahel kuma wannan alaƙa ta kai shekara 10 tana gudana.

    Ƙasashen biyu sun kuma ƙulla yarjejeniyar cinikin makmai da sauran kayan aikin soji, inda Turkiyya za ta bai wa Nijar jirgin yaƙi maras matuƙi ƙirar Byraktar TB2 da kuma sauran makamai da hamɓararren shugaban ƙasar Mohammed Bazoum ya saya.

  6. Gwamnan Kano ya naɗa sabbin sarakuna uku masu daraja ta biyu

    Abba kABIR

    Asalin hoton, KNSG

    Gwamnan Kano a arewacin Najeriya, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sarakuna uku masu daraja ta biyu a jihar.

    Sanarwar da daraktan yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature, ya fitar ta ce sarakunan da aka amince a naɗa su sun haɗa da Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin sarkin Karaye, da Muhammad Isa Umar, a matsayin sarkin Rano da kuma Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin sarkin Gaya.

    Sanarwar ta ƙara da cewa naɗin sabbin sarakunan ya fara aiki nan take.

    Hakan na nufin gwamnan ya mayar da Aliyu Ibrahim Abdulkadir kan karagarsa ta sarkin Gaya bayan sauke shi sakamakon soke dokar masarautu ta 2019 da majalisar dokokin jihar ta yi. Sai dai wannan karon a matsayin mai daraja ta biyu.

    A bisa tanadin sabuwar dokar ƙananan masarautu da gwamnan ya sanya wa hannu, masarautar Rano ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da kuma Bunkure.

    Masarautar Gaya kuma ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Albasu da kuma Ajingi, yayin da kuma masarautar Ƙaraye da ta ƙunshi Ƙaraye da Rogo.

    Gwamna Abba Ƙabir ya yi bayanin cewa sabbin sarakunan masu daraja ta biyu za su kasance ƙarƙashin masarautar Kano mai daraja ta ɗaya tare da tallafa wa sarkin wajen tafiyar da harkokin mulki a masarautun nasu.

  7. Medecins sans Frontieres ta roƙi ƙungiyoyin agaji su koma ayyukan su a Sudan

    Shugaban ƙungiyar agaji ta Medecins sans Frontieres ya roƙi sauran ƙungiyoyin agaji da su koma Sudan domin tallafawa ƴan ƙasar.

    Dr Christos Christou ya ce ƙungiyar MSF din na magana da dukkan ɓangarorin dake yaƙi da juna domin ganin sun bada damar shigar da kayan agaji ga miliyoyin ƴan sudan dake cikin matsanciyar yunwa da rashin ruwa da muhalli sakamakon yaƙin da aka kwashe watanni 15 ana gwabzawa.

    Ya ce halin da sudan ke ciki shine mafi muni a duniya da aka taɓa fuskanta a ɓangaren ayyukan agaji.

  8. Trump ya samu goyon bayan tsofaffin abokan hamayyarsa

    Trump

    Asalin hoton, Pool

    Yayin da aka shiga rana ta biyu ta gagarumin taron jam'iyar Republican a Amurka, tsofaffin abokan neman takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar sun nuna goyon bayanansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa, Donald Trump.

    Sun rika yabawa da koda Trump a kan manufofinsa na tattalin arziki da bin doka da oda da kuma musamman kan baki ko shigi da fice.

    Shararrariyar ƴar kasuwar nan kuma tsohuwar jakadiyar Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta ce a lokacin mulkin Obama, Shugaba Putin ya mamaye Crimea, haka kuma ya sake mamaye Ukraine a lokacin mulkin Joe Biden.

    Ta ce amman lokacin mulkin Donald Trump babu mamaye, babu yaƙe-yaƙe, saboda Putin ya san Donald Trump baya da wasa.

  9. Barka da zuwa

    Barka da zuwa shafin labaran kai-tsaye na BBC Hausa.

    Badamasi Mukhtar da Umar Mikail ne ke fatan za ku biyo mu domin samun rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya a yau Laraba.