Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Gwamnan Rivers ya rubuta wa majalisar jihar wasiƙar sake gabatar da kasafin kuɗi

    Siminalayi Fubara

    Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X

    Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya sake rubuta wa majalisar dokokin jihar wasiƙar sanar da ƴanmajalisar aniyarsa ta sake gabatar da kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025, domin neman amincewarsu.

    Cikin wasiƙar da gwamnan ya aike wa kakakin majalisar dokokin jihar, Martin Amaewhule ranar Alhamis ya ce yana son gabatar da kasafin a gaban ƴanmajalisar a ranar Laraba 19 ga watan Maris, ko a wata rana cikin watan Maris da majalisar ke ganin zai fi dacewa.

    Fubara ya ce matakin biyayya ce ga hukuncin Kotun Ƙolin ƙasar, da kuma buƙatar da ƴanmajalisar suka yi masa na sake gabatar musu kasafin kuɗin jihar.

    A cikin wasiƙar gwamnan ya tuna wa kakakin majalisar zuwansa zauren majalisar a ranar Laraba da nufin gabatar da kasafin, amma sai aka kulle ƙofar aka hana shi shiga tare da tawagarsa.

    “Za ka iya tuna ziyarar da kawo majalisar a ranar Laraba 12 ga watan Maris domin gabatar da kasafin, domin biyayya ga hukuncin Kotun Ƙoli, amma ba a ba ni damar shiga zauren majalisar ba'', kamar yadda wani ɓangare na wasiƙar ya nuna.

  2. 'Amurka ba za ta ajiye makaman nukiliyarta a Poland ba'

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya ce Donald Trump ba zai goyi-bayan bukatar Poland na ajiye makaman nukiliyar Amurka a ƙasarta ba.

    Shugaba Poland, Andrzej Duda, ya fada wa BBC cewa wannan mataki zai ƙara musu ƙarfi da tabbatar da tsaro, daga duk wata barazana ta Rasha a nan gaba.

    Sai dai a lokacin tattaunawa da kafar yaɗa labarai ta FOX News, Mista Vance ya ce zai yi matuƙar mamaki muddin shugaban Amurka ya nuna zai amince a ajiye wani makami na Nukiliya a gabashin Turai.

  3. Fatan Amurka na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine ya gamu da cikas

    Fatan Amurka na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Ukraine ya gamu da cikas, bayan Shugaba Putin ya gindaya wasu sharuɗan masu tsauri da suka shafi yarjejeniyar da Washington ta gabatar.

    Shugaba Trump ya yi maraba da martanin nasa, amma ya ce akwai sauran rina a kaba.

    Mista Trump ya kuma nuna zai yi matuƙar takaici idan Rasha ta yi watsi da yarjejeniyar baki ɗaya.

    Yayin da shi kuma shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ke ganin kamar akwai surkulle a lamarin nasu.

    Mista Putin dai ya ce yana tsoron ya fito kai-tsaye ya faɗa wa Mista Trump cewa yana son a cigaba da wannan yaki.

  4. Assalamu alaikum

    Masu shafin BBC Hausa barkanmu da safiyar ranar juma'a Hajji babbar rana, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin jan ragamar wannan shafi.

    Sai ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawar kan labaran da muke wallafawa.