Mu kwana lafiya
Mun kawo ƙarshen rahotonnin a wannan shafin.
Za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/03/2025
Haruna Ibrahim Kakangi, Nabeela Mukhtar Uba, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail
Mun kawo ƙarshen rahotonnin a wannan shafin.
Za mu kawo muku wasu sababbin rahotonnin gobe da safe.

Asalin hoton, Getty Images
Wata kotu a Finland ta yanke wa wani ɗan Rasha hukuncin ɗaurin rai-da-rai saboda kama shi da laifin aikata laifukan yaƙi a gabashin Ukraine a 2014.
Voislav Torden mai shekara 38 na cikin dakarun sojin haya na Rasha mai suna Rusich, kuma an kama shi da laifi kan tuhuma huɗu tare da wanke shi kan guda ɗaya.
Tuhume-tuhumen sun danganci kwanton ɓauna da kuma harbe-harbe a yankin Luhansk na Ukraine, inda aka kashe sojojin Ukraine 22 da kuma raunata wasu huɗu. Torden ya musanta zarge-zargen.
Wannan ne karon farko da aka tuhumi wani mutum da laifukan yaƙin a Finland game da yaƙin na Ukraine.

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Flying Eagles ta matasan ƴanƙwallon Najeriya ƴan ƙasa da shekara 20 za su yi atisaye domin tafiya gasar kofin Afirka na ƴan ƙasa da shekara 20.
Sanusi Mohammed, sakatare janar na hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa gwamnatin jihar Katsina ce za ta ɗauki nauyin zaman atisayen ƴan ƙwallon.
Sanarwar ta ƙara da cewa tawagar ƴan wasan za ta yi atisayen ne kafin ta tafi gasar kofin ƴan ƙasa da shekara 20 da za a fafata tsakanin 26 ga watan Afrilu zuwa 18 ga Mayun 2025 a birnin Abidjan da ke ƙasar Cote d’Ivoire.
Tawagar Flying Eagles za ta fafata wa Masar da Moroco da Afirka ta Kudu ne a rukunin B na gasar.

Asalin hoton, State House
Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotonnin da ta ce "na ƙarya" ne da ake yaɗawa cewa ana kashe Kiristoci da gangan a ƙsar ta yammacin Afirka.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar a yau Juma'a ba ta bayyana takamaimai masu yaɗa rahotonnin ba, amma ta ce ana yi ne da zimmar sauya tunanin ƙasashen waje kan Najeriya.
"Abin takaici, ana yin wannan ne da zimmar sauya tunanin ƙsashen waje, musamman Amurka domin ta ayyana Najeriya a matsayin ƙasar da ake da shakku a kanta [CPC]," in ji sanarwar.
"Ya kamata a sani cewa matsalolin tsaron da ke faruwa a jihohin arewaci inda Musulmi ke da rinjaye, ba don a kai wa wasu mabiya addini hari ake yin su ba.
"Duk wani rahoto da ke yaɗa irin wannan manufar ngurɓatacce ne."

Asalin hoton, Reuters
Ma'aikatar tsaro ta Rasha ta ce "bayan ƙwaƙƙwaran matakin" da dakarunta suka ɗauka, sun ƙwace yankuna 28 a yankin Kursk na ƙasar da Ukraine ta mamaye.
Cikin yankunan har da Sudzha, in ji ta.
Ta kuma dakarunta sun ƙwace iko da wani gari a yankin Sumy na Ukraine ɗin, inda kafar yaɗa labaranta ta Zvezda TV ta ce a makon da ya gabata hakan ta faru.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi iƙirarin cewa ya nemi Shugaba Putin na Rasha ya rangwanta wa dakarun na Ukraine da ke cikin yankin Kursk.
Putin ya yi iƙirarin cewa dakarunsa sun kewaye sojojin Ukraine a yunƙurin da suke yi na ƙwace iko da shi.
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi Iran da amfani da abubuwan fasahar zamani da manhajar leken asiri domin hukunta wadanda ake ganin suna karya doka musamman mata wadanda ba sa bin dokokin sanya sutura masu tsauri.
Wani sabon bincike na Majalisar suka yi ya gano cewa jami'an tsaron Iran na amfani da wata manhaja ta musamman da aka sanya a wayoyin wasu mutane domin su rinka bayar da rahoton duk matan da ake zargin sun saba dokar sanya tufafi.
Wakiliyar BBC ta ce a yanzu ana sanya wa matan Ido ta hanyar amfani da kamarorin leken asiri dama jirage marasa matuka domin tabbatar da cewa sun sanya tufafin da gwamnati ta amince da su.
A 2022 ne aka gudanar da gagarumar zanga zanga a kasar bayan mutuwar wata matashiya 'yar shekara 22 Mahsa Amini a lokacin da ake tsare da ita saboda ta karya dokokin sanya tufafi.

Asalin hoton, Sokoto State Gov
Gwamnan jihar Sokoto, Dokta Ahmed Aliyu ya ƙaddamar da tallafin azumi ga ƴangudun hijira 77,000 da ke zaune a sassan jihar daban-daban.
Cikin wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, ta ce matakin na cikin wani yunƙuri na gwamnatin jihar don tallafa wa waɗanda suka rasa muhallansu domin su samu sauƙin gudanar da bukukuwan sallah da ke tafe.
A lokacin bikin ƙaddamar da tallafin, gwamnan ya ce kowace mace da ke sansanin ƴangudun hijira a jihar za ta samu tallafin turmin atamfa da buhun shinkafa mai nauyin kilogram 10, tare da kuɗin da bai bayyana adadinsu ba.
Yayin da ya ce kowane magidanci da ke zaune a sananin zai samu tallafin shadda da kuma kuɗi.
Ahmed Aliyu ya kuma alƙawarta yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da komawar mutanen garuruwansu domin su ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali.
Jihar Sokoto dai na fama da matsalolin tsaro, wani abu da ke tilasta wa mutanen wasu ƙauyuka da garuruwa barin gidajensu domin komawa zazamn gudun hijira a wasu garuruwan.

Asalin hoton, Getty Images
Rasha da Ukraine sun kai hare-hare da jirage marasa matuƙa cikin dare duk da tattaunawar tsagaita wutar da ake tsakanin jakadan Shugaba Trump da kuma Shugaba Putin.
Hare-hare da jirage marasa matuƙan da Ukraine ta kai sun faɗa Moscow kan wata matatar mai mai matuƙar muhimmaci ga Rasha da ke yankin Krasnodar a kudu maso yammacin Rasha.
Harin da Rasha ta kai Ukraine kuwa ya faɗa ne kan birni na biyu mafi girma a Ukraine ɗin wato Kharkiv inda mutum bakwai suka samu rauni.
Mai shiga tsakani daga Amurka Steve Witkoff, ya bar Moscow bayan samun abin da Rasha ta kira sabon bayanai.
A ranar Alhamis Mista Putin ya ce akwai buƙatar a sake zama a duba abubuwa da dama da ke cikin yarjejeniyar tsagaita wutar kafin ta fara aiki.

Asalin hoton, Nig Police
Hukumomin ƴansanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun cafke wata mata bisa zarginta da kashe kishiyarta ta hanyar zuba mata ruwan zafi.
Lamarin ya faru ne a ƙauyen Buju da ke ƙaramar hukumar Dutse babban birnin jihar Jigawa, kuma bayanai na cewa matar ta rasa ranta ne sakamakon rashin jituwar da ta kaure tsakaninta da abokiyar zamanta.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam ya shaida wa BBC cewa matar ‘yar shekara 20 ta watsa wa abokiyar zamanta tafasasshen ruwan zafi ne, sakamakon taƙaddamar da ta kaure tsakaninsu.
SP Shi’isu Adam ya ce marigayiyar ta samu mummunan ƙuna, inda aka kai ta asibiti daga baya kuma ta rasu a can.
Mai unguwar ƙauyen, Malam Kabiru Abbas ya shaida wa BBC cewa bayan ƙura ta lafa, wadda aka watsa wa ruwan zafin, kafin ta rasu ta kai masa ƙorafi, inda ya ba ta shawarar zuwa ofishin ƴansanda domin shigar da ƙorafinta.
Ya ƙara da cewa sai da ta shafe mako guda tana fama da jinya, kafin ta rasu, sakamakon munanna raunukan da ta ji saboda ƙunar.
Kakakin ƴansandan ya ce tuni suka kammala tattara bayanai kuma domin tura ta kotu.
Hamas ta ce a shirye take ta saki sauran Amurkawa 'yan asalin Isra'ila da ta ke rike da su masu rai da kuma bayar da gawar mutum hudu da suka mutu a yayin da take tsare da su.
Wakiliyar BBC ta ce cikin wata sanarwa yanzu Hamas ta ce ta amince ta mika matashin sojan nan na kasar Amurka da ke zaune a Isra'ila da kuma gawawwaki hudu na wadanda suka mutu a hannunta a lokacin da take tsare da su.
A bangare guda kuma, Hamas ta ce ta karbi sabon kundin yarjejeniyar tsagaita wuta daga masu shiga tsakani na Qatar da kuma Masar, kuma za ta bayar da amsa mai dadi.
To amma duk da haka kungiyar ta Hamas ba ta bayyana abin da take bukata da za a yi mata ba.

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar Premier na wata-wata karo na bakwai a tarihin.
Mohamed Salah ya lashe kyautar watan Fabrairu a matsayin ɗan wasan da ya fi hazaƙa a watan, bayan da bajintar da ya yi a watan, a ƙoƙarin da ƙungiyarsa ke yi na lashe gasar Premier.
Ɗan wasan na ƙasar Masar ya ci ƙwallo shida, ciki har da biyu da ya zura a ragar Bournmouth da wanda ya zura a ragar Manchester City a watan, sannan ya taimaka aka ci huɗu.
Mo Salah ya samu kyautar ne bayan doke Beto da Jean-Philippe Mateta da Yankuba da Djed Spence da kuma Dominik Szoboszlai.
Da wannan nasara, a yanzu Salah ya kamo tarihin da Sergio Aguero da Harry Kane suka kafa na cin kyautar sau bakwai.
Sannan ya zarta Steven Gerrard da Cristiano Ronaldo waɗanda suka ci kyautar sau shida.
Salah ya samu kyautar ce a watannin Nuwamban 2017 da Fabrairun 2018, da Maris ɗin 2021 da Oktoban 2021 da Oktoban 2023 da Nuwamban 2024 sai kuma Fabrairun 2025.

Asalin hoton, Adewole Adebayo
Jagoran jam'iyyar SDP na ƙasa, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar jam'iyyar a zaɓen 2023, Adewole Adebayo ya ce duk wanda ya shiga jam'iyyar tasu, yana sane da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugabancin ƙasar, kamar yadda ƴan jam'iyyar suka riga suka sani.
Cikin wata hira da gidan talbijin na Arise TV, Mista Adebayo yana da ƙwarin gwiwar sake yi wa jam'iyyarsa takara a zaɓen 2027, duk kuwa da irin manyan ƴan siyasar da ake sa ran za su koma jam'iyyar.
Ɗan siyasar ya ce ba ya fargabar rasa takara, duk kuwa da samun sabbin ƴan siyasar da ke shiga jam'iyyar daga wasu jam'iyyun.
“Ai duk mutumin da yake ganin shigowar wasu jam'iyyarsa zai zame masa barazana, ba zai iya zama shugaban Najeriya ba.”
“Ku fahimci wani abu, ba na damuwa da waɗanda ke shigowa jam'iyyarmu, duk wanda ya shigo yana sane cewa ni ne zan yi wa jam'iyyar takara a 2027'', kamar yadda ya bayyana a hirar.
Kalaman na Mista Adewole na zuwa ne kwanaki bayan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya koma jam'iyyar ta SDP bayan ficewa daga APC.
Jagoran SDPn ya kuma yaba wa El-Rufai bisa kasancewarsa jigo a siyasar Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai katse bayar da agaji ga mutum miliyan guda a Myanmar saboda rashin kuɗi.
WFP ya ce idan bai samu dala miliyan 60 da zai ci gaba da samar da tallafin abincin ba, dole ya dakatar da ayyukansa a wasu yankunan kasar da yaki ya daidaita.
Shirin ya ce yan gudun hijirar Rohingya 100,000 da ke zaune a sansanonin yangudun hijira a jihar Rakhine, waɗanda suka dogara kacokan kan tallafin, na daga cikin wadanda lamarin zai shafa.
To sai dai WFP bai bayyana ko rashin kuɗin na da alaka da katse tallafin da gwamnatin Trump ta ɓullo da shi ba.
A yanki West Java na ƙasar Indonsiya, dubban mutane ne ke ziyartar kogon Safarwadi, inda suka yi amannar cewa yana da wata ɓoyayyiyar ƙofa da ta ɓulle zuwa Makkah.
Wasu na zuwa ne domin tabbatar da ko batun gaskiyar ne, wasu kuma na zuwa ne domin samun albarkar ruwan da ke cikin kogon.
Shin gaskiya ne ko kuwa shaci-faɗi?

Asalin hoton, Getty Images
A karon farko farashin zinare ya zarta dala 3,000, kuma shi ne karo na 13 da farashin ke ƙaruwa a wannan shekara.
Farashin ma'adinin mai daraja ya ci gaba da tashi tun bayan hawan shugaba Donal Trump na Amurka.
Rahotonni na cewa ƙarin haraje-haraje da ya ƙaƙaba da yaƙin kasuwanci da barazanar da manyan ƙasashen duniya ke yi wa juna, sun taka muhimmiyar rawa wajen ƙaruwar buƙatar zinaren.

Asalin hoton, Getty Images
Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya cire ɗan wasan bayan Ingila Harry Maguire cikin jerin ƴanwasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026.
Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma'a ya sanar da sunan Marcus Rashford bayan cire shi a wasannin baya.
Haka ma kocin ya saka sunan tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar.
A karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar
A ranar Juma'a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila za ta ƙarbi baƙuncin Albania a filin wasa na Wembley, kafin ranar Litinin 24 ga watan na Maris ta kara da ƙasar Latvia a wasannin neman gurbin.
Ga jerin ƴan wasan 26 ga Thomas Tuchel ya fitar domin fafatawa a wasannin.
Masu tsaron raga: Dean Henderson (Crystal Palace), Jordan Pickford (Everton), Aaron Ramsdale (Southampton), James Trafford (Burnley)
Ƴanwasan baya: Dan Burn (Newcastle United), Levi Colwill (Chelsea), Marc Guehi (Crystal Palace), Reece James (Chelsea), Ezri Konsa (Aston Villa), Myles Lewis-Skelly (Arsenal), Tino Livramento (Newcastle United), Jarell Quansah (Liverpool), Kyle Walker (AC Milan, loan from Manchester City)
Ƴan wasan tsakiya: Jude Bellingham (Real Madrid), Eberechi Eze (Crystal Palace), Jordan Henderson (Ajax), Curtis Jones (Liverpool), Cole Palmer (Chelsea), Declan Rice (Arsenal), Morgan Rogers (Aston Villa)
Ƴan wasan gaba: Jarrod Bowen (West Ham United), Phil Foden (Manchester City), Anthony Gordon (Newcastle United), Harry Kane (Bayern Munich), Marcus Rashford (Aston Villa, loan from Manchester United), Dominic Solanke (Tottenham Hotspur)
Albarkacin makon yaƙi da cutar Glaucoma ta Duniya, Dakta Aisha Sheriff Kalambe ta faɗi yadda za ku iya gane ko kuna da Glaucoma mai janyo makanta.

Asalin hoton, Nigerian Presidency
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa.
Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar ƴan majalisa ta uku - wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku - da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce a baya ƙasar na kashe kuɗaɗen yaran ƙasar da ba a kai ga haihuwarsa ba.
"Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kuɗaɗen yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kuɗin shiga. Ba a yi wani tsari na tallafa wa yaran da za a haifa a gaba ba," kamar yadda ya ce.
Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama'a.
"Mun fuskanci tarin ƙalubale a lokacin da na karɓi mulki. Inda ba mu ɗauki matakai ba da yanzu ƙasar ta talauce, kuma ai haƙƙinmu ne mu kare tattalin arzikinmu daga rugujewa'', in ji Shugaba Tinubu.
To amma shugaban ya ce a yanzu kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu dangane da sauye-sauyen da gwamatinsa ta fara ɓullo da su.
"Amma a yau bayan shimfiɗa mai kyau da muka yi, mun smau nasarar magance matsalolin da suka tunkaro ƙasarmu, a yanzu canjin kuɗi ya daidaita, farashin abinci na ci gaba da sauka, musamman a lokacin Ramadan, da yardar Allah wahalar ta zo ƙarshe'', a cewar shugaban na Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta ayyana haramta duka kayayyakin da aka shigar da su ƙasar daga Kenya, a wani mataki na martani karɓar baƙuncin RSF da ƙawayenta da Nairobin ta yi.
Ministan kasuwancin Sudan, ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar, majalisar ikon ƙasar, wadda ta zargi Kenya da rura tashin hankali a Sudan.
A ganawar da aka yi a Nairobi ce, RSF ta yanke shawar kafa gwamnatin ƴan adawa a wuraren da take iko da su tare da sanya hannu kan abin da ta kira 'rubuta kundin tafiyar gwamnatin'.
Sudan ce ƙasa ta 10 a duniya, sannan ta biyu a Afirka, cikin jerin ƙasashen da suka fi sayen ganyen shayin Kenya.

Asalin hoton, EFCC
Hukumar EFCC, mai yaƙi da almundahana a Najeriya ta gurfanar da wata mata da mijinta bisa zargin sojan gona da sunan mai ɗakin gwamnan jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda domin damfar kuɗin da suka kai naira miliyan 197,750,000.
EFCC ta gurfanar da su a gaban babbar kotun jihar Kaduna tare da wasu mutum biyu da ke taimaka musu wajen gudanar da mugunyar sana'ar.
Hukumar ta zargi mutanen huɗu da haɗin baki wajen damfarar waɗannan kuɗaɗe ta hanyar fakewa da sunan mai ɗakin gwamnan Katsina, da nufin neman canjin dala.
EFCC ta zargi matar da ayyana kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, inda take buƙatar a yi mata canjin dala, daga wani mai sana'ar canji.
Mijin nata, ya samar mata da layukan waya da aka yi wa rajista da sunan Fatima Dikko Radda, domin ɓad-da-bami ga manhajar 'True Caller' da ke gano sunan mai lambar waya, a cewar EFCC.
Bayan ta buƙaci yi matan canjin dalar ne, sai suka tura wa mai canjin lambar asusun ajiyar da zai tura kuɗin kafin ta aika masa da dalar, kamar yadda hukumar ta bayyana.
EFCC ta ce da farko matar, ta karbi naira miliyan 89 daga wani mai suna Aminu Usman da nufin tura masa dala 53,300.
Daga baya kuma ta sake karɓar naira miliyan 108 da nufin canja mata dala 118 da ta ce za ta aika masa, kamar yadda EFCCn ta bayyana.