Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Mai ɗakin gwamnan Akwa Ibom Patience Umo Eno ta rasu

    Mai ɗakin gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno ta rasu.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ini Ememobong ya fitar, ranar Juma’a ya ce ta mutu ne ranar Alhamis.

    Sanarwar ta ƙara da cewa marigayiyar ta rasu ne a gaban iyalai da danginta.

    An haife ta ne a garin Ikot Akpa Ekop da ke yankin Ikpa Ibom, yankin ƙabilar Mkpat Enin da ta yi fice wajen noma kwakwan manja da sarrafa shi.

    Marigayiyar da gwamnan na Akwa Ibom sun yi shekara 37 suna tare a matsayin mata da miji kamar yadda jaridar The Nation ta bayyana, inda suka haifa yara shida da jikoki tara.

    Ita ce ta assasa gidauniyar Golden Initiative For Alla (GIFA) domin ayyukan jin ƙai da taimakon marasa galihu, inda ta yi amfani da gidauniyar wajen gina rijiyoyin burtsatse da tallafa wa mata masu shayarwa da wayar musu da kai da taimakon ilimin yara marasa galihu da ciyar da su da sauransu.

  2. Ba mu goyi bayan mayar da Lebanon "sabuwar Gaza" ba - Faransa

    Shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce ba za su goyi bayan mayar da Lebanon wata "sabuwar Gaza" ba, inda ya nanata kiransa na a tsagaita wuta a yaƙin na Isra'ila da Hezbollah.

    Macron ya ƙara da cewa ya yi amannar cewa Firaiministan Isra'ila zai yi kuskure babba idan ya ƙi amincewa da yarjejeniyar.

    Har yanzu dai Natanyahu bai ce komai ba, duk da ya nuna cewa za a iya cigaba da tattaunawar a daidai lokacin da su cigaba da luguden wuta a kan Hezbollah.

  3. Harin Isra'ila ya kashe mutum tara ƴan gida ɗaya a Lebanon

    A cigaba da luguden wuta da Isra'ila ke yi a ƙasar Lebanon, wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar, ya nuna cewa wani hari da Isra'ila ta kai a cikin dare ya kashe mutum tara ƴan gida ɗaya, ciki har da ƙananan yara huɗu.

    Reuters ta ruwaito Magajin Gari Mohammad Saaba yana tabbatar da lamarin, inda ya ce harin ya auku ne a garin Shebaa na kudancin Lebanon.

    A ɗaya gefen kuma, Hezbollah ta ce ta kai hare-hare guda biyu a yankunan Tiberias da Kiryat Ata.

  4. Assalamu alaikum

    Barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a daga nan BBC Hausa, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.