Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Abdullahi Bello da Isiyaku Muhammed

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi na ranar Juma'a.

    Sai kuma gobe Asabar za mu kawo wasu a wani shafin daban.

  2. Isra'ila ta umarci mazauna kudancin Lebanon su bar wasu gine-gine

    Rundunar sojan Isra'ila ta umarci mazauna kudancin Lebanon su fice daga wasu yankuna.

    Umarnin ya shafi wani gini a yankin al-Laylaki, da kuma wasu biyu a unguwar al-Hadath.

    "Kuna kusa da kadarorin Hezbollah, saboda tsira da ranku da 'yan'uwanku, dole ne ku bar gine-ginen nan take," a cewar kakakin rundunar Avichay Adraee cikin wani saƙo a shafukan zumunta.

    Ya ƙara da cewa mazauna kusa da wurin su yi nesa da su aƙalla mita 500.

  3. Trump ya gana da Zelensky a New York

    Donald Trump ya sake maimaita iƙirarinsa cewa yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine zai ƙare nan take idan aka sake zaɓarsa shugaban Amurka.

    Bayan ganawarsa da Shugaban Ukraine Zelensky a New York, Mista Trump ya ce yana da 'kyakkyawar alaƙa" da shugaban da kuma Putin na Rasha.

    A nasa ɓangaren, Zelensky ya ce yana fatan Amurka za ta ci gaba da mara wa ƙasarsa baya.

    Wani saƙo da Zelensky ya wallafa daga baya ya ce ganawar tasu ta yi armashi har ma sun yi bitar halin da ake ciki a Ukraine ɗin tare.

  4. Tinubu ya ba da umarnin yin ƙaramin bikin 'yancin kai saboda 'yanayi'

    A karo na biyu bayan hawansa mulki, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da ƙaramin bikin 'yancin kai "saboda halin da ƙasa ke ciki".

    A ranar Talata, 1 ga watan Oktoba Najeriya za ta cika shekara 64 da samun 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

    Da yake magana yayin wani taron manema labarai a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya ce gwamnatinsu na sane da halin matsi da 'yan ƙasa ke ciki.

    Ya ƙara da cewa matakin na da alaƙa da halin da Najeriya ke ciki, abin da ya sa Tinubu ya ba da umarnin.

  5. Harin Isra'ila a Beirut tsokana ce mai haɗari - Iran

    Iran ta ce mummunan harin da Isra'ila ta kai a Beirut a matsayin "mai haɗari kuma na tsokana".

    Wannan ne karon farko da Iran - uwargijiyar Hezbollah - ta yi magana kan harin da aka ce shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah aka kai wa.

    "Harin tsokana ce da za ta iya jawo wa miyagun hukuncin da ya dace da su," a cewar ofishin jakadancin Iran a Beirut, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

    Hezbollah na cikin ƙawancen da Iran ke kira "ƙawancen gwagwarmaya" a Gabas ta Tsakiya da ke rajin kare haƙƙin Falasɗinawa.

    Iran ce ke bai wa ƙungiyoyin kuɗi da makamai.

  6. Kalli munanan hare-haren Isra'ila a kan Lebanon

    Kalli yadda hayaƙi ke tashi sakamakon munanan hare-hare da Isra'ila ke kaiwa a birnin Beirut na Lebanon.

    Isra'ilar na cewa tana neman karya lagon Hezbollah ne, wadda ita ma harba mata makamai zuwa arewaci da kuma tsakiyar ƙasar.

  7. Isra'ila ta hari shugaban Hezbollah Nasarallah a Beirut, a cewar rahotonni

    Kafofin yaɗa labarai a Isra'ila na ba da rahoton cewa shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah aka hara da mummunan hari ta sama a kan birnin Beirut.

    Sai dai majiyoyin Hezbollah sun faɗa wa kamfanin labarai na AFP, da kafofi a Iran, cewa shugaban nasu na nan lafiya ƙalau bayan harin a yankin Dahiye.

    Zuwa yanzu Isra'ila ba ta tabbatar ko shi ta hara ba, sannan kuma Hezbollah ba ta fitar da wata sanarwa ba game da hakan.

    Tun da farko Isra'ila ta ce ta kai wa hedikwatar hari a Dahiye

  8. An yi wa Najeriya addu'ar cika shekara 64 da samun ƴanci a Babban Masallacin Abuja

    An yi wa Najeriya addu'o'i yayin da take cika shekara 64 da samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

    An yi addu'o'in ne bayan kammala Sallar Juma'a a babban Masallacin Juma'a na ƙasa a Abuja.

    Shugaba Bola Tinubu ya yi Sallar Juma'a a babban Masallacin tare da kakakin majalisar wakilai.

    Akwai tsohon shugaban ƙasa na mulkin Soja Janar Abdussalami Abubakar da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo cikin waɗanda aka yi addu'o'in da su.

  9. Rasha ta sake luguden wuta a Ukraine

    Hukumomi a yankin Odesa da ke kudu maso yammacin Ukraine sun ce mutane uku ne suka mutu a cikin dare a wani harin jirgin sama mara matuki da Rasha ta kai.

    Mutum 11 ne suka jikkata ciki har da karamin yaro daya. kuma Hukumar yankin ta ce yankin na fuskantar luguden wuta mai tsanani.

    A yankin Kherson da ke tsakiyar kasar, hukumomi sun ce hare-haren da Rasha ta kai kan wasu matsugunai ashirin da uku cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sun yi sanadin mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu goma sha tara.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, yana Amurka, inda Joe Biden da Kamala Harris suka sake jaddada masa cikakken goyon bayansu.

  10. Sojojin Sudan sun ce sun ƙwace iko da wasu sassan birnin ƙasar daga hannun RSF

    Rundunar sojin Sudan ta ce ta ƙwace wasu muhimman wurare a babban birnin ƙasar da kewaye, kwana guda bayan ta kai sabon farmaki kan dakarun RSF.

    Sojojin sun bayyana nasarar da suka samu Khartoum da kuma birnin Bahri inda suka yi amfani da atileri da hare-hare ta sama da kasa.

    A ranar Alhamis shugaban rundunar RSF Janar hamdan Dagalo ya shaidawa taron MDD cewar ya shirya don amincewa da tsagaita wuta.

    To amma janar Abdel Fattah al-Burhan ba zai yiwu a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba har sai RSF sun janye daga yankunan da suka mamaye tun farkon fara yakin basasar.

  11. Rodri na Man City zai yi jinya zuwa ƙarshen kakar bana

    Dan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri ba zai sake buga wasa a kakar wasanni ta bana ba.

    Rodri mai shekara 28 ya ji rauni ne bayan karon da ya yi da Thomas Partey, a wasan da ƙungiyarsa ta tashi 2-2 da Arsenal a ƙarshen mako.

    Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yanzu haka an yi wa ɗan wasan tiyata a gwiwarsa kuma ba zai sake buga wasa a wannan kaka ba.

    "An yi masa tiyata a yau da safe,''in ji Guardiola.

  12. Fiye da mutum 30,000 ne suka fice daga Lebanon zuwa Syria cikin kwana uku

    Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce fiye da mutum 30,000 ne suka tsallaka kan iyakar Lebonan zuwa Syria a cikin kwana uku, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Da yawa daga cikin wannan adadi, kusan kashi 80 'yan Syria ne, yayin da sauran suka kasance 'yan Lebanon.

    "Suna ficewa daga ƙasar da ke fama da yaƙi, zuwa ƙasar da ke fama da ricike-rikice na shekara 13,'' in ji wakilin UNHCR a Syria, Gonzalo Vargas Llosa, kamar yadda ya bayyana a wani taron manema labarai.

    Ita kanta Syria na fama da nata matsalolin 'yan gudun hijira tun fara rikice-rikicen ƙasar a 2011.

    Kusan Isra'ilawa 70,000 ne aka raba da muhallansu a arewacin ƙasar, tun bayan fara musayar hare-hare tsakanin Isra'ila da Hezbollah, da ya faru sakamakon yaƙin Gaza da aka kwashe kusan shekara guda ana gwabzawa.

    A Lebanon kuma, kusan mutum 90,000 ne aka raba da muhallansu tun ranar Litinin, ƙari a kan mutum 110,000 da suka fice daga gidajensu, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

  13. Amurka ta ƙara harajin motoci masu amfani da lantarki

    Amurka ta ƙaddamar da sabon tsarin harajin, da ya haɗa da ƙarin kashi ɗari a harajin motoci masu amfani da lantarki da ake shigowa da su ƙasar China.

    An sanar da sauye-sauyen ne a watan Mayu domin yaƙi da abin da Fadar White House ta kira rashin daidaito a harkokin cinikayya da China da kuma buƙatar kare wa ƴan Amurka guraben ayyukansu.

    Wannan ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da tsohon shugaban kasar Donald Trump ke nuna wa juna yatsa kan batun haraji yayin yaƙin neman zaɓe.

    Mista Trump yana kira da a ƙara haraji kan duk wasu kayayyakin da ake shigowa da su ƙasar, matakin da Ms Harris ta ce za ta haifar da hauhawar farashin kayayyaki.

  14. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 11 a jihar Neja

    Mummunar ambaliya ruwa ta yi sanadin mutuwar mutum 11 a jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya, tare da lalata garuruwa masu yawa faɗin ƙananan hukumomi 19 daga cikin 25 da ke jihar.

    Cikin wata sanarwa da daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba-Arah, ya fitar ya ce lamarin ya lalata gidaje fiye da 6,865, tare da gonaki 118,692, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

    Lamarin ya jefa fiye da mutum 41,000 cikin tsananin buƙatar tallafi.

    Baya ga lalata gonakin, ambaliyar ta kuma shafi makarantu 246, lamarin da ya shafi harkokin ilimi a garuruwa 529 na jihar.

    Ƙananan hukumomin da lamarin ya fi ƙamari sun haɗa da Mokwa da Katcha da Lavun da Lapai da Agaie da Shiroro da Munya da Gbako da Kontagora da Bosso da Edati da Agwara da Bida da Magama da Mashegu da Borgu da Gurara da Suleja da ƙaramar hukumar Rijau.

    Rahotonni sun ce ambaliyar ta kuma shafi gadoji 18 da kwalbatoci 80, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufuri a wasu yankunan jihar.

  15. Gwamnatin Najeriya ta nema ƙarin tallafin MDD kan ambaliyar Maiduguri

    Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya gana da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres a shalkwatarta da ke birnin New York na Amurka.

    Cikin wani saƙo da kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya wallafa a shafinsa na X, ya ce a lokacin ganawar an tattauna batutuwa da dama da suka shafi tsaro da ayyukan jin ƙai da tattalin arziki da sauransu.

    Shettima wanda yake wakiltar Shugaba Bola Tinubu a babban taron Majalisar Dinkin Duniyar karo na 79 ya kuma zanta da mataimakiyar Sakatare-Janar ta majalisar, Amina Mohammed.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci ƙarin tallafi domin magance matsalolin da sauyin yanayi suke janyowa, inda ya nanata buƙatar ƙarin tallafi ga mutanen da ambaliya ta illata a jihar Borno.

    A nasa ɓangaren, Mista Guterres ya jajanta wa Najeriya, sannan ya yi alƙawarin samar da ƙarin tallafin.

    Ya ce Majalisar Dinkin Duniya za ta cigaba da tallafa wa Najeriya, sannan ya jinjina wa shugaba Tinubu, inda ya ce Najeriya ƙawar arziki ce ga Majalisar.

  16. Matakan Tinubu suna gyara kura-kuran baya ne – Minista

    Gwamnatin Najeriya ta ce shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauki wasu matakai da tsare-tsare ne domin gyara wasu kura-kuran da aka tafka a baya domin dawo da tattalin arzikin Najeriya da ƙarfinsa.

    Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja a wata ganawa da ya yi da ƴan jarida domin bayyana yadda ƙasar za ta yi bikin cika shekara 64 da ƴancin kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    "A ƙarƙashin mulkin shugaba Tinubu, mun kawo wasu muhimman tsare-tsare domin gyara kura-kuran da aka yi a baya, tare da dawo da martabar Najeriya musamman a ɓangaren tattalin arziki."

    "Duk da matsalolin da aka samu da wahalhalun da ƴan ƙasar suka shiga a sanadiyar matakan, shugaban yana cigaba da ƙoƙarin inganta tattalin arzikin ƙasar da sanya ta a hanya mai ɗorewa da kowa zai ji daɗi."

    Ministan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka hana ƙasar cigaba shi ne hana ƙananan hukumomin ƙasar sakat, amma shugaban ƙasa Tinubu ya ba su ƴanci domin kai romin dimokuraɗiyya kowane lungu da saƙon ƙasar.

  17. Goguwa ta gigita arewacin Florida

    Wata guguwa mai ƙarfin gaske da aka yi wa laƙabi da Hurricane Helene, ta afka wa arewacin jihar Florida ta ƙasar Amurka inda ta taho da iskar da gudun ta ya kai kilomita ɗari biyu da ashirin da biyar.

    Tun da farko dai, Gwamnan jihar Ron De sanctis ya ce ta riga ta yi sanadiyar mutuwar mtum ɗaya, kuma ya gargaɗi mazauna jihar da su ɗauki matakan kiyaye kansu daga guguwar.

    Ya ƙara kira ga jama'a da su kula da irin bishiyoyin da ke kusa da su, saboda a cewarsa guguwa ce mai ƙarfin gaske kuma yayin da take ƙara kusantar jihar bishiyoyi da dama da za su riƙa faɗuwa.

    Ya kuma shawarci mazauna jihar su zauna cikin gidajensu har sai guguwar ta wuce.

  18. Trump zai gana da Zelensky a Amurka

    Shugaban Amurka Donald Trump ya amince ya gana da shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky duk da yawan sukarsa da yake yi a wajen kamfe.

    Ɗan takarar na shugaban ƙasa a jam'iyyar Republican, ya bayyana cewa Zelensky zai ziyarce shi a yau Juma'a a gidansa da ke Amurka.

    Ziyarar na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Trump ya kushe Zelensky da ƙin shiga sulhun zaman lafiya da Rasha.

    Shugaba Zelensky da Trump dai sun daɗe suna takun-saƙa, inda an taɓa yunƙurin tsige Trump daga mulki a 2019 a Amurka saboda zarginsa da tursasa Zelensky ya bankaɗo wasu bayanai da za su ɓata sunan Biden da ɗansa.

  19. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ƴanbindiga 792 cikin wata uku

    Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kashe ƴan bindiga kimanin 792 tsakanin watan Yuli zuwa Satumban da muke ciki.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran hedkwatar, Edward Buba ya fitar, ya ce dakarun tsaron ƙasar, ƙarƙashin rundunar Operation HADIN KAI ta samu nasarar kai hare-hare cikin dajin Sambisa da na Tumbuns a yankin tafkin Chadi, tare da kashe wasu manyan kwamandojin ƴanbindigar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa hare-haren da sojojin suka kai wa mayaƙan ya rage musu ƙarfi, tare da hana su ƙaddamar da manya-manyan hare-hare.

    Edwar Buba ya ci gaba da cewa a lokacin ayyukan soji a waɗanann yankuna tsakanin waɗannan watanni, dakarun ƙasar sun samu nasarar kashe wasu manyan kwamandojin ƴanbingida da suka haɗa da Munzir Arika da Sani Dilla (Ɗan Hausawan Jubillaram) da Ameer Modu da Ɗan Fulani Fari Fari Dungusu da Abu Darda da Bakoura Arina Chiki da Dungusu da Abu Darda da kuma Abu Rijab.

    Haka kuma sanarwar ta ce an kama wasu da ake zargi da kasancewa ƴanbidigar kimanin 606 tsakanin waɗannan watanni tare da kuɓutar da mutum 476 da ake garkuwa da su, sannan kuma wasu iyalan ƴanbindigar kimanin 7,283 suka miƙa wuya.

    Sanarwar ta kuma ce dakarun sojin sun ƙwato makamai da suka haɗa da bindiga ƙirar AK47 guda 339, da ƙirar gida 58 da ƙananan bindigogi 83 da kuma tarin alburusai.

  20. Sama da rabin mutanen Argentina na fama da talauci - Rahoto

    Wani rahoto da Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar Argentina ta fitar ya nuna cewa sama da rabin al'ummar ƙasar na fama da talauci.

    Hakan dai na nuna ƙaruwar lamarin daga kashi arba'in cikin ɗari a rubu'i na biyu na shekarar da ta gabata kuma ya nuna tasirin matakan tsuke bakin aljihu da shugaba Javier Millei ya ɓullo da su.

    Tun bayan hawansa karagar mulki a watan Disamba, gwamnati ta rage tallafin da ta ke bayarwa kan sufuri da man fetur da makamashi tare da korar dubban ma'aikatan gwamnati, a ƙoƙarinta na daƙile hauhawar farashin kayayyaki.

    Hauhawar farashin kayayyaki a Argentina a cikin watan Agusta ya kasance ɗaya daga cikin mafi girma a duniya inda ya kai matakin sama da kashi ɗari biyu da talatin.