Ghana ta amince ta karɓi ƴan Afirika ta yamma da za a kora daga Amurka

Asalin hoton, Getty Images
Ghana ta zama kasa ta baya-bayan nan da ta karbi mutanen da aka kora daga Amurka a wani bangare na yaki da kwararar baƙin haure da ba su da takardun izini.
Shugaba John Dramani Mahama, ya ce a yanzu ana iya karbar 'yan kasar daga kasashen yammacin Afirka daban-daban, inda ya ce goma sha hudu sun riga sun iso.
A watan da ya gabata ne Amurka ta kori bakin haure bakwai zuwa Rwanda. A watan Yuli, an aika biyar zuwa Eswatini, wasu takwas kuma zuwa Sudan ta Kudu.


