Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/09/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/09/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Badamasi Mukhtar

  1. Ghana ta amince ta karɓi ƴan Afirika ta yamma da za a kora daga Amurka

    Ghana ta zama kasa ta baya-bayan nan da ta karbi mutanen da aka kora daga Amurka a wani bangare na yaki da kwararar baƙin haure da ba su da takardun izini.

    Shugaba John Dramani Mahama, ya ce a yanzu ana iya karbar 'yan kasar daga kasashen yammacin Afirka daban-daban, inda ya ce goma sha hudu sun riga sun iso.

    A watan da ya gabata ne Amurka ta kori bakin haure bakwai zuwa Rwanda. A watan Yuli, an aika biyar zuwa Eswatini, wasu takwas kuma zuwa Sudan ta Kudu.

  2. Koriya ta Kudu ta yi gargadin tasirin tsare ƴan ƙasarta a Amurka kan zuba jari

    Koriya ta Kudu ta yi gargadin cewa tsare ɗaruruwan 'yan kasarta a jihar Jojiya ta Amurka ka iya yin wani babban tasiri ga zuba jari a ƙasar nan gaba.

    A wani taron manema labarai a birnin Seoul shugaban ƙasar Lee Jae Myung ya ce kamen bakin haure yan kasarsa a makon da ya gabata a wata masana'antar (Handai) Hyundai da L-G ya yi matukar kidima su.

    Ya ce hakan na iya sa wa yan kasuwar Koriya ta Kudu su yi shakkar zuba jari a Amurka.

    An aika da jirgin sama zuwa Atlanta don maido da ma'aikatan.

  3. Qatar ta yi wa Netanyahu kakkausan martani kan kai sabbin hare-hare

    Qatar ta mayar da martani cikin fushi ga kalaman firaministan Isra'ila na cewa ƙasarsa na iya kai wasu sabbin hare-hare ƙasar idan har bata kori shugabannin Hamas da ke zaune a cikin ta ba.

    Benjamin Netanyahu ya yi gargadin cewa dole ne Qatar da sauran ƙasashen da ke ba da mafaka ga mutanen da ya bayyana a matsayin 'yan ta'adda' su hukunta su, ko kuma Isra'ilan ta yi hakan da kanta.

    Ma'aikatar harkokin wajen Qatar ta bayyana kalaman na shi a matsayin na rashin sanin ya kamata.

    Ta ce Isra'ila tana da cikakkiyar masaniyar cewa Qatar na karbar bakuncin jami'an Hamas din ne a wani yunkuri na tattauna batun zaman lafiya, kuma da sanin Amurka.

  4. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Alhamis.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.