Rufewa
Masu bin shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran namu.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/09/2025.
Daga Usman Minjibir, Aisha Babangida da Badamasi Mukhtar
Masu bin shafinmu na BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labaran namu.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da suka shafi auren jinsi da dangoginsa.
Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar ranar Laraba.
Cikin ƙunshin ƙudurorin da majalisar zartaswar ta aike wa majalisar dokokin - wanda kwamishinan ƙasa da safiyo, Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da dokar da za ta haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar.
Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari'ar addinin musulunci - wadda a dokokinta suka haramta auren jinsi, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga wanda ya aikata.
Babbar kotun Afirka ta Kudu ta ce daga yanzu maza za su iya amfani da sunayen iyayen matansu a hukumance.
Sabon matakin ya soke dokar da a baya ta hana su yin hakan.
Wasu ma'aurata ne suka shigar da ƙara a gaban kotun inda suka buƙaci a soke dokar da suka bayyana da cewa tun ta lokacin mulkin mallaka ce, wadda ta ke nuna wariya tsakanin jinsi.
A yanzu majalisar dokokin ƙasar za ta gyara ƙundin dokokin ƙasar domin gyara dokokin rajistar haihuwa da na mutuwa, domin sama wa sabuwar dokar gurbi.
Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta amince da sabbin jam'iyyun siyasa 14 a ƙasar, da za su shiga harkokin zaɓukan ƙasar.
Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta ce ƙungiyoyi 171 ne suka gabatar mata da buƙatunsu na yi musu rajista domin zama jam'iyyu a ƙasar.
INEC ta ce bayan nazari tare da ɗora buƙatun ƙungiyoyin a ma'aunin sashe na 222 na kundin tsarin mulkin ƙasar da sashe na 79 (1,2 da 4) na dokar zaɓe ta 2022 kan ƙa'idar zama jam'iyya.
''Daga ƙarshe ƙungiyoyi 14 ne suka cika ƙa'idar hukumar zaɓen, yayin da sauran ƙungiyoyi 157 suka gaza cika ƙa'idar'', in ji hukumar ta INEC.
Sabbin jam'iyyun da hukumar ta amince da su sun haɗa da:
Gwamnatin Najeriya ta bi sahun wasu takwarorinta na duniya wajen yin Allah wadai da harin da Isra'ila ta kai Qatar a ranar Talata.
Cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar, ta yi kira ga duka ƙasashen biyu su kai zuciya nesa.
Gwamnatin Najeriyar ta ce ta yi matuƙar damuwa da hare-haren da Isra'ilar ta kai wa jagororin Hamas a birnin Doha.
Sanarwar ta ce Najeriya na kan doron martaba ƴanci da alfarmar kowace ƙasa, ƙarƙashin tsarin dokokin duniya, musamman a abin da ya shafi amfani da ƙarfin soji a kan wata ƙasa.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce babu abin da harin zai haifar illa ƙara dagula lamurra a yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kawo tarnaƙi ga yarjejeniyar diplomasiyya da ake ƙoƙarin amfani da ita wajen kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
Gwamnatin Najeriya ta kuma yaba wa Qatar kan ƙoƙarin da ta ce ta jima tana yi wajen ganin ta zama mai ƙoƙarin wanzar da sulhu a yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka kuma sanarwar ta buƙaci ƙasashen Isra'ila da Qatar su kai zuciya nesa domin guje wa dagulewar lamurra a yankin.
Daga ƙarshe gwamnatin Najeriya ta jajanta wa iyalan waɗanda harin ya rutsa da su tare da jaddada ƙudurin gwamnatin ƙasar na goyon bayan hanyar sasanci da tattaunawa don kawo ingantaccen zaman lafiya a yankin.
Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya na jam;iyyar LP ya gana da tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Cikin wani saƙo da Peter Obi ya wallafa a shafinsa na X ya ce ganawar tasu ta sirri ce da suka tattauna abubuwan da suka shafi Najeriya.
Ganawar jagororin siyasar na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar ƙasar ke ƙara ɗaukar, musamman yadda wasu ƴansiyasar na ɓangaren hamayya ke ƙoƙarin ƙulla ƙawance da nufin kawar da gwamnatin Tinubu ta APC.
A baya-bayan nan an yi da kiraye-kirayen Jonathan da Peter Obi su fito takatar shugaba ƙasa da mataimaki a jam'iyyar PDP, wani abu da masana siyasa ke ganin zai kawo wa Tinubu gagarumar barazana a 2027.
Jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI da ke binciken batun kisan da aka yi wa wani fitaccen mai amfani da shafukan sada zumunta a ƙasar, Charlie Kirk, sun fitar da hotunan mutumin da suke ƙoƙarin kamawa kan harin.
Hotunan sun nuna mutumin sanye da baƙin gilashi.
Danbindigar da ya harbe Kirk a taron Jami'ar Uta ranar Labara ya tsare bayan harbin.
Jami'an da ke faratuat ɗanbindigar sun ce sun gano wata bindiga a kuda da wurin da aka yi harbin.
Tuni dai hukumar FBI ya sanar da ladan dala 100,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama duk wanda ke da hannu a harin.
Shugaba Trump ya ce zai karrama Charlie Kirk da lambar girmamawa ta ƴanci, wadda ita ce lambar yabo mafi martaba da ake bai wa fararen hula a Amurka.
A wani biki da aka gudanar a maƙabartar Arlington domin tunawa da harin 11 ga watan Satumba, Trump ya bayyana Kirk wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa a wannan zamani.
''Ya kasance mai fafutikar ganin mutane sun sami ƴanci kuma abin koyi ne ga miliyoyin mutane'', in ji Trump.
A ranar Laraba ne wani mutum ya buɗe wa Charlie Kirk wuta lokacin da yake tsaka da jawabi a wajen wani taro a Uta.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya buƙaci ƙungiyar Taliban ta ɗage dokar hana mata zuwa wuraren aikin gwamnati.
UNAMA ta ce Taliban na hana ma'aikata mata da masu kwangila shiga harabar Majalisar Dinkin Duniya a Kabul, da wasu muhimman ofisoshi a ƙasar.
Majalisar Dinkin duniyar ta ce hakan na jefa ayyukan jin ƙai cikin mummunan haɗari.
Majiyar Taliban ta ce zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar ba ta fara amfani da dokar yadda ya kamata ba.
An gurfanar da mataimakin shugaban Sudan a Kudu, Riek Machar kan zargin cin amanar ƙasa da kisan kai da kuma keta hakkin ɗan Adam.
Hukumomi sun kuma zargi mataimakin shugaban ƙasar da tallafawa ƙungiyoyin ƴan tawaye a harin da suka kai wa dakarun gwamnati a cikin watan Maris.
Mr Machar ya shafe makonni ana tsare da shi bayan harin, daga baya kuma aka yi masa ɗaurin talala yayin da alaƙa ke ci gaba da tsami tsakaninsa da shugaban Salva Kiir.
Mutanen biyu sun jagoranci ɓangarorin da ke jayayya da juna a yaƙin basasar Sudan ta Kudu, wanda aka kawo ƙarshe bayan ƙulla yarjejeniyar kafa gwamnatin haɗin gwiwa a 2018.
Hukumar bunƙasa bincike kan sinadaran da ake samu daga tsirrai ta Najeriya (NBRDA) ta ce ta ƙulla yarjejeniya da wani kamfanin China domin samar da sinadarin Insulin.
Yarjejeniyar ta hukumar NBRDA da kamfanin Shanghai Haiqi za ta kawo ƙarshen dogaron da Najeriya ke y ikan shigar da sinadarin Insulin cikin ƙasar daga waje, domin wadata sinadarin ga miliyoyin ƴan ƙasar masu fama da ciwon suga.
Ministan fasaha da kimiyya na Najeriya Chief Uche Nnaji yarjejeniyar wani mataki ne na cimma Muradin gwamnatin Najeriya na inganta fasaha da ƙere-ƙere da kiwon lafiyar jama’a da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce “tsawon shekaru masu fama da ciwon suga a Najeriya sun dogara ga ƙasashen waje domin samun Insulin mai muhimmanci ga kiwon lafiyar su. Amma da wannan yarjejeniya, Najeriya ta kama hanyar shiga jerin ƙasashe da suka bayar da fifiko ga iwon lafiyar masu ciwon suga da kuma amani da tsarin wajen samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati’’.
Wannan ne karon farko da Najeriya ta samar da kamanin da zai sarrafa sinadarin Insulin domin amfanin al’ummar ƙasar.
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta ce ta gano wata bindiga da jam'ian hukumar ke kyautata zaton da ita aka harbi fitaccen ɗan fafutukar nan mai ra'ayin riƙau, Charlie Kirk.
A yayin da suke jawabi ga manema labarai a Utah, jami'an sun ce sun sami bidiyon wanda ake zargin, wanda har yanzu a ke nema ruwa a jallo, kuma a cewar su, matashi ne.
Sun kuma ce sun samo shatin tafin ƙafarsa da wasu shaidun da su ke nazari a kai.
Charlie Kirk na jawabi ne a jami'ar Utah a jiya Laraba, a lokacin da wani harsashi da aka harbo ya same shi a wuya.
Ana sa ran mataimakin shugaban Amurka JD Vance zai ziyarci iyalan Kirk a Utah nan gaba a ranar Alhamis.
Zuwa yanzu ba a san ko wane ne maharin ba ko kuma dalilinsa na kai harin, sai dai Mista Trump ya ɗaura alhakin harin da ma wasu tashe tashen hankulan siyasa na baya bayan nan kan abin da ya kira masu tsatsauran ra'ayin siyasa, kuma ya sha alwashin kawo ƙarshen hakan.
Sai dai kuma bai ambaci hare hare da aka kai kan ƴan Democrat ba, kamar kisan wani ɗan majalisar dokoki a jihar Minnesota a farkon shekarar nan.
Wata babba kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta yanke wa Mahmud Usman, ɗaya daga cikin kwamandojin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin shekaru 15 a gidan yari.
Mutumin wanda hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar a ranar Alhamis ya amsa laifin gudanar da harkokin haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, lamarin da ya ba shi damar mallakar makamai da aikata ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane.
Alƙalin kotun mai shari'a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin a ajiye Mahmud Usman a ofishin hukumar DSS har zuwa lokacin da za a kammal shari'a kan sauran zarge-zargen da ake masa guda 31.
A lokacin gabatar da ƙarar, an tuhumi Mahmud Usman da Abubakar Abba da aikata ta'addanci a 2022, ta hanyar kai hari kan barikin soji ta Wawa da ke Ka'inji a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar Niger, lamain da ya yi sanadiyar kisan mutane da dama.
Ana zargin su da koyon horo a kan sarrafa makamai da haɗa bama-bamai a sansanonin ƴan ta'ada da dama.
Mai shari'a Nwite ya sanya ranar 21 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a ci gaba da shari'ar.
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya ta bai wa gwamnatin ƙasar sabon wa'adin kwana ɗaya ta biya buƙatunta, bayan ƙarewar na kwana 10 da ta bayar a baya, wanda ya ƙare a ranar 10 ga watan Satumba.
Shugabannin ƙungiyar sun ɗauki wannan matkin ne a ƙarshe taron da suka yi a ranar Laraba.
Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a gagauta aiwatar da matakan da aka yi masu alƙawari.
A wata sanarwar da ƙungiyar ta bitar a ranar 1 ga watan Saumban bana, ta nemi a gaggauta biyan ƴaƴanta bashin ƙarin albashinsu na wata buyar da suke bi, bayan aiwatar da ƙarin kashi 25 zuwa 35 na tsarin albashin ma'aikatan lafiya.
Lkitocin sun kuma abatar da wasu buƙatun da suka haɗa da gagauta biyan su bashin alawus-alawus ɗinsu da kuma sauran buƙatu.
Likitoci masu neman ƙwarewar aiki a Najeriya su ne ƙashin bayan aikin kiwon lafiya a ƙasar, inda suke gudanar da ayyuka asibitoci mallakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.
Duk lokacin da suka shiga yajin aiki ana samun koma baya wajen kiwon laiyar al'umma, lamarin da ke jefa rayuwar marasa lafiya ciki halin rashin tabbas.
Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da manyan shugabannin ƙungiyar Ansaru, wata kungiyar tsageru kuma gawurtattun ƴanbindiga mai alaƙa da Al-Qaeda, a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis.
Shugabannin ƙungiyar Ansarun biyu sun hada da Mahmud Muhammed Usman, wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas Mukhtar, da mataimakinsa, Abubakar Abba, wanda aka fi sani da Isah Adam/Mahmud Al-Nigeri.
Ana zargin su da aikata laifuka manyan 32 masu alaƙa da ta'adanaci.
Hukumomin Najeriya na zarginsu da taimakawa da kuma haɗa kai wajen aikata laifukan ta'addanci, tsakanin shekarun 2013 zuwa 2015 da kuma kitsa harin gidan yarin Kuje da aka yi a shekarar 2022 da hari a wajen haƙar ma'adinin uranium na Nijar da garkuwa da wani Bafaranshe mai suna Francis Collomp a Katsina da sace Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba a shekarar 2019 da sace Sarkin Wawa.
Haka kuma suna da alaƙa da ƴanbindiga a yankin Maghreb, musamman Mali da Nijar da Burkina Faso kamar yadda mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya bayyana a wata sanarwar da ya fitar kwanakin baya.
A ranar Larabar 10 ga watan Satumbar 2025 ne babban layin wutar lantarkin Najeriya sake lalacewa a karo na farko a shekarar.
Duk da cewa babu cikakkun alƙaluma dangane da yawan lokacin da babban layin wutar lantarkin na Najeriya ya lalace, bayanai sun nuna cewa ya lalace sau fiye da 100 a tsawon shekaru 10 sannan sau 12 a shekarar 2024.
Bayanin da kamfanin wutar lantarki na Abuja, AEDC ya wallafa a shafinsa na X ya nuna cewa wutar ta faɗi daga megawatts kusan 3000 a ƙasar zuwa megawatts 1.5 a ranar Larabar.
Shin mene ne wannan babban layin wutar lantarki, kuma me ya sa yake yawan lalacewa?