Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 07/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mika'il, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Hotunan ɓarnar da harin Rasha a Kyiv ya haddasa

    Rayuwa a birnin Kyiv ta fara dawowa a hankali a yau Laraba bayan wani mummunan harin gurneti da jiragen yaƙi marasa matuki daga Rasha da ya faru da daddare.

    Harin ya haddasa ɓarna mai yawa tare da hallaka wata uwa da ɗanta a cikin wani ginin haya.

    Ga wasu hotuna daga babban birnin Ukraine da ke nuna yadda mazauna ke bin ta cikin ƙura da tarkace, suna duba barnar da aka yi wa gidaje da gine-ginen gwamnati yayin da jami’an ceto ke ci gaba da aiki a wurin.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  2. 'Yanmajalisar Najeriya sun nuna damuwa kan yadda Boko Haram ke amfani da jirage marasa matuƙa

    ...

    Asalin hoton, Boko Haram

    ’Yanmajalisar tarayya a Najeriya sun bayyana cewa ’yan ƙungiyar Boko Haram mai iƙirarin jihadi na amfani da jiragen yaƙi marasa matuka wajen kai hare-hare, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

    Wani danmajalisa daga kudu maso gabashin Borno - inda hare-haren Boko Haram suka fi ƙamari - ya ce 'yanbindigar sun fi sojojin Najeriya makamai".

    “Ina cikin waɗanda suka gani da idonsu. Ba labari aka ba ni ba. Wannan zai shiga tarihi. Boko Haram na amfani da jiragen yaki marasa matuka, wadanda sojojin Najeriya ba su amfani da su.

    "Ma’ana, suna da kayan aiki fiye da rundunar sojin Najeriya,” in ji Ahmed Jaha, dan majalisar wakilai daga mazabar Chibok.

    Zainab Gimba, wakiliyar mazaɓar Bama, ita ma ta tabbatar da cewa mayaƙan na amfani da jiragen yaki marasa matuka, tana mai zargin akwai hannun ƙasashen waje.

    “Kwamandan ya shaida min cewa daga cikin ’yanta’addan akwai fararen fata da dama; akwai sa hannun wasu daga kasashen waje,” in ji ta.

    An samu ƙarin hare-hare da ake ɗora wa Boko Haram da Iswap alhakin kai su kan jami’an tsaro a jihohin Borno da Yobe a ’yan kwanakin nan.

  3. Sudan ta yanke dangantaka da UAE kan zargin tallafawa RSF

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Sudan ta yanke dangantakar diflomasiyya da ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), bayan zargin da ta maimaita na cewa ƙasar na tallafawa dakarun RSF da ke fafatawa da gwamnati a yaƙin basasar da ke gudana.

    Sanarwar yanke dangantakar ta zo ne bayan da aka zargi RSF da kai hari a birnin Port Sudan tun daga ranar Lahadi, har zuwa ranar Laraba.

    A ranar Talata, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim, ya zargi UAE da take hurumin ƙasarsa ta hanyar tallafawa RSF.

    UAE dai ta musanta zargin da ake mata na bayar da goyon bayan ga dakarun RSF.

    Yaƙin da aka shafe shekaru biyu ana yi ya hallaka dubban mutane, ya kuma tilasta wa miliyoyi barin muhallansu, tare da haifar da mafi muni na rikicin jinƙai a duniya.

    Sakamakon sanarwar ministan tsaro, Sudan za ta janye jakadanta daga UAE ɗin tare da rufe dukkan ofisoshin diflomasiyyarta a ƙasar.

  4. An kama mutum uku a Abuja kan cinikin dabbobin daji ba bisa ƙa’ida ba

    .

    Asalin hoton, NESREA

    Bayanan hoto, .

    Hukumomi a Najeriya sun kama mutum uku bisa zargin safarar namun daji da cinikinsu ba bisa ƙa'ida ba.

    Hukumar da ke sa ido kan ayyuakn da suka shafi kare muhalli ta (NESREA) tare da hukumar kula da gidajen ajiyar dabbobin daji ta ƙasa ne suka yi kamen ranar Talata a Abuja a wani samamen haɗin gwiwa.

    Wata sanarwa daga jami’ar hulda da jama’a ta NESREA, Nwamaka Ejiofor, ta ce an kama waɗanda ake zargi a sassa daban-daban na birnin saboda sayar da tsuntsaye da dabbobin daji da aka haramta, wanda ya saɓa dokar kare dabbobin da ke fuskantar barazaar ƙarewa.

    Shugaban NESREA, Farfesa Innocent Barikor, ya tunatar da 'yan Najeriya cewa safarar dabbobin da ke fuskantar barazanar ƙarewa laifi ne a karkashin dokar ƙasar, yana mai gargaɗin cewa za a gurfanar da duk wanda aka kama da irin wannan laifi a gaban kotu.

  5. Hotunan yadda ake taron adu'o'i a cocin Katolika kafin fara zaɓen sabon Fafaroma

    A yayin da aka killace manya-manyan limaman ɗariƙar Katolika a zauren ibada na Sistine ranar laraba don zaɓo mutumin da zai gaji Fafaroma Francis, ga wasu hotuna da ke nuna yadda ake taro a cocin Kotolika ɗin yayin zaɓen.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  6. Gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin haɗaka - Atiku

    ...

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/X

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa a najeriya kuma jagoran adawa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta firgita da yunƙurin da suke yi ƙulla haɗakar jam'iyyun adawa.

    Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga kalaman Daniel Bwala, tsohon hadiminsa kuma mai bai wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin sadarwa, inda ya shawarci Atiku da ya haƙura da takara a zaɓen 2027.

    Cikin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Bwala ya ce: "Ya kamata Atiku ya yarda da ƙaddara, wataƙila ba nufin Allah ba ne ya shugabanci Najeriya."

    A martanin da ya fito daga ofishin yada labaran Atiku, an siffanta kalaman Bwala da “raini da kuma rashin mutunci”.

    "Ceto da gina Najeriya aikin ne mai matuƙar muhimmanci na ƙasa — wanda bai kamata a bar shi yana tangal-tangal ba saboda son zuciyar wasu hadiman fadar shugaban ƙasa masu neman faranta wa kansu rai,” in ji sanarwar.

  7. Majalisar dattawa za ta shirya taron ƙasa kan matsalolin tsaro a Najeriya

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kafa kwamitin wucin gadi domin shirya taron ƙasa na kwana biyu kan matsalolin tsaro a birnin Abuja.

    Taron na da nufin magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar ta hanyar haɗa kai da duk hukumomin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi – tare da sarakunan gargajiya da kuma sauran masu ruwa da tsaki a fannin tsaro.

    Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya amince da kudirin kuma ya umurci kwamatin wucin gadin da ya fara shirye-shiryen taron nan take.

    "Dole ne a tsara taron ta yadda zai samar da matakan aiwatarwa, ba wai kawai yin taro na nuna bajinta ba," in ji shi.

    Ana sa ran taron zai samar da mafita mai amfani da haɗin kai ga matsalolin da ke barazana ga zaman lafiyar kasa.

    A zaman majalisa da aka gudanar a ranar Talata, ‘yan majalisa sun tattauna tasirin sake shirya irin wannan taro, inda suka nuna cewa tarukan baya ba su haifar da gamsasshen sakamako ba.

  8. Mutanen da suka mutu a India da Pakistan na ƙaruwa bayan hare-hare

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawan mutanen da suka mutu a hare-haren indiya da Pakistan na ƙaruwa, inda aka ruwaito cewa aƙalla mutum 26 sun mutu, 46 kuma sun jikkata a Pakistan bayan hare-haren sojojin Indiya.

    A ɓangaren Indiya kuma, mutum 10 ne suka mutu yayin da 32 suka samu raunuka a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi sakamakon harin ramuwar gayya daga Pakistan.

    Sojojin Indiya ne dai suka fara ƙaddamar da wani hari mai suna “Operation Sindoor” inda suka hari wurare tara da ke cikin Pakistan da kuma yankin Kashmir da Pakistan ke iko da shi.

    Wannan harin ya haifar da martani cikin gaggawa daga Pakistan, wanda ya janyo rikicin da ya fi kowanne tsanani cikin fiye da shekaru ashirin da suka gabata tsakanin ƙasashen biyu masu makaman nukiliya.

    Shugabannin ƙasashen biyu na gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba domin tattaunawa kan rikicin.

    Harin da Indiya ta kai da kuma ramuwar gayya daga Pakistan na faruwa ne a daidai lokacin da ake fama da matsanancin tashin hankali, bayan wani hari da aka kai a watan da ya gabata kan masu yawon buɗe ido a yankin Kashmir da Indiya ke iko da shi – wanda New Delhi ta ɗora alhakin hakan a kan Islamabad, sai dai Pakistan ta musanta wani hannu a cikin harin.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar Laraba, gwamnatin Indiya ta ce dakarunta sun kai harin ne kan “wuraren 'yan ta’adda da ke cikin Pakistan da kuma yankin Jammu da Kashmir da Pakistan ke iko da shi, inda ake shiryaw da kuma kaddamar da hare-hare a kan Indiya.”

  9. Assalamu alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Laraba.

    Sannunmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Aisha Babangida ce ke tare da ku a wannan safiya bisa kulawar Umar Mika'il