Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 07/05/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mika'il, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumi, PSG ta doke Arsenal, ta kai wasan karshe na Champions League

    UCL

    Asalin hoton, Reuters

    Paris St-Germain ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai, bayan doke Arsenal a wasa mai zafi da suka fafata a Paris.

    PSG ta tsallake ne da jimillar kwallaye 3-1, bayan doke Arsenal 2-1 a Paris da kuma ci 1-0 a Emirates.

    Karo na biyu kenan da PSG ta kai zagayen ƙarshe a gasar Zakarun Turai tun 2020 da Bayern Munich ta doke ta kuma ta lashe kofin gasar.

    Fabian Ruiz da Achraf Hakimi ne suka fara ci wa PSG ƙwallo a ragar Arsenal, yayin da Bukayo Saka ya farke wa Arsenal kwallo ɗaya a wasan.

    PSG wadda ba ta taɓa lashe kofin ba a tarihinta, za ta fafata da Inter Milan wadda ta fitar da Barcelona.

    Za a ɓarje gumi a wasan karshe ne ranar Asabar 31 ga watan Mayu, a filin wasa na Allianz Arena da ke Jamus.

  3. Pakistan ta ce harin roka da Indiya ta kai mata tsokanar yaƙi ne

    Rikicin Pakistan da Indiya

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Pakistan ta ce harin roka da Indiya ta kai mata a tsakar dare tsokanar yaƙi ne.

    Rundunar sojin Pakistan ta ce yawan fararen hula da harin ya kashe ya ƙaru zuwa 31.

    Wakiliyar BBC ta ce girman martanin da Pakistan za ta mayar ne zai tantance ko rikicin zai ƙara rincaɓewa, ko kuma akasin haka.

    Har yanzu Indiya ba ta ce komai ba a kan harin, amma an samu rahoton harbo wasu jirage aƙalla uku a yankin Kashmir da take iko da shi.

  4. Saka ya farke wa Arsenal kwallo ɗaya

    UCL

    Asalin hoton, Reuters

    Bukayo Saka ya farke wa Arsenal kwallo ɗaya.

    Ƙungiyar dai tana ci gaba da kai wa PSG hare-hare a halin yanzu... suna ji har yanzu suna da dama.

    Da alama kwallon zai ƙara wa Arsenal ƙwarin gwiwa.

  5. Hakimi ya ci wa PSG kwallo ta biyu

    UCL

    Asalin hoton, Reuters

    Ɗan wasan PSG Achraf Hakimi ya ci wa ƙungiyarsa kwallo ta biyu.

    Hakimi ya ci kwallo mai kyau a cikin yadi na 18 a gaban ƴan wasan Arsenal.

    Magoya bayan PSG sun ɓarke da sowa a filin wasa na Parc des Princes.

    Yanzu dai sun fara ji a ransu cewa za su iya kai wasan karshe.

  6. PSG ta samu bugun fenariti ta ɓarar da shi

    UCL

    Asalin hoton, Reuters

    PSG ta ɓarar da bugun fanariti da ta samu a wasan da suke fafatawa da Arsenal.

    Vitinha ne ya buga kwallon, inda Davida Raya bai yi wata-wata ba ya kaɗe ta.

    Shin Arsenal tana da sauran dama har yanzu?

  7. Majalisar dattijai ta amince da kudurorin dokar haraji biyu

    Akpabio

    Asalin hoton, Nigerian Senate

    Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kudurori biyu daga cikin huɗu na dokar haraji da aka gabatar mata.

    Kudurorin sun haɗa da na dokar da ta shafi sauya tsarin hukumar tara haraji ta ƙasa da kuma samar da wata hukumar da za ta shafi tattara haraji na hadin gwiwa tsakanin sassa daban-daban.

    Shugaban majalisar dattawan, Sanata Godswill Akpabio, ya yi farin ciki da amincewa da kudurorin biyu - inda ya ce za su inganta harkar shugabanci da kuma zamanantar da yadda ake karɓar haraji da kuma raba shi a faɗin ƙasar.

    "Waɗannan kudurori za su ƙara inganta harkar gudanar da gwamnati da kuma sauye-sauye kan yadda ake karɓar haraji," in ji shi.

    Ya ƙara tabbatar da cewa za a kammala amincewa da sauran kudurorin biyu a gobe Alhamis.

    Wannan doka ta haraji dai ta sha suka daga ƴan Najeriya musamman ma shiyar arewacin ƙasar, inda ake kallon cewa tsarin tattara harajin zai mayar da yankin saniyar ware.

    A watan Oktoban 2024 ne, shugaba Bola Tinubu ya aika wa majalisar kudurorin dokar haraji huɗu domin yin zama da kuma amincewa da shi.

  8. An tafi hutun rabin lokaci PSG na cin Arsenal 1-0

    UCL

    Asalin hoton, EPA

    Yanzu an tafi hutun rabin lokaci a wasan da PSG ke fafatawa da Arsenal a matakin daf da karshe na gasar Zakarun Turai.

    Duk da cewa Arsenal ta fi PSG taka kwallo a minti 45 na farko, amma PSG ce ta samu damar cin kwallo.

    PSG na gaban Gunners da kwallo biyu zuwa yanzu - bayan cin kwallo ɗaya a fasan farko a Emirates.

    Arsenal na da jan aiki a gabanta idan tana son farfaɗowa ta kuma kai wasan karshe.

    Ko ya za ta kaya idan aka dawo daga hutun rabin lokaci?

  9. 'Hare-haren Isra'ila a gidan abinci na Birnin Gaza da kasuwa sun kashe mutum 20'

    Scene of a bombing

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Aƙalla Falasɗinawa 20 aka kashe a harin da Isra'ila ta kai wani gidan cin abinci da kasuwa a birnin Gaza.

    Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gawawwaki suka faɗi kan tebura a gidan cin abinci, da ke arewacin garin Rimal.

    Hotuna daga kasuwar mai nisan kilomita 60, sun nuna wani gawar wani jariri yashe a ƙasa a kan titi.

    Sojojin Isra'ila sun ce suna duba rahotannin.

    Tun da farko, jami'an asibitoci sun ce aƙalla mutum 59 aka kashe a wasu hare-hare ranar Talata da daddare, yawancinsu kan makarantu biyu da ke zama a matsayin wuraren matsuguni ga iyalan da aka ɗaiɗaita.

  10. PSG ta zura wa Arsenal kwallo ɗaya a raga

    PSG VS Arsenal

    Asalin hoton, Reuters

    Paris St Germain ta zura wa Arsenal kwallo ɗaya a wasan zagaye na biyu na daf da karshe na gasar Zakarun Turai da suke fafatawa.

    Ɗan wasan PSG Fabián Ruiz ne ya ci kwallon a minti na 27.

    Yanzu dai Arsenal na buƙatar cin aƙalla kwallo biyu idan tana son dawowa cikin wasan.

  11. Babu wanda ya yi nasara a zaɓen sabon Fafaroma da ake yi zuwa yanzu

    Zaben sabon Fafaroma

    An ga baƙin hayaki na fita daga cocin Sistine, abin da ke nufin cewa ba a samu wanda ya yi nasara a zaɓen sabon Fafaroma da manyan limamai ke yi zuwa yanzu.

    Sai mutum ya samu kuri'a kashi biyu cikin uku na masu zaɓe kafin zai iya zama Fafaroma.

    Wannan na nufin limaman za su ci gaba da zama a zauren domin tantance wanda zai gaji marigayi Fafaroma Francis.

    An kulle manyan limaman a cikin cocin - kuma babu wata hanya da za su iya tattaunawa da wani a waje har sai an zaɓi sabon Fafaroma.

  12. Syria ta buƙaci a ɗage takunkuman da aka kakaba mata

    Ahmed al-Sharaa

    Asalin hoton, Reuters

    Sabon shugaban Syria, Ahmed al-Sharaa ya nemi a janye takunkumin da aka ƙaƙabawa ƙasar.

    Al-Sharaa ya nemi buƙatar ce yayin wata ganawa da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron a birnin Paris a ziyararsa ta farko zuwa Turai tun bayan hamɓarar da shugaba Bashar al-Assad daga mulki a ƙarshen shekarar da ta gabata.

    Shugaba Macron ya ce zai matsa lamba don ganin tarayyar Turai ta janye takunkumin da ta ƙaƙabawa Syrian a lokacin Mulkin Assad.

    Ya kuma bayyana cewa yana ƙoƙarin shawo kan shugaba Trump domin ya jinkirta kwashe dakarun Amurka daga Syria.

    Shugaban na Syria da tawagarsa suna ƙoƙarin shawo kan ƙasashen yamma ne domin su ɗage takunkumin da suka ƙaƙabawa Syria a lokacin gwamnatin Assad.

    A lokacin ziyarar a Paris, al-Sharaa ya kuma gana da wani ɗan ƙasar Syrian mai kwarmata bayanan sirri, wanda ya fitar da hotunan yadda gwamnatin Assad ke azabtar da ƴan Adawa.

  13. 'Yarjejeniyar tsagaita wuta da muka ƙulla ba ta nufin mun daina kai wa Isra'ila hari'

    Wani babban jami'in ƙungiyar Houthi ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta da suka ƙulla da Amurka ba ta nufin cewa sun daina kai wa Isra'ila hari.

    A ranar Talata ƙungiyar ta amince ta daina kai wa jiragen ruwan Amurka hari, idan har Washington ta kawo ƙarshen harin da take kai wa Yemen.

    Amma Mohammad Abdulsalem, wanda ke cikin tattaunawar tsagaita wutar ya ce yarjejeniyar ba ta shafi rikicin su da Isra'ila ba.

    Wakilin BBC ya ce: Isra'ila ta kai wani gagarumin hari a filin jirgin saman babban birnin ƙasar, a matsayin martani ga wanda Houthi ta kai a birnin Tel Aviv.

    Tun bayan watsewar tsagaita wuta a Gaza, mayaƙan Houthi suka ƙaddamar da hare-hare a kan Isra'ila.

  14. Ba ma son Najeriya ta zama mai jam'iyya ɗaya – Gwamnan Nasarawa

    Gwamnan Nasarawa

    Asalin hoton, AA Sule/Facebook

    Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ba ta son zama jam'iyya ɗaya a ƙasar.

    Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Talata bayan wata ganawa da shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda ya ce ya je ne domin tattauna batutuwan da suka shafi jihar da kuma jam'iyyar APC.

    Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan yanayin siyasa a ƙasar da kuma damuwa da ɓangaren adawa ke nunawa cewa ƙasar ta doshi zama mai jam'iyya ɗaya, gwamna Sule ya ce APC na son jam'iyyar da ke sahun gaba a ƙasar ne kaɗai, wadda za ta iya lashe zaɓuka.

    Ya kuma yi iƙirarin cewa batun canza sheƙa da ake ta yi, musamman zuwa jam'iyyar APC - na faruwa saboda irin ƙokari da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi, inda ya ce "hakan manuniya ce ta ƙwazon jam'iyyar APC da kuma Tinubu. Shugaban ƙasa na kawo sauye-sauye da dama. Mun ga wasu daga cikinsu."

    "Ban amince cewa za mu iya zama ƙasa mai jam'iyya ɗaya ba. Ida ka duba batun, kowace irin nasara za mu samu, hakan ba za ta faru ba, alal misali ga jam'iyyar Republican a Amurka da kuma Democra. Akwai jam'iyyar Green da kuma wasu da dama da ba ka jin labarinsu. Haka batun yake a Najeriya," in ji gwamna Sule.

  15. Yadda iyalai ke tserewa ƙauyuka bayan ɓarkewar rikici tsakanin Indiya da Pakistan

    Bayan kaddamar da hare-hare na cikin dare da Indiya ta yi, mutane da dama da ke zaune a wasu ƙauyuka da ke tsakann Indiya da Pakistan - na tserewa muhallansu.

    Waɗannan hotuna sun nuna yadda iyalai ke barin ƙauyukan Suchetgarh da Jeora - a yankin Kashmir da ke karkashi ikon Indiya.

    Indiya

    Asalin hoton, Reuters

    Indiya

    Asalin hoton, Reuters

  16. An sake kai hari birnin Port Sudan kwana huɗu a-jere

    Port Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwana na hudu a jere, birnin Port Sudan ya ci gaba da fuskantar hare-haren jirgin sama marar matuƙi, inda rundunar sojin Sudan ta ce ta daƙile wasu hare-haren da aka yi niyyar kai wa barikin sojin ruwanta.

    Wakiliyar BBC ta ce an jiyo ƙarar fashewa abubuwa da safiyar yau Laraba, kuma shaidu sun hango baƙin hayaƙi na tashi daga barikin sojin ruwa ta Flamingo.

    Hare-hare a birnin Port Sudan ya kawo gagarumin sauyi a kan yadda ake shigar da kayan agaji ga mabuƙata a ƙasar.

    Gwamnatin Sudan ta yanke huɗɗa da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a kan zargin tana tallafawa mayaƙan RSF.

  17. An yi wa masu fasa-ƙwaurin tururuwa ɗaurin shekara guda a Kenya

    Ants

    Asalin hoton, Reuters

    Wata kotu ta yanke wa mutum huɗu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yari ko kuma su biya tarar dala 7,700 saboda yunƙurin fasa-ƙwaurin dubban sarauniyar tururuwa daga ƙasar.

    An kama waɗanda ake zargin su huɗu ne – biyu 'yan Belgium da ɗan ƙasar Vietnam sai kuma wani ɗan Kenya – cikin watan jiya da dubban tururuwa mai rai kuma ana zargin za su kai su ƙasashen Turai da na Asiya.

    Sun dai amsa tuhume-tuhumen da aka yi musu, har ma 'yan ƙasar Belgium ɗin suka faɗa wa kotun cewa sun kama tururuwar ce wadda ake matuƙar nema saboda nishaɗi, kuma ba su san yin hakan laifi ba ne.

    Sai dai a hukuncin da ta yanke ranar Larabar nan, alƙalin ta ce nau'in tururuwar da suka kama na da matuƙar daraja kuma sun kwashi dubbai, ba ma 'yan kaɗan ba.

    Majistare Njeri Thuku ta ce ana iya ɗaukar kama tururuwa 'yan kaɗan a matsayin nishaɗi, amma ba kama sarauniyar tururuwa har 5,000 ba.

    "Tuni duniya ta yi asarar nau'o'in tururuwa a wani ɓangare saboda haɗama. Don haka lokaci ya yi da za a dakatar da wannan al'amari.

    Daga cikin nau'o'in tururuwar har da wata wadda da Ingilishi ake kira African harvester ant, kuma wasu dillalai a Birtaniya na sayen duk ƙwaya ɗaya a kan fam 170.

  18. Gwamna Zulum ya hana sayar da giya a jihar Borno

    Kwalabar giya

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayar da umarnin haramta sayar da barasa ko kuma giya a Maiduguri babban birnin jihar.

    Zulum ya ce an ɗauki matakin ne saboda yadda ake samun ƙaruwar rikici tsakanin masu adawa da juna a ƙungiyoyin asiri, da karuwanci, da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, da kuma ayyakan daba.

    "Na ji daɗi da na ga sojoji da ƴansanda da sauran ɓanagarorin tsaro na nan, saboda mafi yawan wadan nan abubuwa... wasu ne daga cikin sojojin da aka sallama daga aiki, da sauran jami'an tsaro da aka kora, da ma wasu daga cikin jami'an soji da ke aiki, da ma fararen hula," in ji Zulum.

    "Babu wani sabon abu a wannan doka, idan har muna son mu tsaftace birnin Maiduguri, to babu wanda za a bari."

  19. An dakatar da aƙalla jirage 550 daga tashi a Indiya da Pakistan

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hare-haren da suka faru tsakanin Indiya da Pakistan sun janyo dakatar da tashin kusan jirage 550 a ƙasashen biyu.

    Bayan harin jiragen sama da aka kai, an dakatar da tashin jirage 135 a Pakistan, yayin da a Indiya jirage 417 aka dakatar, kamar yadda bayanan na'urar da ke bibiyar jirage kai tsaye na Flightradar24 suka nuna.

    A ranar Laraba, an ga fasinjoji cike a filin jirgin Sama na Jinnah da ke Karachi, suna jiran jiragen.

  20. Mun harbo jiragen saman Indiya biyar - Firaministan Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ya bayyana wa majalisar dokokin ƙasar cewa dakarun tsaron Pakistan sun harbo jiragen sama na Indiya biyar, kamar yadda rahotannin kafafen yada labarai na Pakistan suka nuna.

    Ya ce biyu daga cikin jiragen sun faɗi ne a yankin Kashmir, yayin da daya kuma ya fadi a Bathinda da ke ƙasar Indiya.

    Har yanzu ba a ji wani martani daga ɓangaren Indiya ba kan wannan ikirari.

    ...

    Asalin hoton, Pakistan's PM Office/Getty Images