Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Daga nan BBC Hausa, muke cewa mu kwana lafiya.

  2. Gwamnan Darfur ya soki sojoji kan rashin kawo karshen ƙawanyar da aka yi wa yankin

    Gwamnan yankin Darfur da ke Sudan ya soki sojojin gwamnati da gaza kawo karshen ƙawanyar da aka yi wa yankinsa wanda ya jefa al'ummar birnin El Fasher cikin matsananciyar yunwa.

    Minni Minawi, ya kasance tsohon jagoran ƴan tawaye ne har yanzu kuma shi ke jagorantar wasu mayaƙa masu ɗauke da makamai waɗanda ke taimakawa sojojin ƙasar wajen kare birnin daga hannun mayakan RSF.

    Sai dai duk da haka ana fama da yunwa a birnin inda kuma ba a iya shigar da kayan agaji.

    Yanayin jin-kai a El Fasher na ƙara munana a kullum.

    Mayaƙan RSF na ƙoƙarin ganin sun ƙwace ikon birnin fiye da shekara guda - inda suka hana shigar da abinci lamarin da ya jefa fararen hular birnin cikin matsananciyar yunwa.

    Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam da dama sun ce mayaƙan RSF na aikata kisan kiyashi da kuma kai hare-haren da ba su dace ba kan fararen hula da asibitoci.

  3. Remi Tinubu ta bai wa iyalan da rikicin Benue ya ɗaiɗaita tallafin biliyan ɗaya

    Mai ɗakin shugaban Nijeriya, Remi Tinubu ta bai wa waɗanda rikicin jihar Benue ya ɗaiɗaita tallafin naira biliyan ɗaya, domin rage musu raɗaɗin da suka shiga.

    Remi ta bayyana haka ne a yau Talata a gidan gwamnatin jihar ta Benue lokacin da ta kai ziyarar ta'aziyya ga al'ummar jihar, bayan hare-haren da wasu suka kai garin Yelewata a watan Yuni - abin da ya janyo asarar rayuka sama da 100.

    Remi ta ce an bayar da tallafin ne don taimakawa iyalai da aka ɗaiɗaita, sannan su kuma samu damar komawa muhallansu da farfaɗowa da kuma gina rayuwarsu.

    "Wannan gudummawa yana karkashin shirin mu na Renewed Hope Initiative ne, wanda manufarsa ita ce kyautata rayuwar iyalai," in ji mai ɗakin shugaban Najeriyar.

    Ta kuma nuna damuwa kan kashe-kashen da suka faru a jihar a makonnin baya.

    "A matsayina na uwa, ina so dukkanmu mu ɗauki wannan iftila'i a matsayin lokaci ne na kalubale. Aikin mu shi ne taimakawa waɗanda abin ya shafa," in ji Remi Tinubu.

  4. An kashe mutum huɗu tare da kama ɗaruruwan masu zanga-zanga a Angola

    Ƴansanda a Angola sun ce an kashe mutum huɗu sannan an kama sama da 500 bayan da zanga-zanga ta ɓarke a Luanda, babban birnin ƙasar.

    Lamarin da ya fara da yajin aikin direbobin tasi na kwana uku kan tsadar farashin fetur ya rikiɗe zuwa zanga-zangar gama-gari a faɗin ƙasar wanda ƙasar ba ta gani ba cikin shekaru.

    Dubban mutane ne suka shiga zanga-zangar ta ranar Litinin a babban birnin ƙasar, abin da ya janyo rufe hanyoyi, ɓalla shaguna da satar kayayyaki da kuma lalata motoci har ma da artabu tsakanin masu zanga-zangar da kuma ƴansanda.

    Tun ranar Litinin da daddare aka samu rahoton harbe-harben binidiga a wasu sassan Luanda.

    An ci gaba da zanga-zangar yau Talata a Luanda, inda aka ƙara samun bata-kashi tsakanin ƴansanda da masu zanga-zangar da kuma ɓalla shagunan mutane, yayin da zanga-zangar ta bazu har zuwa birnin Huambo.

    "Batun tsadar man fetur ya zama abu na karshe da ya sanya mutane fitowa domin nuna fushinsu... mutane sun gaji. Yunwa ta tsananta sannan talakawa na cikin ƙara shiga ƙunci," kamar yadda wata mai fafutuka, Laura Macedo ta faɗa wa BBC.

  5. Gwamnan Gombe ya ce arewa za ta mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027

    Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce yankin arewacin Nijeriya za ta mara wa shugaba Bola Tinubu a fafukarsa ta neman tsayawa zaɓe a 2027.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a yau Talata a wani taron kwanaki biyu na shugabannin arewa da ake gudanarwa a jihar Kaduna domin duba irin ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ta yi, musamman kan abin da ya shafi walwalar ƴan yankin.

    Ya ce goyon baya da aka bai wa Tinubu a zaɓen 2023 ya fara haifar da ɗa mai ido a ɓangarorin ayyukan more rayuwa da tsaro da noma da kuma makamashi.

    Taron wanda gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya, ta samu halartar gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, gwamnan Gombe Inuwa Yahaya, sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci, hafsoshin tsaro da kuma sauran ƴansiyasa daga yankin arewa.

  6. An samu raguwar hare-haren Boko Haram da na ƴan bindiga - Ribadu

    Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkar tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce an samu raguwar hare-haren Boko Haram da na ƴanbindiga har ma da rikice-rikice tsakanin al'ummomi a yankin arewacin ƙasar cikin shekaru biyu da suka wuce karkashin gwamnatin shugaba Tinubu - idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.

    Ya bayar da misalin cewa an kashe mutum 1,192 sannan an sace sama da 3,348 a jihar Kaduna a gwamnatin da ta shuɗe, yayin da sama da mutane 5,000 suka rasa rayukansu a jihar Benue a wannan lokaci.

    Ribadu ya bayyana haka ne a yau Talata yayin jawabi a taron masu ruwa da tsaki na arewacin Najeriya wanda aka gudanar a jihar Kaduna.

    Ya ce nasarar da aka samu a yaƙi da rashin tsaro ya samo asali ne sakamakon umarnin da shugaba Tinubu ya bai wa jami'an tsaro kan bin tsarin tabbatar da tsaro na bai-ɗaya.

    Ya ƙara da cewa an samu nasarar sakin mutum 11,259 waɗanda aka yi garkuwa da su a watan Mayu kaɗai - a wasu samame daban-daban da sojojin Najeriya suka kai a arewa maso yamma.

    Ribadu ya kuma bayyana cewa jami'an tsaro sun kashe shugabannin ƴanbindiga da mambobinsu da dama a jihohin Zamfara da Kaduna da kuma Katsina.

    Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani kan amfani da hanyoyi daban-daban wajen shawo kan matsalar tsaro a kudancin jihar da Birnin Gwari har ma da wasu yankuna da ke fama da matsalar tsaro a faɗin jihar.

  7. Ouattara zai sake tsayawa takarar shugaban Cote d'Ivoire karo na huɗu

    Shugaban ƙasar Ivory Coast Alassane Ouattara mai shekara 83, ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa karo na huɗu - wanda za a yi a ranar 25 ga Oktoba.

    Sanarwar da ya yi a kafafen sada zumunta, na zuwa ne bayan da jam'iyyarsa ta Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP) ta amince da takararsa a hukumance.

    A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki.

    Tuni dai shugabannin ‘yan adawa suka yi Allah-wadai da matakin, suna zargin cewa gwamnatinsa ta yi wa dokar zaɓe garambawul ne domin durkusar da manyan abokan hamayya.

    Tsohon shugaban ƙasar Laurent Gbagbo, da tsohon Firaminista Guillaume Soro, da kuma tsohon minista Tidjane Thiam duk an cire saunayen su daga rajistar masu zaɓe, lamarin da ya hana su tsayawa takara.

    Hankali ya ƙara tashi a yau bayan da hukumomi suka haramta zanga-zangar lumana da aka shirya yi a ranar 7 ga watan Agusta, ranar bikin samun 'yancin kai na Cote d'Ivoire.

    Ƙungiyoyin 'yan adawa ne suka shirya zanga-zangar da nufin neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan jerin sunayen masu kaɗa kuri'a tare da mayar da sunayen waɗanda aka hana tsayawa takara.

    Matakin na Ouattara ya yi nuni da wani gagarumin sauyi daga alkawuran da ya yi a baya na miƙa mulki ga sabbin shugabanni.

    Har ila yau, ya kasance wani tunatarwa da tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaɓukan da suka gabata - ciki har da rikicin bayan zaɓen 2010-2011 wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 3,000, da tashin hankalin da ya biyo bayan yunkurinsa na neman wa'adi na uku a shekarar 2020.

    Sama da masu jefa kuri'a miliyan 8.7 ne suka yi rajista don kaɗa kuri'a a zaɓen mai gabatowa.

    Ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin addinai, ciki har da ƙungiyar limaman cocin Katolika, sun nuna fargaba game da ƙaruwar rikice-rikicen siyasa, inda suka yi gargadin cewa za a iya samun sake ɓarkewar tashin hankali.

  8. Kungiyar malaman jami'ar jihar Yobe ta janye yajin aiki

    Ƙungiyar malaman jami'a reshen jami'ar jihar Yobe sun sanar da janye yajin aiki da suka shiga ranar 11 ga watan Yulin, 2025.

    Shugaban malaman jami'ar, Ahmed Karange, ya bayyana cewa sun cimma yarjejeniya da gwamnatin jihar ta Yobe, inda ta yi alkawarin biyan sauran buƙatu da malaman ke nema.

    "Bayan cimma yarjejeniyar, shugaban malaman jami'ar ya bayar da damar janye yajin aikin," kamar yadda sanarwar da suka fitar ta bayyana.

    Sanarwar ta buƙaci dukkan mambobi da su koma bakin aiki nan take.

  9. Matatar Dangote ta janye ƙarar da ta maka kamfanin NNPCL a kotu

    Matatar man Dangote ta janye ƙarar da ta shigar a gaban kotu kan hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA da kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL, da kuma wasu kamfanonin mai guda biyar.

    Ƙarar da aka shigar ta nemi waɗanda ake ƙara da su biya diyyar naira biliyan 100.

    Ƙarar dai ta zargi NMDPRA da bayar da lasisin shigo da man fetur ba bisa ka’ida ba, wanda Dangote ya ce ya saɓa da dokar masana’antar man fetur ta 2021.

    Sauran kamfanonin da aka kai ƙara sun haɗa da AYM Shafa da A.A. Rano da T. Time Petroleum, 2015 Petroleum da kuma Matrix Petroleum.

    Dangote ya buƙaci kotu ta bayyana cewa NMDPRA ba ta tallafa wa matatun cikin gida yadda doka ta tanada ba.

    Sai dai waɗanda aka kai ƙara sun mayar da martani cewa suna da cikakken cancantar karɓar lasisin, kuma Dangote na ƙoƙarin neman mamaye kasuwar man fetur a Najeriya ne gaba ɗaya.

    A wata takarda da lauyoyin Dangote suka gabatar a kotu, sun bayyana cewa kamfanin ya yanke shawarar janye karar, ba tare da bayyana dalili ba.

    Babu tabbacin ko an cimma yarjejeniya a bayan fage.

  10. Wane ne sabon sarkin Gusau Abdulkadir Ibrahim Bello?

    Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon sarkin Katsinan Gusau.

    Hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifinsa Dr Ibrahim Bello a daren Juma'a 25 ga watan Yulin 2025 bayan doguwar jinya a wani asibiti da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

    Alhaji Abdulkadir zai maye gurbin ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar.

    Sanarwar da sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad ya fitar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin, wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.

    Karanta cikakken labarin a nan...

  11. Labarai da dumi-dumi, Birtaniya za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa a watan Satumba - Starmer

    Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce ƙasar za ta amince da kafa ƙasar Falasɗinawa a watan Satumba a taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

    Firaiministan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gudanar a ranar yau Talata.

    Starmer ya ce hakan zai tabbata "har sai idan Isra'ila ta ɗauki matakai na kawo karshen abin da ke faruwa a Gaza, ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, ta kuma tabbatar da cewa ba za a ƙwace Gaɓar Yamma ba, har ma da cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tsawon lokaci da za ta haifar da mafitar ƙasashe biyu".

    Firaministan ya ƙara nanata cewa babu wani bambanci tsakanin Isra'ila da Hamas kuma buƙatar da Birtaniya take da su kan Hamas suna nan - cewa dole su saki dukkan waɗanda suke garkuwa da su, su saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, su kuma amince cewa ba za su saka baki a gwamnatin Gaza ba sannan su ajiye makamai.

    Starmer ya ce za su ci gaba da duba lamarin da ke faruwa a Gaza gabanin taron babban zauren MDD Da za a yi don ganin yadda ɓangarorin biyu suka ɗauki matakai na samar da zaman lafiya kafin ta ɗauki mataki na karshe.

  12. Rasha na son fara haƙar makamashin Uranium a Nijar

    Ƙasar Rasha ta ce tana so ta fara haƙar ma'adanin Uranium a Jamhuriyar Nijar domin samar da makamashin nukiliya a cikin ƙasar.

    Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar ta Nijar shekaru biyu da suka gabata, jagororinta suka yanke hulɗa da ƙasashen Yamma tare da karkatawa zuwa bangaren Rasha, wadda take da tarin makaman ƙare-dangi fiye da kowace ƙasa a duniya.

    Haka nan gwamnatin mulkin sojin ta Nijar ta yi yunƙurin ƙwace iko da filayen haƙar ma'adanin uranium waɗanda a baya suke ƙarƙashin wani kamfani na Faransa.

    A lokacin wata ziyarar aiki a Yamai, babban birnin na Nijar, hukumar sarrafa makamashin atam ta Rasha, Rosatam da ma'aikatar makamashi ta Nijar sun sanya hannu kan yarjejeniyar amfani da makamashin nukilya bisa tafarkin zaman lafiya.

  13. 'Ana fuskantar yanayi mafi muni na yunwa a Gaza'

    Hukumar sanya ido kan bala'in yunwa da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ce ana fuskantar yanayi mafi muni na yunwa a Gaza.

    Rahoton hukumar ya bayyana irin yunwa da rashin abinci mai gina jikin da ake fama da shi a Gaza inda aka kwantar da yara fiye da dubu 20 a asibiti sakamakon rashin abinci mai gina jiki a tsakiyar watan da muke ciki kawo yanzu, sannan kuma an ƙara samun mace-macen yara saboda yunwa.

    Jami'ai a shirin samar da abinci na MDD sun ce hukumomin Majalisar na da dama da kuma Ƙwararrun da za su samar da agaji a Gaza, a don haka dama kawai suke jira.

    Isra'ila dai ta nanata cewa duk da yake akwai ƙarancin abinci a Gaza, amma babu yunwa, sai dai kuma shirin samar da abinci na MDD ya ce halin da ake ciki a Gazan ya wuce hankali da kuma irin abinda ya faru a Habasha da kuma Biafra a Najeriya.

  14. Ɗan sanda da wasu uku sun mutu a harbin bindiga a birnin New York

    Wani mutum ɗauke da bindiga ya kashe mutane hudu a birnin New York na Amurka, ciki harda wani ɗansandan birnin.

    Maharin ya kuma yi wa wani mutum mummunan Rauni, kafin daga baya ya kashe kansa.

    Maharin ya yi tattaki riƙe da bindiga a hannu daga wajen ajiye motoci zuwa cikin ginin da ya aikata ɓarnar, inda ya kutsa kai sannan ya buɗe wuta kan mutane.

    Ya kuma shige har hawa na 33 na ginin, kuma a can ma ya aikata kisa.

    A yayin taron manema labarai ɗazunnan, kwamishinan ƴansandan birnin New York, Jessica Tisch, ta yi bayanin yadda lamarin ya faru.

    ''Bidiyo ya nuna wani mutum ya fita daga cikin wata baƙar mota ƙirar BMW da aka ajiye a gefen ginin, kuma yana riƙe da bindiga ƙirar M4 a hannunsa na dama, inda ya doshi ƙofar shiga ginin.

    ''Na'urar ɗaukar bidiyo ta nuna yadda mutumin ya shiga cikin ginin, ya kuma buɗe waw ani ɗansandan birnin New York wuta nan take. Daga nan kuma ya harbi wata mata da ta ɓoye a jikin turken ginin, sannan ya kutsa kai ciki, ya kuma buɗe wuta.'' In ji Jessica Tisch.

    Ƴansanda sun ce sunan maharin Shane Tamura, kuma matashi ne mai shekara 27 ɗan asalin Las Vegas.

    Hukumomi sun ce kawo yanzu babu masaniya kan dalilinsa na aikata wannan ɓarna, amma ana ci gaba da bincike.

    Harin ya jawo firgici da gudun jama’a a titi.

  15. Sojojin Najeriya sun daƙile harin mayaƙan ISWAP a Bitta na jihar Borno

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na Operation HADIN KAI sun samu nasarar daƙile wani hari da mayakan ƙungiyar JAS da ISWAP suka kai a garin Bitta da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno da misalin ƙarfe.

    Rundunar ta bayyana cewa maharan sun zo ne daga yankin Damboa, inda suka yi yunƙurin kutsawa cikin sansanin sojoji.

    A cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce mayakan sun samu nasarar shiga wani ɓangare na sansanin tsaron sojin na ɗan lokaci, amma sojojin sun daƙile harin cikin gaggawa bayan wata musayar wuta mai zafi.

    Rundunar ta ce sojojinta sun kashe wasu daga cikin ƴan bindigan tare da ƙwato bindigogi kirar AK-47 daga hannunsu.

    Sanarwar ta ƙara da cewa babu asarar rai ko raunuka da aka samu a ɓangaren sojojin Najeriya.

    A ranar 28 ga Yuli, 2025 kuma muƙaddashin kwamandan rundunar tare da wasu manyan kwamandoji, sun kai ziyara a Bitta domin duba halin da ake ciki da kuma ƙarfafa gwiwar dakarun.

    Rundunar ta ce al'amura sun lafa a halin yanzu, kodayake halin tsaro har yanzu ba tabbatacce ba ne.

  16. Waɗanda aka kashe a Gaza sun haura 60,000 - Ma'aikatar lafiyar Gaza

    Ma'aikatar lafiyar Gaza da ke ƙarƙashin kulawar Hamas ta ce waɗanda Isra'ila ta kashe daga ranar 7 ga Oktoban shekarar 2023 da aka fara yaƙin sun haura 60,000 zuwa yanzu.

    Ma'aikatar ta ce, "yanzu waɗanda aka kashe sun kai 60,034, sannan waɗanda suka jikkata sun kai 145,870," kamar yadda ta bayyana a sanarwar da ta fitar.

    Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce an kashe mutum 113, sanan aka jikkata wasu 637 a cikin kwana ɗaya, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ta bayyana.

    Sanarwar ta ƙara da cewa akwai wasu mutane da ake tunanin sun maƙale a ƙarƙashin baraguzai.

  17. Dabbanci ne kashe mutum 30 da ƴanbindiga suka yi - Gwamnan Zamfara

    Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ya bayyana kashe sama da mutum 30 da ƴanbindiga suka yi daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su a matsayin dabbanci da rashin sanin darajar ɗan'adam.

    Gwamna Dauda Lawal ya bayyana haka ne bayan wasu ƴanbindiga a jihar sun kashe wasu mutane da ke hannunsu, lamarin da gwamnan ya ɗauki alwashin cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai makasan sun ɗanɗana kuɗarsu.

    An yi garkuwa da gomman mutanen ne a ƙauyen Banga kimanin wata huɗu da suka gabata, kafin ƴanbindigar suka kashe su saboda ba a biya kuɗin fansa ba.

    Rahotanni sun ce da yawa daga cikin mamatan yankar rago aka yi musu.

  18. 'Ban ga abin magana ba don Tinubu ya ba ƴanƙwallo kyautar dala 100,000'

    Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Bayo Onanuga ya ce bai ga abin magana domin shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya ba ƴanƙwallon ƙasar mata da suka lashe gasar cin kofin Afirka ta mata kyautar dala 100,000 kowannensu.

    Bayo ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook a matsayin martani ga masu sukar kyautar, inda ya ce ko shirin BBNaija ana bayar da kyauta mai gwaɓi kamar haka.

    Ya ce, "idan ka tuna cewa yadda Multichoice masu shirya BBNaija suke ba wanda ya zo na ɗaya kyautar naira miliyan 150, sai ka fara tunanin me ya wasu ƴan Najeriya suke sukar kyautar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba ƴanƙwallon Najeriya mata kyautar dala miliyan 100,000,"

    Ya ƙara da cewa Tinubu yana ƙarfafa gwiwar hazaƙa da ƙarfin gwiwa da sauran abubuwa da ke ɗaga darajar Najeriya a idon duniya.

  19. Ƴanbindiga sun yi barazanar kashe ɗaliban aikin lauya idan ba a biya kuɗin fansa ba

    Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun ƙwarewar a aikin lauya da aka sace a jihar Benue sun ce idan ba a biya kuɗin fansa ba, za ku kashe su, kamar yadda kafar The Punch ta ruwaito.

    An sace ɗaliban ne a ranar 26 ga watan Yulin a hanyarsu ta zuwa makarantar domin samun horo da ke Yola a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin ƙasar daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashi.

    Kafar ta Punch ta ruwaito daga wata majiya cewa masu garkuwar sun ƙara kuɗin fansar daga dala 13,110 zuwa dala 32,688 kan kowane ɗalibi, sannan suka yi barazanar kashe ɗaliban matuƙar ba a biya kuɗin ba.

    "Sun ce idan ba mu kawo kuɗin ba, za su kashe su, sanan sun gargaɗe mu kada mu saka jami'an tsaro a maganar."

    Kakakin runduar ƴansandan jihar Adamawa, Yahaya Suleiman ya ce suna aiki tare da rundunar jihar Benue domin ceto ɗaliban.

  20. Harin Rasha a gidan yari ya kashe aƙalla mutum 16 - Ukraine

    Ukraine ta ce Rasha ta kai hari a wani gidan yari da ke kudancin Zaporizhzhia tare da kashe aƙalla mutum 16 da raunata wasu da dama.

    Harin da Rasha ta kai cikin dare ya lalata ginin gidan yarin da kuma gidajen da ke kusa.

    Sai dai ita ma Rasha ta ce Ukraine ɗin ta kai hare-haren jirage marasa matuƙa a lardin Rostov da ke ƙasar.

    Sannan hukumomi sun ce harin ya yi sanadiyar kashe mutum ɗaya.