Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/07/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Cambodia ke saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta - Thailand

    Thailand ta zargi Cambodia da saɓa yarjejeniya tsagaita wuta da aka amince bayan kwana biyar na rikicin kan iyaka tsakaninsu.

    Thailand ta ce Cambodia ta kai hare-hare wurare da dama jim kaɗan bayan yarjejeniyar tsagaita wutar ta fara aiki, wanda ya sa sojojin Thailand suka mayar da martani.

    An bayar da rahoton cewa kura ta lafa a yanzu, amma an dage tattaunawar da ya kamata kwamandojin soji su yi.

    A jiya Litinin ne aka amince da yarjejeniyar tsakanin Thailand da Cambodia a tattaunawar da Malasia ta jagoranta

  2. Ƴan Ghana na so a faɗaɗa tilascin amfani da kuɗin ƙasar maimakon dala

    A ƙasar Ghana masana ne ke ci gaba da tsokaci tare da yin kira ga gwamnatin Ghana na ta faɗaɗa sabon umarnin amfani da kuɗin cedi maimakon dalar Amurka.

    Masu ruwa da tsaki a ƙasar suna kira da a tilasta amfani da ƙudin ƙasar waje hada-hada wasu muhimman abubuwa, ba kawai a biyan ƴankwangila da sauran sassan cibiyoyi da ma`aikatun gwamnatin.

    Ministan kuɗi na Ghana ne ya sanar da matakin na dakatar da biyan ƴankwangila da dala, sannan babban bankin ƙasar ya ce an ɗauki matakin ne don farfado da kudin ƙasar

  3. Gwamnan Zamfara ya naɗa Sarkin Gusau

    Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.

    Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.

    Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar, inda ya ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa.

    Sabon sarkin ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.

    Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.

    Ya kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.

  4. Agajin da ake kai wa Gaza kamar ɗigon ruwa ne a cikin teku - MDD

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa mutanen Gaza suna matuƙar fama da matsananciyar yunwa, bayan Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce lamarin bai kai yadda ake tunani ba.

    Trump ya bayyana haka ne a lokacin da aka tambaye shi ko ya amince da bayanin Netanyahu cewa babu matsananciyar yunwa a Gaza, inda ya ce, "da ganin yaran ka san suna cikin yunwa mai tsanani. Wannan ma ai kisan mummuƙe ne."

    Trump ya bayyana a lokacin da yake tattaunawa da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer a Scotland cewa, "babu wani wanda ya ɗauki mataki mai muhimmanci a kan lamarin. Baki ɗaya zirin ya ɗaiɗaice, na faɗa wa Isra'ila cewa ya kamata ta sauya salo."

    Jawabin Trump na zuwa ne bayan shugaba ayyukan jin-ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya ce ana buƙatar abinci sosai domin daƙile matsananciyar yunwa a Gaza.

    Ya ce ya yi maraba da matakin da Isra'ila ta ɗauka na barin a jefa wa mutanen Gaza abinci ta sama, sai dai ya ce abincin da aka kai, tamkar "ɗigon ruwa ne a cikin teku."

  5. Dole a bar mana kujerar mataimakin shugaban ƙasa - Tsagin ANPP

    Tsagin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP da ke cikin babbar jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya sun ce lallai ne a bar musu kujerar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027, inda suka buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi watsi da buƙatar nemo wani daban.

    Tsagin ANPP ɗin sun ce su ne na biyu wajen ƙarfi a haɗakar da aka yi a shekarar 2013 da ta haifar da jam'iyyar APC, inda suka yi barazanar cewa yin watsi da su a tikitin takarar zaɓen 2027 zai iya tilasta musu su fara tunanin sauya sheka daga APC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ƙungiyar tsofaffin mambobin ANPP ne suka bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, inda suka ce ba a saka musu yadda ya dace ba bisa babbar gudunmuwar da suka bayar wajen kafa jam'iyyar APC.

    Jagoran ƙungiyar Farfesa Vitalis Orikeze Ajumbe ya ce, “za a samu matsala a takarar 2027 idan aka ɗauki wanda ba ɗan tsagin ANPP ba a matsayin mataimakin shugaban ƙasa."

    Ya ce tsaginsu na ANPP ya sha wahala tare da fuskantar wariya a zamanin mulkin Marigayi Muhammadu Buhari.

    Ya ce daga cikin mambobin su akwai mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da gwamnoni irin su Babagana Umara Zulum na jihar Borno da Mai Mala Buni na jihar Borno da tsofaffin gwamnoni irin su Attahiru Bafarawa da Sani Yarima Bakura da Ali Modu Sheriff da sauran su.

  6. Ambaliyar ruwa ta kashe aƙalla mutum 30 a China

    Aƙalla mutum 30 ne suka mutu a yankunan da ke wajen birnin Beijing sakamakon mummunar ambaliyar ruwa.

    Wakilin BBC ya ce jami'ai sun ce kimanin ƙauyuka 130 ne suka kasance ba lantarki yayin da masu agaji ke amfani da jirage masu saukar ungulu don isa ga al’ummar da bala'in ya shafa kasancewar ruwa ya mamaye hanyoyi.

    An kwashe mutane kimanin dubu 80 daga yankunan da ambaliyar ta mamaye, wanda hakan ya sa tuni Beijing ta yi babban gargaɗi game da ambaliyar.

    Mamakon ruwan sama ne ya yi sanadiyar ambaliyar, wadda ta haifar da zabtarewar ƙasa - da tafiya da motoci.

  7. Buɗewa

    Jama'a barkamu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin na labaran kai-tsaye na BBC Hausa, inda za mu ɗaura daga inda muka tsaya a jiya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa irin su Facebook da Instagram da X da ma zaurenmu na Whattsap domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.