Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/12/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Fulani na zargin ƴan sa-kai da cin zali a Zamfara

    ...

    Ƙungiyoyin Fulani a yankin arewacin Najeriya na nuna damuwa game da abin da suka kira jama'u da ake yi wa al'ummarsu sanadiyyar matsalar tsaro da ake fama da ita a yankin.

    Suna zargin cewa ana zaluntar ƴan ƙabilar ta Fulani wadanda ba su, ba su gani ba ta hanyar cin mutuncinsu da kona masu rugage da kwashewa ko ma karkashe masu dabbobi, baya ga kisan gilla da ake yi masu a wurare da dama.

    Hakan kuwa yana hana su walwala da shiga garuruwa, da kasuwanni da cudanya da sauran jama'a.

    Ƙorafi na baya-baya nan da al'ummar Fulanin ke yi game da irin tsangwamar da suke kukan ana yi musu ya fito ne daga jihar Zamfara inda wani magidanci Bafulatani a ƙaramar hukumar Gumi, ya ce Fulani sun zama masu fargabar fitowa ko yin tafiya a kan tituna saboda hare-haren ‘yan sa-kai ba don komai ba, sai domin kasancewarsu Fulani.

    "Yanzu haka da nake magana, hanyarmu nan daga Gumi, Bafulatani bai isa ya wuce ba saboda matsalar ƴan sa-kai, kama mu suke yi su kashe."

    Lokacin da aka tambaye shi ko wasu ɓata-gari ne ke aikata hakan, sai ya ce: "Ba yan ɓata gari ne ke aikata hakan ba, ƴan sa-kai ne ɗauke da makamai," in ji shi.

    Da aka tambaye shi ko yana ganin zargin wasu Fulani ne da ke kai hare-hare ne ya jawo hakan, sai ya ce "Cikin Fulanin, ba kowa ba ne ɗan ta'adda.

    Zamfara da sauran jihohin arewa maso yammacin ƙasar na fama da matsalar ƴan bindiga masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

    Ana zargin cewa Fulani ne waɗanda suka fi yawa cikin ƴan bindigar da ke kai hare-haren kan al'umma.

    Sai dai wani abuda masana ke ganin yana iza wutar rikicin shi ne ayyukan ƴan sa-kai da ke kare ƙauyukan da ake kai wa hari, inda a wasu lokuta ake zargin cewa sukan dauki matakai ba tare da bin ƙa'idojin doka ba sanadiyyar rashin ƙwarewa.

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Za mu yi bincike - gwamnatin Zamfara

    A martaninta, gwamnatin jihar Zamfara dai ta yi Allawadai da aukuwar irin wannan lamari kuma ta lashi takobin magance matsalar, a cewar Mustapha Jafaru Kaura, mai bayar da shawara kan harkokin yaɗa labarai ga gwamnan jihar Dauda Lawal.

    "Shi wannan lamari na ƴan sa-kai da ke kashe Fulani a Zamfara, gwamnatin jihar ba ta tare da duk wani nau'i na cin zali da cin zarafi ko tsangwama kuma ba za ta lamunci irin waɗannan abubuwan ba."

    "Za a haɗa kwamiti ba da dadewa ba domin gudanar da bincike da kuma hukunta masu laifi."

    Jihar Zamfara ta kafa rundunar tsaro ta Askarawa, wadda ke taimakawa bayan sojojin gwamnatin Najeriya da ke aiki a yankin.

    Sai dai a baya an zargi Askarawan da wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu, inda har gwamnatin jihar ta ce za ta gudanar da bincike a kai.

  2. Dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Australia

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya.

    Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi.

    Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki.

    Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat.

    Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar.

    Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.

  3. Ana ta ce-ce-ku-ce a Kano kan ƴunƙurin kafa sabuwar ƙungiyar hisbah

    ...

    Asalin hoton, PT

    Cece-kuce na ci gaba da kunno kai kan yunkurin kafa sabuwar kungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar Kano wacce tsohon gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya ɓullo da ita.

    Wannan yunkuri ya gamu da suka daga ɓangarori daban-daban, musamman daga gwamnatin Kano, wacce ta bayyana cewa kafa irin wannan ƙungiya ya saɓawa doka, kana kuma na iya zama tamkar kishiya ga hukumar Hisbah ta gwamnati.

    Gwamnatin Kano ta yi gargadin cewa tsarin na iya haifar da barazana ga tsaro da kuma tsarin doka na jihar.

    Wasu masu rajin kare doka da oda suma sun yi Allah-wadai da shirin, inda suka ce akwai haɗari a bari mutane su kafa irin wannan runduna ba tare da kulawar gwamnati ba.

    Daya daga cikin masu sukar tsarin, Barista Sadiq Sabo Kurawa, ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ba ta da tushe a tsarin doka.

    Sai dai waɗanda ke goyon bayan shirin sun musanta wadannan zarge-zarge.

    Sheikh Harun Ibn Sina, tsohon kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano wanda ake ganin shi ne jagoran sabon tsarin, ya ce kungiyar Independent Hisbah fisabilillah ba wai za ta yi takara da hukumar hisbah ta gwamnati bane, illa dai ta taimaka wa al’umma ta hanyar gudanar da ayyuka na kyautata tarbiyya da tallafa wa jama’a.

    Bayanai sun nuna cewa an riga an ƙaddamar da tsarin neman shiga kungiyar, inda aka fitar da fom, kuma ɗimbin mutane daga ƙananan hukumomi 44 na jihar sun halarci taron ƙaddamarwar domin nuna goyon bayansu ga shirin da bangaren Ganduje ya bullo da shi.

  4. Wace rawa sojojin Najeriya da Tinubu ya aika Benin za su taka?

    ...

    Asalin hoton, HQ NIGERIAN ARMY/FACEBOOK

    A daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da shirye-shiryen tura dakaru zuwa Jamhuriyar Benin mai maƙwabtaka da ƙasar domin tabbatar da zaman lafiya da dimukuraɗiyya, tuni an fara tafka muhawa a faɗin ƙasar kan rawar da jami'an tsaron Najeriya za su iya takawa.

    Tuni majalisar dattawan Najeriya ta amince da buƙatar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike mata, yana neman sahalewarta domin tura sojoji zuwa ƙasar domin kwantar da tarzoma bayan wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a baya bayan nan, inda shugaban ya bayyana cewa zaman lafiya a ƙasar na da muhimmanci ga zaman lafiya a Najeriya.

    Sanatocin dai sun kaɗa kuri'ar amincewa da tura sojojin da gagarumar, inda suka bayar da goyon bayan majalisa kan batun tabbatar da tsaro a yankin.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.