Gasar kofin duniya 2026: Sifaniya ta ragargaji Saudiyya

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Spain 4 , Saudi Arabia 0 at Full time
Spain
Saudiyya
Full time
Hutun rabin lokaci Spain 3 , Saudiyya 0

Key Events

Spain

  • Lamine Yamal Goal 10 minutes
  • Mikel Oyarzabal Goal 21 minutes, Goal 24 minutes
  • Hassan Al Tambakti Own Goal 49 minutes

Saudiyya

    Ba da ƙwallo a ci
    Spain,Mikel Oyarzabal (10 minutes), Aymeric Laporte (21 minutes), Dani Olmo (24 minutes)

    Taƙaitattu

    Rahoto kai-tsaye

    Mohammed Abdu tare da taimakon AI

    1. Lamine Yamal na Spain, Moteb Al Harbi na Saudiyya, Salem Al Dawsari

      Asalin hoton, Getty Images

    2. , Spain 3-0 Saudi Arabia

      Bana tsammanin akwai wata tawaga da ta fi bukatar hutun shan ruwa kamar ta Saudi Arabia a wannan lokaci.

      Duk abin da koci, Georgios Donis ya fadawa yan wasansa, ya kamata ya kasance mai tasiri sosai.

    3. An je hutun shan ruwa

      Dan karamin lokaci ake warewa yan wasa domin su sha ruwa, sannan a ci gaba da wasa, saboda yanayin zafi da ake fama da shi.

      Yanzu za a ci gaba da karawar Sifaniya ta ci kwallo uku.

    4. GOAL - Spain 3-0 Saudi Arabia, Mikel Oyarzabal

      Wasan nan zai zama mummuna ga Saudiyya.

      Oyazaaabal ne ya kara na uku na biyu a wasan, kuma cikin ruwan sanyi ya zura a raga.

      Saudiyya kamar babu yan baya da yawa haka suke barin gida Siafniya na samu kwallo cikin ruwan sanyi.

      Oyazabal, wanda ya kasa kokari a wasan farko da Cape Verde, yanzu yana wanke kansa.

      Mikel Oyarzabal na Spain ya ci kwallo

      Asalin hoton, Getty Images

    5. GOAL - Spain 2-0 Saudi Arabia, Mikel Oyarzabal

      Kwana ce aaaka buga daga baya aka mayar da ita cikin gidan Saudiyya ana ta kokarin fitar da ita sai Oyazabal ya samu ya buga ta shia raga.

      Mikel Oyarzabal na Spain ya zura kwallo ta biyu a ragar kungiyarsa

      Asalin hoton, Getty Images

    6. Moteb Al-Harbi da Mohammed Al-Owais na Saudiyya sun yi bakin ciki

      Asalin hoton, Reuters

    7. , Spain 1-0 Saudi Arabia

      Mikel Oyarzabal ya gwada sa'a daga nesa, Sifaniya so take ta kara na biyu daga wankin hula ya kaita dare.

    8. , Spain 1-0 Saudi Arabia

      Watakila a ci Saudiyya kwallaye da yawa domin ta bar bayan ba yan wasa da yawa, kuma Sofaniya ta kai kora amma ba wani hadari, kwallon ya fita.

    9. GOAL - Spain 1-0 Saudi Arabia, Lamine Yamal

      Kwallo ce daga gefen hagu aka sharo ta cikin gidan Saudiya sai Yamal ya yi sauri ya buga daga turken ragar hagu, kuma haka ta fada raga cikin ruwan sanyi.

      Lamine Yamal na Spain ya ci kwallo ta farko a ragar kungiyarsa

      Asalin hoton, Getty Images

    10. , Spain 0-0 Saudi Arabia

      An kwaso kwana kai tsaye zuwa wajen Olmo, bai bata lokaci ba ya buga amma ta yi sama da yawa. Yamal ne ya buga masa kwallon.

    11. Lamine Yamal na Spain da Salem Aldawsari # 10 na Saudi Arabia suna fafatawa don kwallon

      Asalin hoton, Getty Images

    12. , Spain 0-0 Saudi Arabia

      Sifaniya na kokarin cin kwallo tunda wuri, Yamal ya samu dama daga wajen gidan Saudiyya ya buga ta yi sama da yawa.

    13. , Spain 0-0 Saudi Arabia

      Ana yawan kuwwa duk lokacin da Yamal ya dauki kwallo a filin wasa na Atlanta daga gefen hagu.

    14. An fara wasan...

      Sifaniya ce ta fara wasan da za a yi minti 45 daga nan suje hutu, kafin nan akwai hutun shan ruwa da zarar an haura minti 20 da take leda.

    15. Magoya bayan Spain suna taya tawagar su murna

      Asalin hoton, Getty Images

    16. , Spain v Saudi Arabia

      An gama taken kasashen biyu, yan wasa na gaisawa a tsakaninsu, ana daf da take leda.

    17. , Spain v Saudi Arabia

      Sifaniya ta ƙare wasa biyu na ƙarshe a gasar kofin duniya babu ci, amma ba ta taɓa yin wasa uku a jere ba tare da zura ƙwallo ba a raga a gasar.

      Tun daga lokacin da suka zura ƙwallo a minti na 11 a kan Japan a wasan rukuni na uku a gasar 2022, ƴan wasan Sifaniya sun raba kwallo sau 2,500 tare da kai hare-hare 49, amma ba tare da cin ƙwallo ba.

      Sifaniya

      Asalin hoton, Getty Images

    18. , Spain v Saudi Arabia

      Atlanta

      Asalin hoton, Getty Images

      Saudiyya

      Asalin hoton, Getty Images

      Sifaniya

      Asalin hoton, Getty Images

      Sifaniya

      Asalin hoton, Getty Images

    19. Saudiyya na fatan maimaita tarihin Saeed al-Owairan, Spain v Saudi Arabia

      Saudiyya ta yi rashin nasara a wasa 10 daga cikin 11 da ta buga a gasar cin kofin duniya da ta fuskanci tawagogi daga nahiyar Turai, amma ba za ta taba mantawa da lokacin da ta yi nasara a kan wata kasa daga Turai ba.

      Nasarar ita ce doke Belgium da ci 1-0 a USA 94 za a tuna da wasan har abada, saboda kwallo mai ban mamaki da Saeed Al-Owairan ya ce, wanda tun daga mita 69 ya fara yanka har sai da ya dangana da raga.

      Yana daga cikin kwallon da aka ci mai ban mamaki.

      Saudiyya

      Asalin hoton, Getty Images

    20. Oyazabal bai yi kokari ba a wasan Cape Verde, Spain 0-0 Saudiyya

      Dan wasan Sifaniya, Mikel Oyarzabal — wanda ya ci kwallon da ta ba kasar nasara a wasan karshe a Euro 2024 a kan Ingila — bai taɓa kwallo ba a mintuna 30 na farko a wasan da suka tashi 0-0 da Cape Verde.

      Masu kididdiga a Opta sun ce ba su da wani misali makamancin haka a wasan kofin duniya tun daga shekarar 1966.

      Daga baya, Oyarzabal ya yi kokarin neman raga sau biyar, amma ya kasa samun hanyar cin mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha.

      Shin ko zai yi tasiri a wasan yau?

      Oyarzabal

      Asalin hoton, Getty Images