Gwamnatin jihar Kano ta yaba da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Abuja ta yanke game da shari'ar masarautar Kano da ta shafi Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II.
Da yake jawabi ga manema labarai a ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya reshen jihar Kano a ranar Asabar, babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan shari'a, Barista Haruna Dederi, ya yaba da hukuncin a matsayin babban nasara ga ɓangaren shari'a.
Ya ce, "Hukuncin ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya kuma ya tabbatar da matakin da gwamnati ta ɗauka game da naɗin sarauta da gyara a cibiyoyin gargajiya na jihar."
Barista Dederi ya kara jaddada cewa hukuncin ya fayyace hukunce-hukuncen da suka shafi masarautu, inda ya bayyana iyakokin tsarin mulki na kotuna a cikin irin wannan lamari.
"Wannan hukuncin ya sake jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da adalci da gaskiya da kuma bin ƙa'idojin zamani wajen sabunta tsarin masarautu tare da kiyaye al'adun jihar Kano," inji Barista Dederi.
Ya ƙara da cewa, "Don kaucewa shakku, kotun daukaka kara ta yi watsi da duk wani hukunci da sanarwa, da umarnin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke.
"Bugu da ƙari, dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa da ta shafi masarautu, tare da duk wani mataki da mai girma Gwamnan Jihar Kano ya ɗauka bisa ga waccan dokar, kotun daukaka ƙarar ta amince da ita kuma ta halasta ta."
Barista Dederi ya buƙaci duka ɓangarorin da hukuncin ya shafa da su mutunta hukuncin kotun.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta bayar da sabon hukunci a kan bambarwar da ta biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka a shekarar da ta gabata bisa ga dokar masarautar Kano ta 2024, inda ɓangarorin da ke jayayya suka garzaya kotu, suka kuma samo hukunce-hukuncen da suka yi karo da juna.