Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/01/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/01/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Lebanon da Syria za su ƙulla yarjejeniyar tsare iyakokinsu

    Najib Mikati

    Asalin hoton, AFP

    Firaministan Lebanon wanda ke ziyara a Syria ya ce ƙasashen biyu za su yi aiki tare don tabbatar da tsaron iyakokinsu.

    Najib Mikati na magana ne a wani taron manema labarai a Damascus tare da sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa.

    Wannan dai ita ce ziyarar aiki ta farko a hukumance da wani shugaban Lebanon ya kai ƙasar Syria tun bayan barkewar yaƙin basasar ƙasar a shekara ta 2011.

    A baya-bayan nan dai an sake samun ɓullowar takun saƙa tsakanin maƙwabtan biyu.

    A makon da ya gabata Syria ta sanya sabbin takunkumai kan shigar ƴan ƙasar Lebanon bayan wata tarzomar da ta taso a kan iyakar kasar.

    Hezbollah, wadda ke da hedkwata a Lebanon, ta goyi bayan gwamnatin Bashar al-Assad a lokacin yaƙin basasar Syria.

  2. Mummunar guguwa ta afkawa arewacin Madagascar

    Wata mummunar guguwar da aka yi wa laƙabi da 'Dikeledi' ta afkawa arewacin ƙasar Madagaska, lamarin da ya haifar da bala'in ambaliya.

    Masu hasashe sun yi gargadin yiwuwar samun zaftarewar ƙasa, lamariin da ya sanya aka rufe hanyoyi tare kuma da tura sojoji.

    Ana sa ran yankin Mayotte da ke maƙwabtaka da ƙasar wanda kuma ta ke ƙarƙashin ikon Faransa zai bayar da sanarwar gargaɗi nan gaba a ranar Asabar, gabanin isowar guguwar.

    A watan da ya gabata guguwar Chido ta afkawa tsibirin, inda ta shafe wasu garuruwa tare da kashe mutane da dama.

  3. Harin jirgin yaƙi ya rutsa da mutanen gari a jihar Zamfara

    Zamfara

    Asalin hoton, Others

    An samu rahotanni cewa ana ta ƙoƙarin kawar da gawarwaki, da kuma waɗanda suka tsira da munanan raunuka a garin Tungar Kara na yankin ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, bayan da wani jirgin sama da ake zargin na sojoji ne ya kai ya yi kuren barin wuta kan wasu ƴan sa kai da jama'ar gari a yammacin Asabar.

    An ce lamarin ya auku ne, yayin da ake ƙoƙarin daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai garin, suna ƙoƙarin kore wasu dabbobi.

    Wani mutum, wanda ya rasa ɗan yayansa a wannan hari, ya bayyana cewa ƴan sa kai da dama ne lamarin ya rutsa da su yayin da suke yunƙurin tunkarar ƴan bindigan da aka ce suna ɓarna a yankin, inda ya kara da cewa ƴan bingidan sun riga sun bar yankin a lokacin da jirgin ya fara ɓarin wuta..

    Ya ce: ''Muna zaune sai muka ga jirgi ya nufi wuraren da aka ce ƴan bindigan suke, amma ko a lokacin sun riga wuce. Waɗannan yaran da da mutanen da ke ƙasa ne wannan jirgin yake ta harbi, yanzu haka ga ɗan yaya na an kawo mun shi a mace.''

    Ya ƙara da cewa aƙalla mutane 20 ne suka mutu sakamakon wannan hari.

    jami'in watsa labarai na rundunar operation Fansar Yamma da ke gudanar da ayyukan tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi, inda ya ce zai bincika ya tuntuɓe mu. Haka shi ma mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya shaida mana.

    Sai dai kuma wata majiyar gwamnatin jihar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya tabbatar wa BBC aukuwar wannan lamari, amma bai yi wani cikakken bayani ba.

  4. Gobarar Los Angeles ta laƙume gidaje 12,000

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gobarar daji da ta tashi a yankin Los Angeles a yanzu ta lalata gine-gine kimanin dubu goma sha biyu tare da tilasta kwashe mutane sama da dubu ɗari da arba'in.

    A yayin da jami’an ƙashe gobara ke ƙoƙarin shawo kan gobarar, masu hasashe sun ce dawowar iska mai karfi a ranakun Asabar da Lahadi na iya ƙara rura wutar, a yankin da ba aka shafe watanni takwas ba a samu ruwan sama ba.

    Aƙalla mutane goma sha ɗaya aka sani sun mutu tun bayan da gobarar ta tashi a ranar Talata.

    Tun da farko hukumar kashe gobara ta Los Angeles ta musanta rahotannin da ke cewa an kori shugabanta Kristin Crowley, bayan ta soki magajin garin birnin kan ƙarancin ma'aikata da kayan aiki.

  5. Gwamnatin Kano na son a bi umarnin kotu kan rikicin masarauta

    ...

    Asalin hoton, Others

    Gwamnatin jihar Kano ta yaba da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta a Abuja ta yanke game da shari'ar masarautar Kano da ta shafi Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II.

    Da yake jawabi ga manema labarai a ƙungiyar ƴan jarida ta Najeriya reshen jihar Kano a ranar Asabar, babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan shari'a, Barista Haruna Dederi, ya yaba da hukuncin a matsayin babban nasara ga ɓangaren shari'a.

    Ya ce, "Hukuncin ya soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a baya kuma ya tabbatar da matakin da gwamnati ta ɗauka game da naɗin sarauta da gyara a cibiyoyin gargajiya na jihar."

    Barista Dederi ya kara jaddada cewa hukuncin ya fayyace hukunce-hukuncen da suka shafi masarautu, inda ya bayyana iyakokin tsarin mulki na kotuna a cikin irin wannan lamari.

    "Wannan hukuncin ya sake jaddada ƙudirin gwamnati na tabbatar da adalci da gaskiya da kuma bin ƙa'idojin zamani wajen sabunta tsarin masarautu tare da kiyaye al'adun jihar Kano," inji Barista Dederi.

    Ya ƙara da cewa, "Don kaucewa shakku, kotun daukaka kara ta yi watsi da duk wani hukunci da sanarwa, da umarnin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke.

    "Bugu da ƙari, dokar da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa da ta shafi masarautu, tare da duk wani mataki da mai girma Gwamnan Jihar Kano ya ɗauka bisa ga waccan dokar, kotun daukaka ƙarar ta amince da ita kuma ta halasta ta."

    Barista Dederi ya buƙaci duka ɓangarorin da hukuncin ya shafa da su mutunta hukuncin kotun.

    A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja ta bayar da sabon hukunci a kan bambarwar da ta biyo bayan matakin da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka a shekarar da ta gabata bisa ga dokar masarautar Kano ta 2024, inda ɓangarorin da ke jayayya suka garzaya kotu, suka kuma samo hukunce-hukuncen da suka yi karo da juna.

  6. Isra'ila ta kashe mutum takwas a arewacin Gaza - Hamas

    Hukumomin Hamas a Gaza sun ce wani hari da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a wata tsohuwar makaranta a garin Jabalia da ke arewacin ƙasar, ya kashe mutane takwas ciki har da ƙananan yara biyu.

    An bayyana cewa makarantar Halwa tana ɗauke da dubban mutanen da suka rasa matsugunansu. Rundunar sojin Isra'ila dai ta ce ta kai hari ne kan wata cibiyar bayar da umarni na Hamasa da ke yankin.

    Harin dai shi ne na baya bayan nan a jerin hare-haren da aka kai kan gine-ginen makarantu da ke ɗauke da ƴan gudun hijira a Gaza. Isra'ila ta sha nanata cewa Hamas na amfani da irin waɗannan wuraren wajen kai hare-hare kan dakarunta - zargin da ƙungiyar ta musanta.

  7. Sojojin Sudan sun fatattaki dakarun RSF daga Wad Madani

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Sudan sun ce sun ƙwace birnin Wad Madani daga hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF).

    Wasu masu sharhi sun bayyana hakan a matsayin nasara mafi girma da sojoji suka samu a kusan shekaru biyu na yaƙin basasan da ake gwabzawa a ƙasar.

    Babban birnin jihar, Al jazira, wanda ita ce cibiyar aikin gona na gabashin Sudan, ya shafe fiye da shekara guda yana ƙarƙashin ikon ƙungiyar RSF.

    Hotuna a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jama'a ke murna a kan titunan garin.

    Yaƙin basasa a Sudan ya haifar da abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira yunwa mafi muni a duniya.

    Dubun mutane ne aka kashe yayin da sama da miliyan goma sha ɗaya suka rasa matsugunansu, sakamakon yaƙin.

  8. Jami'an tsaro sun daƙile wani hari kan ƴan shi'a a Damascus

    Syria's intelligence service says it's foiled an attempt by the Islamic State group to blow up a Shiite shrine in Damascus.

    Hukumar leƙen asirin Syria ta ce ta dakile wani yunƙurin da ƙungiyar IS ta yi na tarwatsa wurin ibadar ƴan Shi'a a Damascus.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an kama wasu mayakan masu iƙirarin jihadi kafin su kai harin a wurin ibadar da ke Sayeda Zinab.

    Duk da yake ƙungiyar ta IS ta rasa yanki na ƙarshe da ta ke iko da ita a Siriya kusan shekaru shida da suka gabata, akwai ƴan tsirarun ƙungiyar da ke ci gaba da kasancewa a ƙasar.

  9. Mun kama sojojin Koriya ta Arewa a Rasha - Zelensky

    ...

    Asalin hoton, @ZelenskyyUa/X

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa, sojojin ƙasar Ukraine sun kama wasu sojojin Koriya ta arewa biyu da suka jikkata a matsayin fursunonin yaki a yankin Kursk na ƙasar Rasha.

    Mutanen biyu suna samun kula a asibiti kuma suna hannun Hukumar Tsaro ta Ukraine (SBU) a birin Kyiv, a cewar Zelensky.

    Shugaban ya ce yana godiya ga sojojin Ukraine da dakarun soji na musamman da suka kama ƴan Koriya ta Arewan.

    Ya ƙara da cewa "wannan ba abu ne mai sauki ba", yana mai cewa sojojin Rasha da Koriya ta Arewa sukan kashe ƴan Koriya ta Arewa da suka samu raunuka "don shafe duk wata shaida da ke nuna cewa Koriya ta Arewa na da hannu a yaƙin da ake yi da Ukraine".

    "Duniya na buƙatar sanin gaskiya game da abin da ke faruwa." in ji Zelensky

    Zelensky ya kuma wallafa hotunan wasu mutane biyu da suka jikkata amma bai bayar da shaidar cewa su Koriya ta Arewa ba ne.

  10. Shugaban Somaliya zai kai ziyarar ban mamaki Ethiopia

    Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, na wata ziyara ta ban mamaki zuwa ƙasar Ethiopia a yau Asabar.

    Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara inganta bayan cimma yarjejeniya a watan da ya gabata, domin taimaka wajen magance rikicin da ke tsakanin ƙasashen.

    Rikicin ya faro ne a lokacin da ƙasar Ethiopia da ba ta da iyaka da ruwa ta cimma yarjejeniya da yankin Somaliland domin samun damar zuwa tekun Maliya.

    An cimma yarjejeniyar ne domin ita Ethiopia ta amince da yankin a matsayin ƙasa mai cin gashin kai.

    A nata ɓangare Somaliya na kallon yankin na Somaliland a matsayin wani ɓangare nata, lamarin da ya sa ta yi watsi da yarjejeniyar, abin da kuma ya janyo taƙaddamar.

  11. Everton ta kammala ɗaukar David Moyes a karo na biyu

    Sabon Kocin Everton

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta kammala ɗaukar David Moyes a matsayin kocin ƙungiyar a karo na biyu.

    Mai shekara 61, ya sanya hannu kan kwantiragin shekara biyu da rabi a Goodison Park, bayan da ƙungiyar ta kori Sean Dyche a ranar Alhamis.

    Yanzu haka Everton na matsayi na 16 a kan teburin Premier, bayan da ta yi nasara sau uku kacal a wasa 19 da ta buga a kakar bana.

    Bayan sanya hannu a ƙungiyar, sabon kocin ɗan asalin Scotland ya alƙawarta mayar da Everton kan ganiyarta musamman a gasar Premier.

    David Moyes ya taɓa horas da Everton daga 2002 zuwa 2013 kafin ya koma Manchester United.

    Sai dai ya raba gari da United bayan wata 10 kacal, inda ya koma Real Sociedad daga bisani ya koma Sunderland sai kuma West Ham.

    Kocin ya kasance ba shi da ƙungiya tun bayan barin West Ham, wadda ya ɗaukar wa kofin Europa Conference League a 2023

  12. Malala Yousafzai za ta ziyarci Pakistan karon farko cikin shekaru

    Malala Yousafzai

    Asalin hoton, Getty Images

    Fitacciyar 'yar gwagwarmayar Ilimi kuma wadda ta taɓa lashe kyautar Nobel, Malala Yousafzai, 'yar asalin Pakistan, za ta ziyarci ƙasarta ta haihuwa a karon farko cikin shekaru.

    Matashiyar mai shekara 27 za ta halarci wani taro na kwana biyu - da zai mayar da hankali kan ilimin yara mata a ƙasashen musulmi.

    An fitar da Malala Yousafzai daga Pakistan a shekarar 2012 bayan da wani ɗan ƙasar na ƙungiyar Taliban ya harbe ta a ka lokacin da take cikin motar ɗaukar ɗalibai.

    Tun daga lokacin sau ƙalilan ta ziyarci ƙasar.

    An gayyaci shugabannin Afghanistan waɗanda 'yan Taliban ne - da ke taƙaita wa mata neman ilimi - zuwa taron, kodayake ba su ce komai ba game da gayyatar.

  13. An yanke wa gidaje da shaguna fiye da 60,000 wutar lantarki a Los Angeles

    Aƙalla gidaje da shagukan 60,000 ne suka kasance babu wutar lantarki a birnin Los Angeles, sakamakon gobarar da ke ci gaba da yi wa yankin barazana.

    Kamfanin da ke bibiyar yanke lantarki a gidaje ya nuna cewa a gundumar LA kaɗai kusan gidaje 32,000 ne aka yanke wa lantarkin, yayin da aka yanke wutar a gidaje fiye da 30,000 a gundumar Edison da ke kudancin California.

    Gobarar da ta ɓarke tun a ranar Talata na ci gaba da yi wa al'mma barazana sakamakon yadda aka kasa kashe ta.

  14. An buƙaci ɗaukar matakan gaggawa saboda ƙaruwar hayaƙi a Los Angeles

    Hukumomi a Los Angeles sun ayyana buƙatar ɗaukar matakan gaggawa kan lafiya a yankin sakamakon yadda gobara ke ci gaba da yi wa yankin barazana.

    Hayaƙi da turirin wutar sun mamaya sararin samaniyar yankin.

    Cikin wata sanarwa da hukumar lafiyar yankin ta fitar, ta shawarci mazana yankunan da hayaƙin ke shawagi su ci gaba da zama a cikin gidajensu tare da rufe tagoginsu don kauce wa mummunan hayaƙin.

  15. Gobarar Los Angeles: An umarci fiye da mutum 144,000 su fice daga gidajensu

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Hukumomi a Los Angeles na Amurka sun buƙaci fiye da mutm 144,000 su bar gidajensu sakamkon gobarar da ke ci gaba da yi wa yankin barazana.

    Cikin wani saƙo da ofishin gwamnan jihar ya wallafa a shafinsa na X, a ce ya tanadi wurare takwas domin tsuganar da mutanen da suka bar gidanjen nasu, kuma a yanzu haka kawai fiye da mutum 700 da tuni ke zaune a wuraren.

    Gobarar da ta shafe kwanaki tana ci ta yi sanadin mutuwar mutum 11 a jihar.

    Iska mai ƙarfi da ake kaɗawa a yankin na kawo cikas ga ƙoƙarin kashe gobarar da jami'ai ke yi.

  16. An zaɓi Sanata Azuta-Mbata shugaban Ohanaeze Ndigbo

    Shugaban

    Asalin hoton, X

    Ƙungiyar cigaban al'ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, ta zaɓi Sanata John Azuta-Mbata a matsayin sabon shugabanta.

    An zaɓi Sanata Azuta-Mbata, tsohon ɗan majalisar dattawa daga jihar Rivers a lokacin taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar da ya gudana a birnin Enugu ranar Juma'a.

    Gwamnonin jihohin yankin kudu maso gabashin ƙasar biyar da shugabannin al'umma da masu ruwa da tsaki daga ƙabilar Igbo ne suka halarci taron zaɓen sabon shugaban.

    Sanata Azuta-Mbata shi ne shugaban ƙungiyar na 13, bayan da ya gaji Fidelis Chukwu ɗan jihar Imo da ya kammala wa'adin mulkinsa.

    Sabon shugaban ya alƙawarta tafiya da kowa wajen gudanar da shugabancinsa, domin haɗa kan 'ya'yan ƙungiyar da kuma ci gaban al'ummar ƙabilar Igbo.

    Shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu maso gabashin Najeriay, Hope Uzodinma ya tabbatar wa ƙungiyar Ohanaeze Ndigbo cewa gwamnonin yankin za su bai wa shugabancin ƙungiyar goyon baya da haɗin kai, domin ciyar da yankin gaba.

    Tuni dai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon taya murna ga sabon shugaban ƙungiyar ta Ohanaeze Ndigbo.

  17. Wata matashiya ta buƙaci a ci gaba da tsare mahaifinta a kurkuku

    'Yar mutumin nan - da aka samu da laifin shirya fyaɗen taron dangi ga matarsa a shari'ar da ta girgiza ƙasar Faransa - ta faɗa wa BBC cewa tana fatan mahaifin nata ya mutu a gidan kaso.

    Caroline Darian ta ce ta kaɗu matuƙa lokacin da ta gano mahaifinta na bugar a mahaifiyarta, Jizel Pelico da ƙwaya, sannan ya gayyato maza su ci zarafinta.

    An samu Dominique Pelicot - da ke zaman kason shekara 25 - da laifin ɗaukar hotunan tsiraicin 'yarsa.

    Ita ma Mis Darian ta yi imanin ya yi mata fyaɗe, amma ya musanta zargin.

    ''Bana ta fatan a sake shi daga kurkuku, saboda mutum ne mai hadarin gaske'', a cewar Pelico - da a yanzu ta daina kiransa 'Baba'.

    A yanzu dai Mis Darian na kokarin wayar da kan mutane kan yadda masu aikata laifi ke amfani da sinadarai domin bugar da su sannan su ci zarafinsu.

  18. INEC ta buƙaci naira biliyan 126 a kasafin kuɗinta na 2025

    shugaban INEC

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya ta yi buƙaci a ware mata naira biliyan 126 a matsayin kuɗin da za ta kashe a shekarar 2025.

    Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Juma'a, a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dokokin ƙasar don kare kasafin kuɗin hukumar na 2024.

    Tun da farko shugaban hukumar ya yi watsi da naira biliyan 40 da aka ware wa hukumarsa a kasafin kuɗin wannan shekara.

    Yana mai danganta hakan da ƙaruwar tsadar abubuwa a Najeriya ciki har da kayayyakin aikin zaɓe.

    ''Zaɓe a Najeriya ya kasance wani babban abu da ke buƙatar wadatattun kuɗi, don haka abin da muke buƙata a wannan shekara ya kai naira biliyan 126, kuma muna da takardun da ke ɗauke da cikakkun bayanan yadda za mu kashe waɗannan kuɗaɗe da muka buƙata'', in ji Farfesa Yakubu.

    Daga cikin ayyukan da ya ce hukumar za ta gudanar a shekarar sun haɗa da cigaba da aikin rajistar masu zaɓe, da shirya zaɓukan wasu jihohin a bana, da sauya wasu kayyakin zaɓen da suka lalace da gyara ofisoshin hukumar da ke wasu ƙanann hukumomi.

    Haka kuma ya ce shekarar 2025, shekara ce mai muhimmanci ga hukumar wajen shirya zaɓukan 2027.

  19. An fara gano bayanan hatsarin jirgin saman Koriya ta Kudu

    jirgi

    Ma'aikatar sufurin Koriya ta Kudu ta ce bayanan da aka samu a akwatin naɗar murya na jirgin fasinjan nan da ya yi hatsari a watan da ya wuce, sun nuna cewa akwatin ya daina aiki mintina huɗu gabannin hatsarin jirgin.

    Ma'aikatar ta ce za a fara bincike kan dalilin daina aikin na'urar naɗar muryar da kuma sauran bayanan da aka rasa.

    Jirgin saman mallakin kamfanin Jeju, ya yi saukar gaggawa da gudun gaske lamarin da ya kai shi ga faɗuwa kan kankaren da ke titin saukar jirgi a filin jirgin sama na Muan daga nan ya kama da wuta.

    Mutum 179 ne suka mutu a lokacin hatsarin jirgin, yayin da ma'aikatan jirgi biyu suka tsira.

    Masu binciken na fatan samun bayanan da za su taimaka sanin dalilin da ya sa jirgin ya yi saukar gaggawa da musabbabin hatsarin.

  20. Putin na cikin tsaka-mai-wuya - Biden

    Putin

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Amurka, Joe Biden ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin na cikin tsaka mai wuya bayan Amurka da Birtaniya sun sanya wa fannin makamashin Rasha sabbin takunkumi kan mamayar Ukraine.

    Mista Biden ya shaida wa manema labarai a Fadar White House ce wa abu ne mai matukar muhimmanci a tabbatar ba a bai wa shugaban na Rasha sararawa ba.

    Shugaban Amurkan ya ce takunkumin da aka sanya wa Rashan, zai girgiza tattalin arzikinta ta yadda zai yi mata wahalar iya ci gaba da yaƙin Ukraine ba.

    Tun da fari ma'aikatar cikin gida a Amurka ta fitar da bayanan yadda takunkuman za su shafi ƙasar, ciki har da jiragen ruwa kusan 180.