China ta tura ɗanjarida gidan yari bisa zargin leƙen asiri

Asalin hoton, Reuters
Wata kotu ta yanke wa wani ɗanjarida a ƙasar China hukuncin zaman gidan kaso na shekara bakwai bisa zarginsa da leƙen asiri, kamar yadda iyalansa suka shaida wa BBC.
Dong Yuyu, mai shekara 62, ya kasance a tsare tun a shekarar 2022, kuma ya kasance fitaccen ɗanjarida a ƙasashen Amurka da Japan, kuma yana yawan ganawa da jakadun ƙasashen waje.
Ƴansanda sun kama shi ne a daidai lokacin da yake ganawa da jakadan ƙasar Japan a birnin Beijing.
Dong na cikin manyan ƴanjarida na kafar Guangming Daily, wadda take ɗaya daga cikin manyan jaridu guda biyar da suke da alaƙa da jam'iyyar gurguzu ta China.
Iyalansa sun bayyana a wata sanarwa cewa, kotun ta ce ma'aikatan ofishin jakadancin Japan da Dong ya gana da su "ƴan leƙen asiri ne.
"Muna mamakin yadda gwamnatin China za ta kira ofishin jakadanci 'masu leƙen asiri," kamar yadda sanarwar iyalan ta nuna.




