Za mu cigaba da yaƙi idan Hezbollah ta saɓa yarjejeniya - Netanyahu
Rahoto kai-tsaye
Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Isiyaku Muhammed da Ahmad Bawage
Asuba ta gari
Nan muka zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Amma za ku iya ziyartar shafin mu na BBCHausa.com domin ci gaba da karanta labarai daban-daban.
Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.
Georgia: Mutane sun bazama kan tituna don adawa da jingine batun shiga Tarayyar Turai
Asalin hoton, Reuters
Dubban
mutane sun sake fita zanga-zanga a Tbilisi, babban birnin Georgia, domin nuna
rashin amincewa da matakin gwamnati na jingine ƙoƙarin shigar ƙasar ƙungiyar Tarayyar Turai har nan da shekara huɗu.
A jiya da dare ma an yi wata zanga-zangar, inda ƴan sanda suka kama gomman mutane
bayan ƙoƙarin tarwatsa su da hayaƙi mai sa hawaye da kuma ruwan zafi.
Masu zanga-zangar sun
tunkari ƴan sanda suna ihu, lamarin da ya janyo aran-gama tsakanin su.
Abin da taurarin Kannywood ke cewa kan Hikayata
Shugaban Hukumar fina-finai ta Najeriya, Ali Nuhu da shugaban Hukumar tace fina-fina ta jihar Kano, Abba El-Mustapha na daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a lokacin bikin Hikayata ta 2024.
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Kashi 16 kaɗai na yara ke zuwa makaranta a Jigawa - Unicef, Daga Zahraddeen Lawan
Asalin hoton, Getty Images
Wani
rahoton asusun kula da kananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF ya
bayyana cewa kashi 16 ne kaɗai cikin yara ke zuwa makaranta a jihar Jigawa.
Gwamnatin
jihar da ɓangaren majalisa da kuma UNICEF sun amince da wani tsari da zai
taimaka wajen tabbatar da cewa yaran da suka isa zuwa makarantar firamare da
sakandare sun shiga.
Matsalar
rashin zuwa makaranta wani al’amari ne da ke ci wa al’ummomin nahiyar Afrika
ciki har da Najeriya tuwo a kwarya, duk kuwa da irin hobɓasa da gwamnatoci a
matakai daban-daban ke cewa suna yi wajen magance matsalar da ke yi wa yara
tarnakin zuwa makarantar.
Rahoton wanda aka fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa kashi 44 huɗu na yaran da suka isa zuwa makarantun firamare da kuma
kashi 52 na waɗanda suka isa zuwa
sakandire ne ba sa zuwa, inda wasu daga cikinsu ke gararamba da kuma tallace-tallace.
Dr Lawan Yunusa Danzomo, kwamishinan ma’aikatar ilimi a matakin farko na jihar, ya ce sun ɓullo da matakai daban-daban na magance matsalar.
"Mun ƙara sabunta makarantu a karkara. Muna tattara shugabanni don sanar da su muhimmancin ilimi a wjaen da yara ba sa zuwa makaranta. Muna kuma ci gaba da aikin gina ƙarin makarantu da gyara wasu da suka lalace," in ji Dr Lawan.
Dr. Danzomo ya kara da cewa sun lura akwai wasu matsaloli da suke hana yaran
zuwa makaranta ciki har wasu al’adu.
Ya ce cikin abubuwan da suka janyo wasu yaran ba sa zuwa makaranta sun haɗa da talauci da rashin wadata da zai sa wasu sai sun yi tallace-tallace domin samun na kai wa baka, da kuma matsin tattalin arziki da ƙasa ke ciki.
Gwamnati da tallafin asusun na UNICEF sun yi wa shugabannin jihar kaimi, inda
yayin wani zama da ɓangaren majalisa suka amince su rika tallafawa yara masa
galihu.
Kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Haruna Aliyu ya ce bayan ganawa da UNICEF, ya raba wa yara 8,000 littafai da kuma abin rubutu.
Gwamnatin jihar ta kafa hukumar kula da makarantun tsangaya, inda za a
tattaro yara al’majirai da marasa galihu a mayar da su makaranta su ci gaba da
karatu, sannan kuma an samar da wani tsari mai taken "mathers association" wanda
zai rika jawo hankalin iyaye mata su rika tabbatar da cewa ‘ya’yansu suna zuwa
makarnta a kan lokaci.
Labarai da dumi-dumi, Leicester ta naɗa Ruud van Nistelrooy sabon kocinta
Asalin hoton, Getty Images
Leicester City ta naɗa Ruud van Nistelrooy a matsayin sabon kocin ƙungiyar.
Van Nistelrooy ɗan asalin Netherland zai maye gurbin Steve Cooper, wanda aka kora a makon da ya gabata bayan jan ragamar ƙungiyar a wasanni 12 na gasar Firimiya ta bana.
Ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekara uku wadda za ta kai har watan Yunin 2027.
Naɗin Ruud na zuwa ne makonni biyu bayan da ya bar muƙaminsa na kocin rikon ƙungiyar Manchester United.
Mutanen da suka mutu a zaftarewar laka a Uganda ya kai 20
Asalin hoton, Uganda Red Cross Society
Yawan mutanen da aka tabbatar sun mutu
a zaftarewar laka a gabashin
Uganda ya kai 20,a cewar hukumomoin ƙasar.
Sun ce ana can ana ci gaba da
aikin ceto.
Zaftarewar ƙasar
ta faru ne a yankin Bulambuli a ranar Laraba, inda hukumomi suka ce har yanzu
akwai mutane fiye da 100 da ake nema.
Rundunar sojin Uganda ta ce tana ci
gaba da ƙoƙarin
gano mutanen, yayin da gwamnati ke ƙara kira da a tashi daga yankin.
Rodri, Vinicius, Yamal da Messi na cikin masu neman gwarzon ɗan wasan Fifa
Yan wasan da dama ne sunayensu suka shiga jerin waɗanda za su fafata wajen lashe kyautar ƴan wasan Fifa na 2024.
Jr Vinicius da ƴan wasan Manchester City Haaland da Rodri da ya lashe Ballon dOr suna cikin jerin sunayen.
Ƴan wasan City biyun sun shiga cikin jerin ne saboda nasarar da ƙungiyarsu ta samu na lashe Premier a bana sau hudu a jere.
Ɗan wasan Real Madrid da Ingila Jude Bellingham na daga cikin 'yan wasa 11 d za su iya cin kyautar, waɗanda ke taka leda a Spain.
Lionel Messi, wanda ya lashe kyautar a 2023, shi ɗaya ne ɗan wasan da ke cikin jerin sunayen waɗanda ke taka leda a wajen Turai.
Rodri da ya lashe Ballon d'Or shi ke kan gaba a neman lashe kyautar amma yana fuskantar gogayya daga ɗan wasan Real Madrid Vinicius Jr, wanda ya yi na biyu a zaɓen da aka yi a Oktoba.
Ku San Malamanku tare da Gwana Aisha Gwani Yahuza Ɗanzarga
Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama don ku kalli bidiyo:
Aisha Yahuza Ɗanzarga - wadda ake yi wa laƙabi da Maraƙisiyya - na ɗaya daga cikin mata da aka fara naɗawa a matsayin gwanayen Alƙur'ani a ƙasar Hausa.
Mahaifinta Gwani Yahuza Danzarga shahararren malamin Ƙur'ani ne a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kuma shi ne ya naɗa ta gwana.
Ta taɓa wakiltar Najeriya a musabaƙar Ƙur'ani ta duniya da aka yi a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (Dubai), inda ta zo ta biyu a ajin hizifi 60.
Haifaffiyar birnin Kano ce kuma a nan ta yi karatun littafin mai tsarki da na zamani.
Gwamnatin Katsina ta kulla yarjejeniyar haƙar ma'adinai ta biliyoyin naira
Asalin hoton, Dikko Umaru Radda/X
Gwamnatin Katsina ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar haƙar ma'adinai a faɗin jihar da kamfanin Geoscan na ƙasar Jamus.
Shugaban hukumar haƙar ma'dinai ta jihar Katsina, Umar Abbas Dangi ne ya bayyana haka yayin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tare da wakilan kamfanin Geoscan a Berlin.
Abbas wanda ya wakilci gwamna Dikko Umaru Radda, ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen samarwa jihar kuɗaɗen shiga da kuma ayyukan yi.
Ya ƙara da cewa ganin kwarewar Geoscan wajen aikin haƙar ma'adinai a Najeriya, ya janyo suka kulla yarjejeniyar.
"Kamfanin ya kware wajen haƙar ma'adinai yadda ya dace ba tare da yin wani mummunan tasiri kan muhalli ba," in ji Umar Dangi.
Sun yaba wa gwamna Radda da wannan yunkuri da ya yi wajen ganin ɗorewa da kuma bunƙasar ɓangaren haƙar ma'adinai.
NYSC ta sake buɗe sansanin horaswa na Zamfara bayan wata 16
Asalin hoton, X/NYSC
Bayanan hoto, Duk shekara dubban matasa da suka kammala karatun digiri ne ke zuwa jihohin Najeriya domin yi wa ƙasa hidima
Hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya (NYSC) ta sake bude sansanin horaswa na jihar Zamfara, bayan rufe shi na wata 16 saboda dalilai na tsaro.
Yayin taron budewar da ya gudana a sansanin na wucin gadi da ke Gusau, an kuma rantsar da sabbin 'yan hidimar ƙasa na rukunin Batch C Stream 1.
Yanzu haka gwamnatin jihar na aikin sake gina sansanin horarwar na dindindin da ke karamar hukumar Tsafe.
Kulle sansanin da aka yi a shekarar 2023 ya janyo tsaiko ga matasan masu hidimar kasa da aka tura jihar, wadanda daga baya aka tura wasu jihohi kamar Kebbi mai maƙwabtaka.
Rashin kai matasan Zamfara na da nasaba da hare-haren da 'yanfashin daji ke kaiwa kusan a kullum, inda suke garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Harin Isra'ila ya kashe shugaban sashen bayar da kulawa ta musamman na asibitin Gaza
Asalin hoton, Press Association
Likitoci Falasɗinawa sun ce shugaban sashen bayar da kulawa ta musamman a wani asibitin Gaza ya mutu, bayan wani harin rokar Isra'ila ya faɗa asibitin.
Hukumomi a asibitin Kamal-Adwan sun ce Dakta Ahmed Al-Kahlout yana tafiya a kusa da ƙofar shiga asibitin ne, lokacin da harin rokar ya faɗa masa, kuma nan take ya rasu.
Fiye da wata biyu kenan dakarun Isra'ila suna kai hari yankin.
Asibitin yana daga cikin ƴan tsirarun da suka rage, amma kuma yana fama da ƙarancin kayan aiki da magunguna.
'Yan majalisa Birtaniya sun goyi bayan ƙudirin dokar taimaka wa marasa lafiya su mutu
Asalin hoton, AF archive / Alamy
'Yan majalisar dokokin Birtaniya sun goyi bayan daftarin ƙudirin da zai halasta taimaka wa marasa lafiya da ke cikin tsanani su mutu.
Ƙudirin dokar zai bai wa mutanen da ke da sauran ƙasa da wata shida a rayuwa su yanke hukuncin ko suna so a kashe kansu.
Wannan tanadin dokar zai zamo mai matuƙar wuyar aiwatarwa saboda dole ne sai an samu likitoci biyu da za su tabbatar cewa mutum yana da sauran ƙasa da wata biyu a rayuwarsa ta duniya.
Ƴar majalisar da ta gabatar da ƙudirin, Kim Leadbeater ta ce burin nata, wata hanya ce ta bai wa mutane damar mutuwa cikin mutunci.
Ƴansandan a Kano sun kuɓutar da ƴar shekara huɗu daga hannun masu garkuwa
Asalin hoton, Abdullahi Haruna Kiyawa/Facebook
Rundunar 'yansandan jihar Kano ta kuɓutar da wata ƙaramar yarinya mai shekara huɗu daga hannun masu garkuwa da mutane tare da kama wanda ake zargi da sace yarinyar.
Cikin wani saƙo jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a ranar Talata jami'an 'yansanda suka kama wani matashi mai suna Saifullahi Abba, mai shekara 23, bisa zargin garkuwa da yarinyar.
Tun da farko mahaifin yarinyar ne mai suna Zilkiflu Abdullahi da ke zaune a ƙauyen Dakatsalle a yankin ƙaramar hukumar Bebeji ya kai wa 'yansanda ƙorafin sace 'yar tasa mai suna Nabila a ranar 22 ga watan Nuwamban da muke ciki.
''Kwana guda bayan haka kuma sai wani mutum ya kira shi tare da iƙirarin sace 'yar tasa, sannan ya buƙaci naira miliyan uku a matsayin kuɗin fansa'', kamar yadda SP Kiyawa ya bayyana.
'Yansandan sun ce sun kama wanda suke zargi da sace yarinyar - wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar Wudil ne - a ƙauyen Luran da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
''Wanda ake zargin ya amince da laifin da aka tuhume shi, sannan ya jagoranci jami'an 'yansanda zuwa inda ya ɓoye yarinyar a ƙauyen na Luran, inda nan take aka kuɓutar da ita,''Kamar yadda kakakin 'yansandan jihar Kanon ya bayyana.
Faransa ta buƙaci a kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Asalin hoton, Reuters
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noel Barrot ya yi kira ga ɓangarori biyun da ke yaƙi da juna a Sudan su ajiye makamai domin kawo ƙarshen yaƙin da suka daɗe suna gwabzawa.
Mista Barrot na wannan kiran ne a lokacin da ya kai ziyara wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Adre a ƙasar Chadi, wanda ke kusa da kan iyakar Sudan.
A game da zargin ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da tallafa wa dakarun RSF da makamai, ta hanyar amfani da Chadi a matsayin mahaɗa, ministan harkokin wajen Chadi, Abderaman
Koulamallah ya ce babu ruwansu a yaƙin kuma ba sa goyon bayan kowane ɓangare tsakanin sojojin Sudan ɗin da dakarun RSF.
Mista Barrot ya kuma yi kira ga hukumomin Sudan su bar kan iyakar Adre a buɗe domin samun damar shigar da kayayyakin agaji, sannan ya yi kira ga dakarun RSF su guji ƙwacewa tare da karkatar da kayayyakin agajin da aka kawo domin waɗanda suke fuskantar ƙuncin rayuwa a sanadiyar yaƙin.
Ministan ya kuma yi alƙawarin ƙarin fam miliyan bakwai domin taimakon ayyukan jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya domin yaƙi da kwalara da tallafa wa mata.
An sake zaɓar Okonjo-Iweala shugabar WTO a wa'adi na biyu
Asalin hoton, Ngozi Okonjo-Iweala/X
Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO ta sake zaɓar Dakta Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabanta a wa'adin mulki na biyu, inda za ta ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa 2029.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin cinikayyar duniya ke cikin wani mawuyacin yanayi.
A farkon makon nan zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai ƙaƙaba sabbin haraje-harajen cinikayya da ƙasashen Canada da Mexico da China idan ya kama aiki cikin watan Janairu.
A lokacin wa'adin mulkinsa na farko, Donald Trump ya yi yunƙurin hana Ms Okonjo-Iweala samun matsayin, inda ta samu nasarar ɗarewa muƙamin bayan Joe Biden ya zama shugaban Amurka.
Babban abin tambaya a yanzu shi ne irin tasirin da ƙungiyoyin kasuwanci irin WTO za su yi, a daidai lokacin da manyan ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki ke ƙara samun saɓanin kasuwanci.
Ga kuma batun yaƙin Ukraine da ya haifar da ƙarin takunkuman kasuwancin tsakanin wasu manyan ƙasashe.
Asalin hoton, Ngozi Okonjo-Iweala/X
Nahcon ta mayar wa alhazan Najeriya naira biliyan 5.3 saboda rashin kulawa a aikin hajji
Asalin hoton, Nahcon/ Facebook
Hukumar alhazan Najeriya ta mayar da hukumomin alhazai na jihohin da ba su samu cikakkiyar kulawar hukumar ba lokacin aikin hajjin da ya gabata na 2023.
Cikin wani saƙo da Nahcon ɗin ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce kuɗin wanda ya kai naira biliyan 5.3, ta ce ta mayar wa hukumomin alhazai na jihohin da kamfanonin shirya tafiye-tafiyen da ba su samu kulawar da ta dace ba a lokacin aikin hajjin da ya gabata.
Wasu jihohin ƙasar da ma kamfanonin shirya tafiye-tafiye sun bayyana ƙorafe-ƙorafensu bayan kammala aikin hajin kan abin da suka kira rashin ingancin aiki da rashin kulawa daga hukumar alhazai ta ƙasar.
Inda wasu da dama suka zargi hukumar alhazan ƙasar da karkatar da wani ɓangare na kuɗaɗen tallafin aikin hajji da gwamnatin tarayya ta bayar, wani abu da wasu ke alaƙanta wa da korar tsohon shugaban hukumar alhazan ƙasar, Malam Jalal Ahmad Arabi.
'Ilimi ne zai magance matsalar tsaro a arewacin Najeriya'
Asalin hoton, NPF
Ɗanmajalisar wakilai mai wakiltar Bunguɗu da Maru a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya Honarabul Abdulmalik Zubairu Zanna ya ce hanya ɗaya yake ganin za a bi domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi yankin da yake wakilta da jiharsa baki ɗaya.
Honarabil Zanna ya ce matuƙar za a ilimantar da matasan jihar Zamfara yadda ya kamata, to matsalar tsaro za ta zama tarihi a kusa.
Ndume ya sa alamar tambaya kan gaggawar amincewa da ƙudurin haraji na Tinubu
Asalin hoton, OTHER
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta kudu ya ɗiga alamar tambaya kan yadda ake gaggawa domin amincewa da ƙudurin harajin da shugaban ƙasa Tinubu ya aika majalisa.
Ndume ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirin Politics Today.
Sanatan ya ce a zaɓen 2023, sanatoci 25 ne kawai suka dawo, wanda hakan a cewarsa ke nuna cewa mutane sun fara daina amince da su.
Ya ƙara da cewa yadda ake gaggawar amincewa da ƙudurin na harajin, ya nuna kamar akwai lauje cikin naɗi.
"Ba wai ina da matsala da ƙudurin ba ne, kuma ba wai ina cewa a yi watsi da shi ba ne baki ɗaya, amma tunda gwamnoninmu waɗanda su ne jagororinmu da kuma majalisar tattalin arziki da wasu ɗaiɗaikun mutane sun bayyana cewa akwai buƙatar ƙarin lokaci domin a tattauna, ya kamata a ɗan ƙara lokaci. Me ya sa ake gaggawa?" in ji shi.
Ndume ya ce babbar matsalarsa da ƙudurin ita ce lokacin da aka bijiro da ita, inda a cewarsa bai kamata a ce an kawo maganar ƙudurin ba a daidai wannan lokacin da ƴan Najeriya suke cikin ƙuncin rayuwa.
"Tun kakanninmu uuna biyan haraji a arewa. Don haka ba wai muna tsoron biyan haraji ba ne, duk wani ɗan ƙasa na ƙwarai zai biya haraji, amma gaskiya zuwa da wannan maganar a wannan lokacin bai dace ba," in ji shi.
An kama ɗan Najeriya a Amurka bisa zargin damfara
Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta kama Oluyomi Omobolanle Bombata, wadda aka fi sani da ‘Bobo Chicago,’ bisa zargin damfara.
An kama matashin ne bisa zarginsa da hannu wajen damfarar kusan dala miliyan 3 ta internet da kuma badaƙalar kuɗade.
Rahotanni sun bayyana cewa matashin mai shekara 25 ya damfari ƴan Najeriya da dama a unguwar Houston da sauran wasu wurare kafin ya gudu zuwa Chicago, inda aka kama shi.
Kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 200 ya kife a Neja
Asalin hoton, OTHER
A safiyar yau Juma'a ce aka wayi gari da kifewar wani kwale-kwale a sashen Dambo-Ebuchi na tekun Neja, wanda ya yi sanadiyar wasu mutane.
Waɗanda lamarin ya auku a gaban su sun shaida wa tashar Channels cewa, kwale-kwalen, wanda na wani mai suna Musa Dangana ne, yana tafe ne da fasinjoji sama da 200, ciki har da mata ƴankasuwa da masu aikin gona waɗanda za su tafi kasuwar mako-mako ta Katcha.
A watan Oktoba ne aka samu kwatankwacin hatsarin nan a kwale-kwale a rafin Muwo Gbajibo da ƙaramar hukumar Mokwa na jihar ta Neja, inda mutane da dama suka rasu.