Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 31/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 31 ga watan Maris, 2026.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Haruna Kakangi

  1. El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna bayan makokin mahaifiyarsa

    ....

    Asalin hoton, Mal. Imran U.Wakili (PULLO)/X

    Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhume-tuhume da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa.

    An gurfanar da El-rufai ne kan zargin laifuka da suka haɗa da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida ba, damfara, da bai wa wasu dama fiye da yadda ya dace, da kuma wasu tuhume-tuhume da suka shafi kudade.

    El-Rufai ya bayyana a kotun ne bayan ICPC ta sake shi daga tsare shin da tayi na fiye wata guda, wanda hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai, a Cairo, Masar..

    Bayan kammala gurfanar da shi babbar kotun jihar, za a kai El-Rufai Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda za a fara sauraron buƙatar belinsa da ya shigar.

    Ana sa ran cewa za a duba batun belinsa cikin gaggawa, saboda irin nauyin tuhumomin da ake masa.

  2. Mece ce makomar Kwankwasiyya bayan sauya sheƙar Kwankwaso?

    ...

    Asalin hoton, Saifullahi Hassan/FB

    Tun bayan ficewar tsohon jagoran jam'iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwanso daga jam'iyyar, mutanen da ke bibiyar al'amuran siyasa suka fara magana game da makomar tafiyar kwankwasiyya da ya assasa.

    Sauya shekar tasa na zuwa ne watanni bayan ficewar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

    Fitar Abba daga NNPP ya tafi da kaso mafi yawa na magoya bayan tafiyar Kwankwasiyyar zuwa APC, waɗanda har yanzu ke sanya jar hula, wata alama da ake alaƙanta ƴan Kwankwasiyyar.

    Ficewar jagororin tafiyar biyu zai sauya fasalin ƙungiyar siyasar Kwankwasiyyar, wadda tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya kafa tun bayan komawarsa kan karagar mulki tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

  3. 'Iran ne ke da cikakken iko da mashigar Hormuz'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon kwamandan sojin ruwa, Tom Sharpe, ya bayyana cewa ba ya tunanin cewa za a iya buɗe mashigar Hormuz, ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar mai a duniya, ta amfani da karfi kamar yadda Amurka ke barazanar yi ba saboda Iran ne ke da iko kan halin da ake ciki a mashigar.

    Sharpe ya shaida wa BBC cewa, sai Iran ta amince da dakatar da hare-haren da take yi kan jiragen ruwa da ke wucewa amma kuma amfani da karfi "ba zai yi tasiri ba."

    "Iran ne ke da cikakken iko da mashigar Hormuz, wannan abu a fili yake, kuma ina tsammanin za su ci gaba da riƙe wannan iko a gaba," in ji Sharpe, inda ya ƙara da cewa ba ya cikin muradunsu su canza wannan hali ba.

    Ya ƙara da cewa, duk abin da zai faru zai dogara ne ga Iran da irin matakin da za su ɗauka a makonni ko watanni masu zuwa.

  4. Iran na ci gaba da jerin hare-harenta a yankin Gulf

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    A cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, rundunar juyin juya halin Iran ta ci gaba da harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra'ila da ƙasashen Gulf.

    A Dubai, da misalin ƙarfe 4 na safe,an samu gobara sakamakon fashewar jirgi maras matuƙi da aka kakkabo. Lamarin ya faru kusa da wani gida da aka yi watsi da shi a yankin Al Badiya, inda mutane hudu suka ji rauni, in ji Ofishin Kafofin Watsa Labaran Dubai.

    Haka zalika, wani tankin mai dake ɗauke da fam miliyan biyu na mai da daga tashar mai a Dubai ya kama da wuta bayan Iran ta kai hari da jirgi maras matuƙi daga kamar yadda jami’an Hadaddiyar Daular Larabawa suka bayyana.

    A Sharjah, hukumomin gida sun bayyana cewa wani jirgin sama maras matuki ya kai hari kan ginin ofishin kamfanin sadarwa na Thuraya a daren jiya, amma babu wanda ya mutu ko ya ji rauni.

    Kungiyar Tsaro ta Ƙasar Saudiyya ta ce gidaje shida sun lalace bayan fashewar wani jirgin maras matuki da aka kakkaɓo, amma babu wanda ya ji rauni.

    Wannan jerin hare-hare na nuna ci gaba da rikicin da ke ƙara tsananta a yankin Gulf.

  5. Mun 'cimma fiye da rabin manufarmu ta soji' a Iran - Netanyahu

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce, an cimma sama da rabin burinsa na yaki a kan Iran, amma kuma ya ki ya bayyana takamaimai lokacin da za a kawo karshen yakin.

    Jagoran na Isra'ila ya kara da cewa batun sauya gwamnati ba shi ne manufa ba, amma ya bayyana kwarin gwiwar cewa Jamhuriyar ta Musulunci za ta durkushe daga cikin gida.

    Netanyahu ya ce hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kaiwa na raunana shugabancin Iran din, ta hanyar rage karfin kasar na soji da makamai masu linzami da kuma na nukiliyarta.

    Firaministan na Isra'ila na magana ne bayan da Shugaba Trump ya yi barazanar tarwatsa gaba dayan babbar cibiyar fitar da man Iran waje ta tsibirin Kharg, da tashoshin samar da lantarkinta da na samar da ruwa - in har Iran din ba ta gaggauta amincewa da yarjejeniya ba.

    Fadar gwamnatin Amurkar, ta susuntar da maganar cewa kai hari kan cibiyoyi da kayayyakin amfanin jama'a da ba na soji ba, hakan ka iya zama laifin yaki.

  6. Barka da warhaka!

    Muna muku maraba da shigowa shafinmu na labaran kai-tsaye, kan abubuwan da suke faruwa a Iran da Gabas ta Tsakiya da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.