Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya,17/06/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanan al'amuran da ke faruwa a Najeriya da Afirka da sauran sassan duniya na ranar 17/06/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir

  1. 'Jirgin sojojin Najeriya ya kashe ƴan fashin daji sama da 80 a Katsina'

    ...

    Asalin hoton, fb/Nigerian Airforce

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ta kashe sama da ƴan bindiga 80 tare da ƙona babura 45 waɗanda ƴan fashin ke amfani da su a jihar Katsina.

    Wata sanarwa da rundunar sojin sama ta Najeriya ta fitar a yau Litinin, wadda ta samu sa hannun daraktan hulɗa da jama'a da yaɗa labarunta, Edward Gabkwet, ta ce an kai harin ne a wata maɓuyar ƴan bindiga da ke ƙauyen Gidan Kare a ƙaramar hukumar Faskari da ke jihar ta Katsina.

    Katsina na cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar matsalar ƴan fashin daji masu kisa da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

    Sanarwa sojojin ta ce ta kai harin ne ranar Asabar a lokacin da ta samu rahoton cewa ƴan bindiga kimanin 100 sun kai hari a wani ƙauyen da ke da nisan kilomita biyar daga Gidan Kare, inda suka riƙa ƙona gidajen al'umma.

    Ta ƙara da cewa da misalin ƙarfe 9:40 na daren ranar ne jirgin rundunar ya yi ruwan wuta a kan ƴan fashin dajin waɗanda suka taru a kusa da dabar Kuka Shidda, inda bayanai suka tabbatar da cewa an kashe sama da ƴan bindiga 80 da ƙona babura 45.

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Airfoce

    Haka nan sanarwar ta ce an gano cewa ƴan fashin da aka kashen suna da alaƙa ne da "gawurtattun ƴan bindiga Yusuf Yellow da Rabe Imani".

    A watan Oktoban 2023 ne gwamnatin jihar Katsina ta kafa ƙungiyar ƴan sintiri waɗanda ta ce za su taimaka mata a yaƙin da take yi da ƴan fashin daji, waɗanda suka tagayyara al'umma a ƙauyuka tare da hana gudanar da ayyukan noma.

    Cikin tattaunawarsa da BBC a baya-bayan nan, gwamnan jihar, Dikko Radda ya ce a yanzu "matsalar ƴan fashin daji ta taƙaita ne ga wasu ƙananan hukumomi guda takwas" a cikin 37 na jihar.

    Kuma ya bayyana cewa gwamnati na yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan lamarin.

  2. Me rusa Majalisar Yaƙi ta Isra'ila da Netanyahu ya yi ke nufi?

  3. Za a fuskanci zafin rana mai tsanani a wasu yankunan Amurka cikin wanan mako

    Shugaban Amurka Joe Biden

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Amurka Joe Biden

    Hasashen masana yanayi ya nuna cewa yankunan arewa masu gabashin Amurka da gabashin ƙasar Canada za su fuskanci yanayi mai tsananin zafi, wanda zai shafi kimanin mutum miliyan 70 a cikin wannan mako.

    Hukumar yanayi ta Amurka ta ce wannan ne tsananin zafi na farko da za a fuskanta a lokacin zafin wannan shekara a yankin nahiyar Amurka ta Arewa.

    Hasashen ya nuna cewa yanayin zafi zai iya haura maki 40 a ma'auni salshiyas.

    Masana ilimin sararin samaniya sun bayyana cewa wani yanayi ne a can ƙololuwar sama zai haddasa hakan.

    Masana kimiyya dai na ɗaora alhakin tsananin zafi da bala'o'i da ake samu a doron duniya kan sauyin yanayi.

  4. Amurka ta nuna damuwa kan alaƙar da ke tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Fadar gwamnatin Amurka ta nuna damuwa game da danƙon hulɗa da ke ƙara ƙarfi tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa.

    Mai magana da yawun ɓangaren tsaron cikin gida na Amurka, John Kirby ya ce Amurka ta damu ƙwarai da kwararar makaman Koriya ta Arewa zuwa Rasha, waɗanda ake amfani da su wajen yaƙar Ukraine.

    Ya kuma ce akwai damuwa kan cewa sakamakon hakan Rasha za ta iya taimaka wa Koriya ta Arewa, ta yadda za ta ƙara dagula zaman lafiya a yankin ƙasashen Koriya.

    Mista Kirby na wannan bayani ne gabanin ziyarar kwana biyu da ake sa ran shugaban Rasha, Vladimir Putin zai yi a Koriya ta Arewa, daga gobe Talata.

    A bara ne shugaban Koriya ta Arewar, Kim Jong Un ya kai wata ziyara a Rasha.

  5. Gwamnatin Najeriya ta musanta sauya wa titin Murtala Muhammed suna zuwa Wole Soyinka

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, fb/Bola Tinubu

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa babu ƙamshin gaskiya a batun da ake yi na cewa ta sauya sunan babbar hanyar Murtala Muhammed Esxpress Way da ke Abuja zuwa Wole Soyinka Way.

    Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar yau Litinin, wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa ministan yaɗa labarun ƙasar kan yaɗa labaru, Rabiu Ibrahim.

    Sanarwar ta ce "Wannan gwamnati ba ta taɓa kawo tunanin sauya sunan Murtala Muhammed Express Way ba."

    Ta ce ta fitar da sanarwar ce domin fayyace gaskiya, bayan ganin wasu rahotanni da ke cewa an sauya sunan babban titin.

    Ta ƙara da cewa "a lokacin ƙaddamar da wani sabon titi ne ministan birnin tarayya, Nyesom Wike ya bai wa shugaban ƙasa shawarar sanya wa sabon titin sunan Wole Soyinka, inda shi kuma shugaban ƙasar ya amince da hakan".

    Sanarwar ta ce sabon titin shi ne hanyar da ta tashi daga Unguwar Katampe zuwa Jahi, wadda ta haɗa da babbar hanyar fita Abuja ta Kubwa, da ake kira Murtala Muhammed Expressway.

  6. Za a fitar da jadawalin gasar Firimiyar Ingila

  7. Majalisar Dattijan Najeriya ta soki jihohi kan rashin kyakkyawan shirin aikin hajji

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar dattijan Najeriya ta soki lamirin wasu jihohin ƙasar kan yadda suka gaza yin shiri mai kyawu a aikin hajjin da ke gudana yanzu haka a ƙasar Saudiyya.

    Ko a shekarun da suka gabata mahajjata sun sha kokawa kan matsalar masauki da na abinci, lamarin da ya rataya a wuyan hukumomin kula da mahajjata na jihohi.

    A tattaunawarsa da BBC, shugaban kwamitin kula da aikin hajji na Majalisar Dattijan Najeriya, Ali Ndume, ya ce sun damu matuƙa game da rashin kyakkywan makwancin mahajjata a filin Mina, inda aka samu cunkoso mai yawa.

    Ya ce: "Babbar matsalar da aka samu ta faru ne a filayen Mina da Arafat da kuma wajen jifa".

    Ya ƙara da cewa "lamarin ya jefa mutane cikin mawuyacin hali, sansanin da aka ba su akwai matsi, ya yi cunkoso ƙwarai da gaske".

    "Katifar da aka bai wa mahajjata ƙarama ce sosai kuma an harhaɗa su a matse...Inda wata cuta ta ɓarke da za a iya samun matsaloli sosai".

    Wannan na zuwa ne yayin da mahajjata a ƙasar ta Saudiyya suka koka kan zafin yanayi.

    Lamarin da ya yi sanadiyyar mace-macen maniyyata da dama.

    Ƙasar Jordan ta bayyana cewa alhazanta guda 14 ne tsananin zafi ya yi sanadiyyar rasuwarsu a ƙasar ta Saudiyya sa'ilin aikin hajjin na wannan shekara.

    A ɓangare guda, sanata Ali Ndume ya nuna damuwa kan yadda aka ajiye mahajjata a wuri mai nisa a Mina da kuma wajen jifan sheɗan.

    Ya ƙara da cewa hakan na nuna cewa an samu tangarɗa wajen shirye-shiryen aikin hajjin bana.

    Ya kuma alaƙanta waɗannan matsaloli ga jihohi, musamman na arewacin Najeriya waɗanda ke da mahajjata masu yawa, waɗanda ya ce ba su yi shirin da ya kamata ba.

    Sanata Ndume ya ce bayan kammala aikin hajjinna bana, kwamitinsa zai tattauna da hukumar alhazai ta Najeriya da kuma na jihohi domin ganin an hana faruwar irin haka a gaba.

  8. 'Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta fara bai wa 'yan Najeriya biza'

    ..

    Asalin hoton, Tinubu/Facebook

    Gwamnatin Najeriya ta ce Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa za ta ɗage haramcin bai wa 'yan Najeriya biza nan ba da jimawa ba.

    Ministan harkokin sufirin jiragen sama na Najeriya, Festus Keyamo wanda ya shaida haka a watan tattaunawa da wani mataimaki na musamman ga shugaba Bola Tinubu, Otega Ogra, da ke kan manhajar Youtube kamar yadda jaridar Daily Trust ta ce.

    Keyamo ya ce shugaba Tinubu ya cimma matsaya da shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Mohamed bin Zayed Al nahya a lokacin da ya kai ziyara ƙasar a watan Satumbar 2023.

    Sai dai kuma mista Keyamo ɗin ya ce duk da cewa Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun gindaya ƙarin wasu sharuɗɗa kafin ɗage hanin bayar da bizar, amma tuni Najeriya ta kammala dukkannin wasu stare-tsare da ke nuni da yiwuwar ayyana dage hannin daga UAE nan ba da jimawa ba.

    Ɗage wannan hani dai ana tsammanin zai janyo sauƙin tafiye-tafiyen ƴan Najeriya zuwa ƙasar ta UAE, ta hanyar huɗar kasuwanci da ci gaba tsakanin ƙasashen biyu.

  9. An samu ƙaruwar rashin tsaro a Najeriya a watan Mayu - Rahoto

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting ya fitar ya nuna cewa an samu karuwar rashin tsaro a watan Mayun 2024 da kashi 10.28 inda aka samu faruwar al'amura da ke nuna taɓarɓarewar tsaro sau 762, idan aka kwatanta ta watan Afrilun da ya gabata da al.amuran rashin tsaro suka faru sau 691.

    " Wattan Mayun 2024 ya gano yadda rashin tsaro ya ƙara ƙamari inda ya ƙaru da kaso 262.70 saboda samun ƙaruwar garkuwa da mutane. Ana kuma alaƙanta hakan ne sakamakon hare-haren ƴan bindiga a arewa maso yammacin ƙasar...." In ji rahoton.

    To sai dai rahoton ya nuna cewa duk da samun ƙarin matsalolin tsaro da aka samu a watan Mayun amma kuma an samu ragin yawan mace-mace a watan inda alƙaluman suka ragu zuwa 1090 daga 1097 a watan Afrilu.

    Hakan in ji rahoton na nuna raguwar mace-macen ne da kaso 0.64.

    Rahoton ya kuma lissafa jihohin da aka fi samun matsalolin da suka haɗa da Borno da Edo da Abuja da Kaduna da Katsina da Kogi da Kwara da Niger da Sokoto da kuma Zamfara.

    Daga ƙarshe rahoton ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ɗauki dukkannin matakan da suka kamata wajen ganin an kare dukiya da rayukan al'umma.

  10. Alhazai 14 ƴan Jordan sun rasu saboda tsananin zafi a Saudiyya

    ..

    Asalin hoton, EPA-EFE

    Aƙalla alhazai 14 ne ƴan ƙasar Jordan suka rasu sakamakon tsananin zafin rana kamar yadda jami'ai suka ce

    Ministan harkokin waje na ƙasar ta Jordan a wata sanarwa ya ce "ƴan kasarsa 14 ne suka mutu bayan fama da bugun zafin rana sakamakon matsanancin zafin rana da ake fuskanta, inda ya kuma ce akwai mutum 17 da har yanzu ba a san wurin da suke ba."

    Sanarwar ta kara da cewa ma'aikata sun bazama neman mutanen nasu da ba a gan su ba.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP da kungiyar agaji ta ƙasar Iran su ma sun tabbatar da rasuwar ƴan Iran ɗin guda biyar duk da dai ba su yi bayanin yadda suka rasu ba.

  11. ..

    Asalin hoton, Malawi govt

    'Yan sanda a Malawi sun ce ɗaya daga cikin jerin gwanon motocin da ke ɗauke da gawar mataimakin shugaban ƙasar, ta bi ta kan masu makoki da ke gefen titunan wani ƙauye tare da hallaka mutane huɗu.

    Rahotanni sun ce wasu mutane 12 sun jikkata, lokacin da akai hatsarin a lokacin da sojoji da 'yan sandan manyan mutane da ke raka gawar mamacin zuwa ƙauyen marigayi Saulos Chilima, wanda ya rasu a makon da ya gabata sanadiyyar haɗarin jirgin sama.

    Dubban mutane ne sukai layi a gefen hanya domin ganin akwatin gawar Mr Chilima tare da yin bankwana da shi.

    Nan gaba a yau Litinin ne za a binne Mr Chilima, kuma gwamnatin Malawi ta ayyana ranar ta yau a matsayin hutu ga ɗaukacin ƙasar.

  12. Tareni: Yadda Sakkwatawa ke sarrafa naman layya

  13. Za a iya yaƙar rashawa da cin hanci a Najeriya — EFCC

    ..

    Asalin hoton, EFCC

    Hukumar da ke yaƙi da rashawa da cin hanci a Najeriya, EFCC ta ce za a iya samun galaba a kan rashawa da cin hanci a ƙasar duk kuwa da irin ƙaruwar da yake yi.

    Sai dai shugaban hukumar Ola Olukayode ya ce hakan zai iya yiwuwa ne kawai idan har dukkanin masu ruwa da tsaki a fagen yaƙi da rashawa da cin hanci sun haɗa ƙarfi da ƙarfe.

    Mista Olukayode wanda ya bayyana hakan a wani saƙonsa na babbar sallah, ya ce sabunta ƙudurin yaƙar dukkannin nau'in yi wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa abu ne mai matuƙar muhimmanci.

    Shugaban ne EFCC ya ƙara da cewa "ƴan Najeriya ba su gaji rashawa da cin hanci kuma ba mu da wata matsala a matsayinmu na ƙasa."

    Daga ƙarshe Mista Olukayode ya buƙaci yan Najeriya da su yi amfani da darussan sallar Idi babba wajen gyara alaƙa da ubangiji ta hanyar kawar da rashawa da cin hanci.

    "Ya kamata mu rungumi darussan haƙuri da sadaukarwa da imani da kuma kyautata tsammanin ga Allah da Idi ke koyarwa."

  14. China ta zargin Philippines da lalata mata jirgi

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    China ta zargi jirgin ruwan Philippines da haddasa taho-mu-gama da nata jirgin a yankin tekun da suke taƙaddama a kai.

    A wata sanarwa da masu gadin tekun Beijing suka fitar, sun ce lamarin ya faru ne a kusa da Thomas Shoal a kudancin tekun ƙasarta.

    Yankin dai na daga ɓangaren da ke ƙarƙashin kasuwancin Philippines maras shinge, amma ƙasasshen biyu na yawan samun saɓani da ikirarin mallakarsa.

    A nata ɓangaren China ta daɗe tana mamaye yawancin kudancin tekun China, da yin watsi da hukuncin kotun duniya kan haramcin mallakarsa.

  15. Senegal ta shiga jerin ƙasashe masu arziƙin man fetir

    ..

    Asalin hoton, Faye/X

    Ƙasar Senegal ta bi jerin ƙasashen da ke da arziƙin man fetur a Afirka ta yamma, wani abun da ya nuna cewa tattalin arziƙin ƙasar na bunƙasa.

    A makon da ya wuce ne ƙasar ta fara haƙo man a karon farko bisa tsammanin samar da ganga 100,000 a kowace rana.

    Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye ya tabbatar wa da kasar cewa Senegal za ta amfana daga kuɗaden sayar da man da iskar gas kuma za a alkilta su.

    "Mun kafa wata gidauniya wadda jikokin-jikokinmu za su amfana." In ji shugaba Faye.

  16. Amurka ta tura wakili domin sasanta Hezbollah da Isra'ila

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani babban mai bada shawara a Fadar White House zai yi balaguru zuwa Isra'ila, domin ƙoƙarin yayyafa wa wutar rikicin da ke ƙoƙarin kunno kai, kan hare-haren da mayaƙan ƙungiyar Hezbollah na Lebanon ke kaiwa kan iyakar ƙasashen biyu.

    Ziyarar Amos Hochstein, na zuwa ne a daidai lokacin da sojin Isra'ilar suka yi gargaɗin yawaitar hare-haren da mayaƙan Hezbollah ke kai musu a ɗan tsakanin nan ka iya assasa rikici a yankin.

    Kakakin sojin Isra'ila, Daniel Hagari ya ce "ƙaruwar hare-haren da Hezbollah ke kaiwa ka iya shafar yankin baki daya."

    Tun harin da Hamas ta ƙaddamar kan Isra'ila a bara, Hezbollah da ke kai hari Isra'ila a matsayin goyon baya ga Falasɗinawa.

  17. Yau ne ake sa ran tsagaita wuta ta fara aiki a Gaza

    ..

    A yau ake sa ran taƙaitacciyar tsagaita wutar da sojin Isra'ila suka sanar a wasu titunan kudancin birnin Rafah za ta fara aiki.

    Dakatar da aikin sojin a wasu titunan kudancin Gaza mai nisan kilomita 14 a mashigar Karem Shalom da tel Sutan.

    Wani jami'in Unicef ya bayyana cewa "kwanaki uku da suka wuce karar bama-bamai da jirage marasa matuka kaɗai sun hana mutum sakat, ina ga kusan sama da watanni takwas da aka ɗauka ana yakin nan."

    Duk wani tsaiko da za a samu na hare-haren nan zai yi wa Falasɗinawa da yaransu daɗi.

    Firaiministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya soki wannan mataki. Amma duk da hakan, sojin Isra'ila ba su janye sanarwar ba, za kuma a shigar da agajin ne ta mashigar Karem Shalom.

  18. Sojojin gwamnati da dakarun RSF na gwabza faɗa a birnin El-Fasheer

    ..

    Wani babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya shaida wa BBC cewa halin da ake ciki a birnin El - Fasheer da ke Arewacin Darfur ya ƙazanta.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji gwamnati da dakarun RSF ke ci gaba da gwabza faɗa.

    Toby Harward ya ce ana samun ƙarin kashe-kashe da ƙona ƙauyuka da sakin bama-bamai ta sama.

    Wannan lamarin dai ya hana a shigar da kayan agaji yankin. Birnin Fashir shi ne kaɗai ya rage da ke ƙarƙashin ikon sojojin gwamnati a yankin Darfur.

  19. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da Sallah. Da fatan za a ci naman sallah bisa ƙa'ida domin gudun ɓacin rana. Yau ma mun dawo domin kawo muku bayanai da labarai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Afirka da ma sauran sassan duniya. Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi na kai tsaye. Mun gode.