Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 16/06/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    To Masu bibiyarmu a wannan ranar ta Babbar Sallah nan za mu yi sallama da ku.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan, Abdullahi Bello Diginza ke cewa a yi shagulgulan sallah lafiya

  2. Ƙungiyar JNIM ta ɗauki alhakin kisan gomman sojojin Nijar

    .

    Asalin hoton, .

    Ƙungiyar JNIM mai alaƙa da Al Qaeda ta ce ita ce ta kai harin bayan-bayan nan a arewa maso gabashin Burkina Faso, kusa da kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.

    A ranar Talatar makon da ya gabata ne dai wasu mahara suka far wa sansanin sojojin, inda suka kashe gomman sojoji.

    Rahotonni sun ce fararen hula da dama ne suka ɓac a lokacin harin.

    Kawo yanzu sojojin mulkin Burkina Faso ba su ce komai ba game da harin.

    Ƙungiyar ta JNIM ta wallafa wani bidiyo da ke nuna manyan makamai da harsasai masu yawa da ta ce ta ƙwace a lokacin harin da ta kai Mansila.

    Ta kuma fitar da wani bidiyon da ke nuna mayaƙan ƙungiyar a kan babura, inda suke harbin kan-mai-tsautsayi a wani ƙauye mai cike da gine-ginen ƙasa.

    A watan da ya gabata ne shugaban mulkin sojojin mulkin Burkina Faso, Kaptin Ibrahim Traoré, ya bayyana ci gaba da mulki har zuwa shekara biyar masu zuwa.

  3. Zuma ya zargi ANC da haɗa kai masu nuna wariyar launin fata

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Jacom Zuma

    Tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Jacom Zuma - wanda kuma shi ne shugaban sabuwar jam'iyyar MK ya zargi jam'iyyar ANC da haɗa kai da masu nuna wariyar launin fata.

    Mista Zuma na shaguɓe ne kan kawancen da ANC ta ƙulla da jam'iyyar DA mai hamayya a ƙasar ranar Juma'a.

    Yayin da yake karanta jawabin mista Zuma, mai magana da yawun jami'iyyar, Nhlamulo Ndhlela, ya ce a yanzu ANC ta zama matsala saɓanin matsayin da aka santa a baya na mai yaƙi da nuna wariya a Afirka ta Kudu.

    Mista Zuma ya ce ba gwamnatin haɗaka za a kafa a Afirka da Kudu ba, inda ya bayyana ƙawancen da cewa ''ƙawance ne da ke kare muradun fararen fata da aka ƙulla tsakanin DA da ANC da kuma Ramaphosa”.

    Kan haka ne ya buƙaci magoya bayansa su fito, su yi yaƙi da wannan mataki ta hanyar shirya zanga-zangar lumana ''Za mu yi fafutiƙa don ceto ƙasarmu daga hannun maƙiyan ci gabanta”, in ji shi.

    Ya kuma tabbatar da cewa lauyoyin jam'iyyarsa sun kammala tattara hujjojin da za su tunkari kotun zaɓen ƙasar don ta soke zaɓen.

    Tsohon shugaban ƙasar mai shekara 82 ya ce nan ba da jimawa ba jam'iyyar za ta fara halartar zaman majalisar dokokin ƙasar, bayan da ta ƙaurace wa zaman farko.

    Jam'iyyar MK ta samu kashi 12 na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen, inda ta samu kujeru 58 a majalisar dokokin ƙasar.

  4. 'Yan bindiga sun sace mutane masu yawa a Sokoto

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga sun kai hari ƙauyen Tudun Doki da ke yankin ƙaramar hukumar Gwadabawa a jihar Sotoko inda suka kashe mutum biyar tare da sace mutanen da ba a san adadinsu ba.

    Rahotonni sun ce 'yan bindigar sun far wa ƙauyen ne da tsakar daren ranar Sallah.

    Gwamnatin Jihar ta tabbatar wa BBC faruwa kai harin, inda ta ce an jikkata fiye da mutum 30 a lokacin harin.

    Jihar sokoto da ke arewacin ƙasar na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, inda 'yan bindiga ke sace mutane masu yawa a lokaci guda domin neman kuɗin fansa.

  5. Buhari ya nuna damuwa kan ƙaruwar yawan al’umma barkatai

    .

    Asalin hoton, Buhari Sallau/X

    Tsohon shugaban shugaban Muhammadu Buhari ya gargaɗin cewa yadda al'ummar ƙasar ke ƙaruwa cikin sauri ka iya zama matsala ga ƙasar matukar ba a ɗauki matakan da suka dace ba.

    Yayin da yake jawabi wa manema labarai a Daura jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi, tsohon shugaban ƙasar ya ce yawan ƙaruwar jama'a a ƙasar abin dubawa ne.

    ''Yadda al'umma ke ƙaruwa cikin sauri matuƙar ba a ɗauki mataki ba, zai kawo matsala ga al'umomi masu tasowa''.

    “Don haka akwai buƙatar gangamin wayar da kan al'umma kan wannan matsala, tare da buƙatar zuba jari a ɓangarorin ilimi da na lafiya.”

  6. Hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a faɗin duniya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nan wasu mata ne masallata a birnin Santabul na ƙasar Turkiyya.
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masallata a masallacin Taza Pir Mosque da ke birnin Baku na ƙasar Azerbaijan.
    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Waɗanen musulman sun gudanar da tasu sallar Idin a West da ke Landan
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nan kuma masallacin Jami ne da ke birnin Toronto, na ƙasar Canada
    ,

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nan ma wasu masallatan ne a masallacin Kebayoran Lama, da ke birnin Jakarta na kasar Indonesia.
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Masallacin Idi na Moskovsky Prospekt a birnin St. Petersburg na ƙasar Rasha, lokacin da suka gabatar da sallar Idin, wadda suke kira 'Kurban-Bairam' a harshensu
    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mata Musulmai a masallacin Idi na Sorumba Ranomeeto da ke Konawa ta Kudu a ƙasar Indonesia
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mata Musulmai a lokacin sallar idi a masallacin da ke tsakiyar Thailand
    .

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Ku koma gona ku noma abinci don sauko da farashinsa - Buhari

    .

    Asalin hoton, Garba Shehu/X

    Bayanan hoto, Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

    Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga al'ummar ƙasar su koma gona don noma abin da za a ci domin magance matsalar tsadar abinci a ƙasar.

    Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da ya gabatar wa manema labarai jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a birnin Daura da ke jihar Katsina.

    “Ina amfani da wannan dama wajen kira ga 'yan Najeriya su zama masu dogaro da kai. Mu koma gona domin noma abin da za mu ci,alamu sun nuna cewa za mu iya, wannan ba lokacin zama ba ne, duba da yadda farashin abinci ke tashin gauron zabbi'', in ji Buhari.

    “Mu riƙa sayen abubuwan da ake samarwa a ƙasarmu, gwamnatocin ƙasarmu sun yi shirye-shirye masu yawa na ci gaban ƙasarmu, kuma ina ƙarfafa wa mutane gwiwa, musamman matasa su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen gina ƙasarmu'', in ji tsohon shugaban ƙasar.

  8. Mahajjata na ci gaba da gudanar da ibadar Hajji

    ..

    Asalin hoton, Haramain/X

    Bayanan hoto, Hukumomin Saudiyya sun tsara hanyoyin da mahajjata za su bi

    Mahajjata na ci gaba gudanar da ibadojin aikin Hajji a ranar Babbar Sallah.

    A yau ne suka gudanar da Dawafin da ke cikin rukunan aikin Haji a birnin Makkah, bayan sun kwana a Muzdalifa tare da yin jifa a Jamrah.

    Alhazan za su sake komawa Muzdalifa inda za su yi wuni uku suna jifa a Jamra.

    Hukumomin Saudiyya sun gudanar da cikakken tsari ga mahajjatan ta yadda za su gudanar da ayyukansu ba tare da tasgaro daga cunkuso ba.

    Shafin Haramain ya ce akwai dubban jami'an tsaro da ke taimaka wa mahajjatan wajen ba su umarni dangane da hanyoyin da za su bi, domin aikin ya tafi ba tare da matsala ba.

    Mahajjata fiye miliyan 1.8 ne ke gudanar da aikin Hajjin a wannan shekara.

  9. An kashe sojojin Isra'ila takwas a Rafah

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila ta ce an kashe sojoji takwas, a lokacin wani samame a birnin Rafah da ke Kudancin Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ilan ta ce dakarun suna tafiya ne a cikin motar sulke a lokacin da wani bom ya tashi da su.

    Sai dai mayaƙan Hamas sun ce sun harba wata roka a kan motocin yaƙin Isra'ila, kuma sun yi ikirarin nasarar harin.

    Dakarun Isra'ila dai sun shafe makonni suna kai hare-hare a birnin Rafah.

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce an kashe mutane fiye da dubu 30 a Gaza, tun lokacin da aka fara yaƙin.

  10. Isra'ila ta sanar da dakatar da ayyukan soji a wasu sassan arewacin Gaza

    Isra'ila ta sanar da abin da ta kira dakatar da aikin soji na kowacce rana a wasu yankunan arewacin Gaza.

    A wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar, ta ce sojoji za su tsagaita ayyukansu tsakanin karfe 8 na kowacce safiya zuwa 7 na dare, a hanyoyin da suka dangana da Kerem Shalom zuwa titin Salah al-Din.

    Wannan na zuwa ne bayan sojin Isra'ila sun sanar da sunayen sojoji takwas da harin Hamas ya hallaka a kudancin Rafah.

    Kakakin sojin Isra'ila Daniel Hagari ya ce cikin waɗanda aka kashe akwai matakaimakin kwamanda Wasseem Mahmoud da sojoji bakwai da ke ƙarƙashinsa.

    Wani hari roka da aka harba wa motar sojojin ne a kan titin Tel Sultan da ke Rafah, ya haddasa mutuwar sojojin.

  11. Sarkin Saudiyya ya yi wa mahajjata barka da Sallah

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz - wanda shi ne shugaban masallan Harami - ya taya alahirin maniyyata murnar gudanar da aikin Hajji.

    Cikin wani saƙo da sarkin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ''Ina yi buku barka da wanna rana mai albarka ta Idin Babbar Sallah, ina fatan rahama da gafarar Ubangiji a gareku''.

    Sarkin ya kuma yi addu'ar Allah ya karɓi ibadun da mahajjatan suka gabatar domin neman yardarsa.

    ''Ina fatan Allah ya wanzar mana zaman lafiya da tsaro a ƙasarmu da addininmu da ƙasashen Larabawa da ma duka duniya baki ɗaya''.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    A jiya ne dai mahajjatan suka gudanar da tsayuwar Arfa, yayin da yau kuma suka gabatar da Dawafin da ke cikin rukunan aikin Hajji.

  12. Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Idi, Aminu Ado ya halarci Sallar Idi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya yi hawan Idi a Kano, bayan gabatar da sallar Idi a masallacin Shehu Tijjani da ke binin Kano, sakamakon tashi da aka yi da ruwan sama a birnin.

    Sarkin ya isa gidan Shattima kan doki tare da rakiyar ɗimbin magoya baya, inda a nan aka tsara zai gaisa da gwamnan jihar.

    Wakilin BBC da je Kano ya ce sarki Muhammadu Sanusi Na biyu fita sallar Idin ne ta duka hanyoyin da sarkin Kano ya saba fita bisa al'ada, sannan kuma ya dawo ta hanyoyin da aka saba.

    Sarkin na kan doki, sannan dawakan zage da raƙuma na biye da shi, sai dai babu mahaya kamar yadda aka saba gani a baya.

    Bayan ya gaisa da gwamna a gidan Shettima, sarkin ya zarce filin Ƙwaru, inda ya yi wa al'umma jawabi kafin ya shiga gidansa.

    Muhammadu Sanusi II ne ya jagoranci sallar Idi a masallacin - inda gwamnan jihar da sauran mukarraban gwamnati - suka halarta.

    A Gefe guda kuma sarki Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci Sallar Idi a gidan sarki na Nasarawa duk dai a birnin na Kano.

    .

    Asalin hoton, Waziri Photos

    Bayan Idar da sallar ne sarkin na 15, ya hau dokinsa, sannan ya koma gidan sarki da ke nasarawa tare da rakiyar dimbin magoya bayansa.

    A cikin makon da ya gabata ne dai rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta haramta hawan sallah a faɗin jihar bisa wasu dalilai da tace na tsaro ne.

    To sai dai gwamnatin jihar ta 'yan sandan ba su tuntuɓeta ba a lokacin da suka fitar da sanarwar.

  13. Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na bukukuwan Babbar Sallah

    ,

    Al'ummar Musulmi a faɗin duniya na gudanar da shagulgulan Babbar Sallah.

    A jiya ne da Mahajjata suka gabatar da tsayuwar Arfa a Saudiyya, inda yau kuma suke gabatar da Dawafi a ɗakin Ka'aba.

    A Najeriya a wasu sassan ƙasar an wayi gari da ruwan sama, inda a wasu wuraren aka yi Sallar Idin a masallatan Juma'a.

    Alal misali a jihar Kano da ke arewacin ƙasar gwamnan jijar Abba Kabir Yusus ya halarci sallar ne a masallacin Shehu Tijjani na kusa da masallacin Idi na kofar Mata.

    Yayin tattaunawara da BBC, Gwamna Abba Kabir ya yi kira ga al'ummar jihar su ci gaba da gudanar abubuwan da suka kamata na kaunar juna da inganta harkokin addini.

  14. Barkanmu da Salla

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da wannan rana ta babbar sallah, wadda aka fi sani da sallar layya.

    Abdullahi Bello Diginza ke muku fatan an yi sallah lafiya.

    Allah ya maimaita mana Barkanmu da shigowa shafin namu da zai kewaya da ku duniya don kawo muku irin wainar da take toyawa.