Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 18/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ina ce mashigar Hormuz, kuma me ya sa take muhimmanci?

    jirgin ruwa

    Asalin hoton, Reuters

    Tun bayan da Iran ta sanar da sake rufe mashigar Hormuz ƙasa da sa'o'i 24 bayan buɗe shi, sakamakon yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran ɗin, mutane na ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

    Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

    Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

    Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

  2. Iran ta musanta iƙirarin Trump na mayar da uranium ɗinta Amurka

    Iran ta musanta kalaman shugaban Amurka, Donald Trump cewa ƙasar za ta yi aiki da Amurkar don gano sinadarinta na Uranium da kuma mayar da shi Amurka.

    Wani jami'in Iran mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ya ce ba a ma taɓa kawo batun a tattaunawar da ake yi ba.

    A ranar Juma'a ne Trump ya yi iƙirarin cewa Amurka za ta yi aiki da Iran don gano duka sinadarin uranium na ƙasar domin tattara shi da kuma mayar da shi Amurka.

  3. Iran ta sake rufe mashigar Hormuz saboda toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke yi

    ..

    Asalin hoton, ..

    Rundunar sojin Iran ta ce ta sake rufe mashigar Hormuz saboda ci gaba da toshe tasoshin ruwanta da Amurka ke ci gaba da yi, kamar yadda kafofinyada labaran kasar ta Iran ta rawaito.

    Kamfanin dillancin labaran Fars da ke da alaka da dakarun juyin juya halin ƙasar, da kamfanin dillancin labarai na Iran Students da kuma kafar yada labarai ta kasar IRIB, sun rawaito wata sanarwa daga rundunar ta IRGC na cewa mashigin ruwan zai koma "irin yadda yake a baya", inda dakarun sojin za su ci gaba da tsare mashigar.

    A baya mun ga wasu jiragen ruwa na jigilar kaya zuwa hanyar ruwan - amma babu tabbas ko jiragen ruwan soji sun bi ta mashigar ba.

    Sanarwar da sojojin ta fitar ta zargi Amurka da "fashin teku", tana mai cewa "abin da ake rufe mashigar da Amurka ke yi" ya kai fashin teku.

    Tun d afarko Iran ta yi barazanar janye matakin da ta ɗauka na buɗe mashigar ga jiragen ruwa, matuƙar Amurka ba ta kawo ƙarshen takunkumin hana jiragenta wucewa da ta sanya a tekun gabas ta tsakiya ba.

    Sai dai Shugaba Donald Trump ya dage cewa matakin zai ci gaba da kasancewa har sai an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin baki ɗaya, yana gargaɗin cewa watakila ba zai sake tsawaita tsagaita wutar da ake ciki ba idan ta kare ranar Laraba.

  4. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hantsi.

    Abdullahi bello diginza ke muku lale maraba a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.