Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 23/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 23/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Dalilin da ya sa aka saki fursunoni 888 a Najeriya

    A

    Asalin hoton, Google

    Hukumi a Najeriya sun ce an saki mutum 888 da aka zarga da alaƙa da ta'addanci saboda gaza samun isassun hujjoji a kansu da kotu ta yi.

    Gwamnatin Najeriya ta ce daga 2017 an gabatar da mutum 1,743 daga lokaci na farko zuwa lokaci na shida na sauraren shari'ar da ake yi wa waɗanda ake zargi da ta'addanci da ake tsare da su a gidan yarin Kainji.

    Daraktan gabatar da ƙara na tarayya Mohammed Abubakar Babadoko ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau a Abuja.

    "An yanke wa mutum 742 hukuncin a duka tsawon wannan lokacin - yayin da aka ɗage sauraren ƙarar 92 daga cikin waɗanda ake tuhuma.

    "Idan na ɗauki abin daki-daki a watan Oktobar 2017, an yankewa mutum 50 hukunci an saki 203 yayin da aka ɗage sauraren ƙarar 28.

    "A watan Fabirairun 2018 an yankewa 203 hukunci aka saki 582 sannan aka ɗage sauraren ƙarar mutum 24.

    "A watan Yulin shekarar dai an yankewa 113 hukunci sannan 102 aka sake su - aka ɗage sauraren ƙarar 9.

    "A watan Disambar 2023 an saki mutum ɗaya da aka samu ba laifi sannan kuma an yanke wa 14 hukunci aka ɗage sauraren ƙarar 10.

    "A 2024 da muke ciki a watan Yuli an yankewa 125 hukuncin yayin da aka ɗage sauraren ƙarar 21. A dai shekar an yanke wa mutum 237 hukunci".

    Da haka adadin ya kai yadda aka bayyana a jumlace tun da fari.

  2. An yi kwana 272 ba a ɗauke wutar lantarki ba a Afrika ta Kudu

    c

    Asalin hoton, @GovernmentZA

    Gwamnatin Afrika ta Kudu ta ce an kwashe kwana 272 a jere ba tare da ɗauke wutar lantarki ba a Afrika ta Kudu - wanda wannan ne lokaci mafi tsayi da ƙasar ta yi ba tare da ɗauke wuta ba a ƙasar cikin shekaru biyar.

    Ministan Lantarki da makamashi na ƙasar Kgosientso Ramokgopa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayar da bayani kan nasarorin da aka samu a Pretoria, inda ya danganta nasarar da aka samu ga kamfanin samar da wutar lantarki na ƙasar Eskom.

    Rashin ɗauke wutar ba kawai samar da nutsuwa ya yi ba ya kuma haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasa.

    Wannan rashin ɗauke wutar lantarki ya sa gwamnati ta samu damar ajiye rand biliyan 16 daidai da dalar Amurka miliyan 870 in ji Ministan.

    An yi hasashen an samu ƙarin lantarkin daga kashi 55.4 a bara zuwa 62.5 a bana.

  3. Kotun Ƙolin Mozambique ta ce Daniel Chapo ya lashe zaɓen watan Oktoba

    A

    Kotun Ƙolin Mozambique ta tabbatar da nasarar ɗan'takarar jam'iyya mai mulki, Daniel Chapo a matsayin wanda ya lashe zaɓen watan Oktoba.

    Alƙalan sun yanke cewa Mista Chapo ya lashe kashi 65 na ƙuri'un da aka kaɗa.Babban abokin hamayyar Chapo,Venancio Mondlane da ya zo na biyu, ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen inda ya yi zargin an yi maguɗi.Iƙirarinsa ya haifar da hargitsi a ƙasar da ya janyo mutuwar mutum sama da 100 tare da jefa ƙasar cikin tangal-tangal.Mista Mondlane , da a yanzu yake gudun hijira saboda abin da ya kira barazana ga rayuwarsa, ya yi gargaɗin za a fuskanci tashin hankali idan kotu ta ƙi ba shi nasara a zaɓen.

  4. Bangladesh na son India ta miƙa mata Firaiminista Sheikh Hasina

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Bangladesh a hukumance ta nemi Indiya ta mayar mata da tsohuwar Firaiminista Sheikh Hasina domin ta fuskanci shari'a a ƙasarta.

    Sheikh Hasina ta tsere zuwa Indiya bayan wata gagarumar zanga-zangar adawa da gwamnati a watan Agusta.

    Indiya ta ce ta samu saƙon daga ma'aikatar harkokin wajen Bangladesh amma ba ta yi wani ƙarin bayani ba.Ƙasashen biyu na da wata yarjejeniyar miƙa waɗanda ake zargi da laifi.

    Firaiministar da aka hamɓarar na fuskantar shari'a da dama game da zarge-zargen laifukan cin zarafin bil adama da cin hanci da rashawa. Tuni dai ta musanta zarge-zargen da ake mata.

  5. Dalilan da suka sa Man City ke kwasar kaya a kakar bana

  6. An gano Matt Gaetz ya biya kuɗin yin lalata da mata

    A

    Asalin hoton, Trump

    Kwamitin ɗa'a na majalisar dokokin Amurka ya gano cewa zaɓin Donald Trump na farko na mutumin da yake son ya zama atoni janar Matt Gaetz, ya biya kuɗin yin lalata da mata da dama - ciki har da wata ƙaramar yarinya.

    Rahoton da aka daɗe ana dako da kwamitin ya fitar ya ƙarƙare cewa akwai hujja mai ƙarfi cewa Mista Gaetz ya saɓa dokokin ƙasa.

    Sai dai ya musanta aikata ba daidai ba kuma ya yi ƙoƙarin hana fitar da rahoton.

    Tsohon ɗan'majalisar ya ajiye aiki a watan Nuwamba.

    Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Trump ya zaɓi Mista Gaetz ya zama atoni janar ɗinsa wanda daga baya kuma ya janye.

  7. Bukayo Saka zai yi jinyar makonni 'masu yawa' - Arteta

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ɗanwasan gaba Bukayo Saka ba zai buga wasa tsawon "makonni masu yawa" saboda rauni a bayan gwiwarsa.

    An fitar da ɗanwasan na Ingila a wasan da Arsenal ta doke Crystal Palace 5-1, inda ya bar filin wasa na Selhurst Park da sanduna.

    Saka mai shekara 23 ya ci wa Arsenal ƙwallo tara kuma ya bayar aka ci 13 cikin wasa 24 da hya buga mata a dukkan gasanni.

    "Lamarin babu kyau," in ji Arteta. "Zai yi jinyar makonni masu yawa.

  8. An kama mutumin da ya kashe abokinsa bayan karɓar kuɗin fansa

    ...

    Asalin hoton, X/Nigeria Police Force

    Kwamishinan ƴansanda a jihar Delta da ke Najeriya, Olufemi Abaniwonda ya ce jami'an rundunar suk kama wasu mutane huɗu da ake zargin su da kashe wani mutum.

    Cikin waɗanda aka kaman har da asalin wanda ya kitsa kisan bayan ya damfari mutumin kudi naira miliyan 30 tare da karɓan kuɗin fansa naira miliyan 20 daga iyalin marigayin.

    Kwamishinan ƴansandan ya ce a ranar 8 ga watan Oktoban 2024 ne aka sanar da rundunar ƴansanda game da ɓatan marigayin mai suna Paulinus Okon, mai shekara 30 a duniya bayan ya bayyana wa iyalinsa cewa zai kai wa abokin nasa ziyara.

    Sai dai abokin ya je gidan su Paulinos yana tambayan inda marigayin yake, tare da bayyana wa iyalin cewa bai san inda yake ba.

    Daga baya ya buƙaci iyalin su bayar da kuɗi naira 500,000 da za a kai wa wani boka, wanda zai yi addu'ar gano abokin nasa.

    Daga baya ya sake komawa inda ya shaida wa iyalin cewa an yi garkuwa da Paulinus, sannan ya karɓi kuɗin fansa naira miliyan 20,715,000 domin karɓo shi.

    Sai dai an kama shi a lokacin da aka fara zargin cewa yana da hannu a ɓatar marigayin.

    Binciken da aka gudanar ya sanay an kamo wadanda ke da hannu a lamarin, inda ɗaya daga cikin su ya shaida wa ƴansanda cewa abokin ne ya kai marigayi Paulinus domin a kashe a rafin Orere da ke yankin Otokutu.

  9. Gwamnan Adamawa ya sanar da ƙirƙirar sabbin masarautu bakwai

    Adamawa

    Asalin hoton, Ahmadu Umaru Fintiri/Twitter

    Gwamnan Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya, Ahmadu Umaru Fintiri ya sanar da ƙirƙiro sabbin masarautu bakwai a jihar.

    Sabbin masarutun sun haɗa da masarautar Huba da ke Hong, da masarautar Madagali da ke Gulak, da masarautar Michika da ke Michika da masarautar Fufore da ke Fufore da masarautar Gombi da ke Gombi, da masarautar Yungur da ke Dumne, sai kuma masarautar Maiha da ke Maiha.

    A cewar gwamnan, sarakunan masarautun Huba da Madagali da Michika da kuma Fufore za su zamo masu daraja ta biyu, yayin da masarautun Gombi da na Yungur da kuma na Maiha an ba su sarki mai daraja ta uku uku.

    ''ƙirƙiro waɗannan sabbin masarautun na da nufin inganta matsayin masarautu wajen samar da zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaban jihar,'' a cewar gwamnan.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. CISLAC ta yi gargaɗi kan cushe a kasafin kuɗin 2025

    CISLAC

    Asalin hoton, @FMINONigeria

    Cibiyar rajin kyautata ayyukan majalisar dokoki da yaƙi da rashawa a Najeriyar wato CISLAC, ta yi kira da a guji yin cushe a kasafin kuɗin 2025, tare da kira ga gwamnatin tarayya ta tabbatar da kasafta kuɗaɗe kan abubuwan da ƴan ƙasar ke buƙata.

    A wata sanarwa da shugaban cibiyar, Auwal Ibrahim Musa (Rafsanjani), ya fitar, CISLAC ta ce cushe a kasafin kuɗi da kasafta kuɗaɗe masu yawa a ayyukan da ba su cancanta ba, bai dace ba, inda ya yi misali da kasafta wa ma'aikatar wasanni da ta Neja Delta kuɗaɗe waɗanda an riga an rufe su.

    Da take amfani da rahoton babban mai binciken kuɗi na bana, CISLAC ta bayyana wasu kuɗaɗe da aka cire da suka sha banbam, inda ta ce an cire sama da naira biliyan 197.72 domin wasu ayyuka a ma'aikatu tsakanin 2020 da 2021 ba bisa ƙa'ida ba.

    Cibiyar sai ta yi kira ga majalisar da ta yi nazarin kasafin kuɗin cikin mutunci da nagarta.

  11. Arewa ba cima-zaune ba ne a Najeriya – Ndume

    Ndume

    Asalin hoton, Other

    Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya ce yankin arewa ba cima-zaune ba idan ana maganar tattalin arziki.

    Ndume ya bayyana haka ne a wata sanarwa, inda ya ce kowace jiha ko yanki da ke ƙasar na buƙatar wani domin ci gaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Sanatan ya ce, "yankin Arewa ba zai taɓa zama cima-zaune ba ko mai dogaro da wani yankin saboda muna da arziki.

    "Waɗanda suke tunanin wai waɗannan ƙudurorin harajin arewa zai shafa, ba su fahimta ba ne. Dukkan wani mai ƙaramin samu a ƙasar sai lamarin ya shafe shi."

  12. Biden ya yi rangwame ga waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa a Amurka

    Biden

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Joe Biden ya yi rangwame ga fursunoni 37 daga cikin guda 40 da aka yanke wa hukuncin kisa a ƙasar, inda ya mayar da hukuncin zuwa ɗaurin rai da rai.

    A yanzu, mutum uku kawai da ke fuskantar hukuncin kisa a matakin tarayya su ne: mutumin da ya jefa bam kan masu tsere a birnin Boston da kuma mutane biyu waɗanda suka kashe masu ibada a wuraren ibada na Kiristoci da kuma na Yahudawa.

    A Amurka ba a cika yanke wa masu laifi hukuncin kisa ba a matakin tarayya, har sai a lokacin mulkin Donald Trump na farko.

    Amma a matakin jiha har yanzu akwai sama da mutum 2,000 a faɗin Amurka waɗanda ke jiran hukuncin na kisa.

  13. Gindaya sharuɗa kan tarukan raba tallafi zai sa a rage taimako - Obi

    Peter Obi

    Asalin hoton, Peter Obi

    Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya Peter Obi ya ce gindaya sharuɗa kan tarukan raba tallafi zai sa ƴan Najeriya da ƙungiyoyi su rage taimakon al'umma.

    Peter Obi ya bayyana haka ne bayan babban sufeto janar na ƴansandan Najeriya ya yi kira ga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da su riƙa sanar da ƴansanda tare da bin dokokin shirya taruka a duk lokacin da za su raba tallafi.

    Shugaban na ƴansanda ya bayyana hakan ne bayan turmutsutsu wajen rabon tallafi ya jawo asarar rayuwa da dama a ƙasar, wanda Obi ya ce hakan zai sa gwiwar mutane ta yi sanyi wajen taimakon al'umma.

    Tashar Channels ta ruwaito Obi yana cewa, "duk da cewa kashedin yana da muhimmanci, hakan zai a wasu su daina taimakon al'umma. Maimakon a ce dole mutane su nemi izini kafin su taimakawa mutane, zai fi kyau a ba su shawara su ɗauki matakan kauce wa turmutsutsun."

  14. Ƙasashen Sahel sun zargi Faransa da ECOWAS da yunƙurin hargitsa Nijar

    Ƙasashen Sahel

    Asalin hoton, Burkina Faso Presidency

    Ƙasashen ƙungiyar Sahel wato Burkina Faso da Mali da Nijar sun zargi ƙasar Faransa da shugabannin wasu ƙasashen Afirka ta yamma da yunƙurin kitsa kutse a Nijar domin hargitsa ƙasar.

    Ƙasashen waɗanda suke ƙarƙashin mulkin soji sun ce sun shirya dakarunsu domin jiran ko ta kwana.

    Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya karanta a tashar ORTM ta gwamnatin ƙasar a ranar Lahadi, inda ya yi gargaɗin cewa ba za su bari hakan ya faru ba.

    Diop ya ce Mali da Nijar da Burkina Faso sun yi watsi da wa'adin wata shida ECOWAS ta ba su na tantance kifewarsu daga ECOWAS.

    Wannan na zuwa ne kwana kaɗan bayan gwamnatin sojin Nijar ta zargi Najeriya da haɗa baki da wasu ƙasashen waje domin hargitsa ƙasar, zargin da Najeriya ta ƙaryata.

  15. Yadda Rasha ke kisan fursunonin yaƙi na Ukraine

  16. Turmutsutsu wajen rabon tallafi na nuna akwai talauci da yunwa a Najeriya - PDP

  17. Dole a tabbatar da ƙudurin haraji na Tinubu - Clark

  18. Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar shekara

  19. Dukkan makaman Syria za su dawo ƙarƙashin gwamnati - al-Shara