Najeriya ce ƙasa ta shida da ta fi fama da rashin tsaro a duniya
Wani rahoton ƙididdigar ta'addanci na duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta shida da tafi fuskantar "ta'addanci" a duniya, daga matakin na takwas a shekarun 2023 da 2024, kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.
Rahoton wanda aka fitar a ranar 5 ga watan Maris ya ce Burkina Faso ce ke kan gaba a matsayin ƙasa ta ɗaya, sai Pakistan, sai Syria.
Masu biye da su kuma su ne Mali da Jamhuriyar Nijar, sai Najeriya a ƙasa ta shida, sannan ƙasashen Somalia da Kamaru da DR Congo suna cikin ƙasashe 13 da rahoton ya bayyana.
Rahoton ya ƙara da cewa Najeriya ta fuskanci kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci guda 565 a shekarar 2024.