Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahima Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Najeriya ce ƙasa ta shida da ta fi fama da rashin tsaro a duniya

    Wani rahoton ƙididdigar ta'addanci na duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta shida da tafi fuskantar "ta'addanci" a duniya, daga matakin na takwas a shekarun 2023 da 2024, kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.

    Rahoton wanda aka fitar a ranar 5 ga watan Maris ya ce Burkina Faso ce ke kan gaba a matsayin ƙasa ta ɗaya, sai Pakistan, sai Syria.

    Masu biye da su kuma su ne Mali da Jamhuriyar Nijar, sai Najeriya a ƙasa ta shida, sannan ƙasashen Somalia da Kamaru da DR Congo suna cikin ƙasashe 13 da rahoton ya bayyana.

    Rahoton ya ƙara da cewa Najeriya ta fuskanci kashe-kashe masu alaƙa da ta'addanci guda 565 a shekarar 2024.

  2. MDD za ta kashe dala miliyan 110 domin tallafin ayyukan jinƙai

    MDD

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za ta ware dala miliyan 110 domin cike giɓin abin da ta kira katse tallafin da ake baiwa duniya ba tare da nazari ba.

    Sai dai a bayanin majalisar ba ta ambaci Amurka ba a cikin sanarwar da ta fitar.

    Sai dai ma'aikatan jinƙai suka bayyana cewa matakin gwamnatin Trump na dakatar da kashi 90 cikin 100 na tallafin da Amurka ke ba duniya ya haifar da mummunan yanayi a ɓangaren ayyukan jinƙai.

  3. Sudan na zargin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ɗaukar nauyin dakarun RSF

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Sudan ta maka Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a kotun hukunta manya laifukka ta duniya, ICC kan zarginta da goyon bayan dakarun RSF.

    Sudan ta ce ta gano UAE na da hannu dumu-dumu a yaƙin basasar ƙasar da ake gwabzawa tsakanin gwamnatin na Sudan da dakarun RSF, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

    Ƙasar ta ce akwai sa hannun sojojin na UAE a kisan kiyashin da aka yi wa mutane a garin Masalit.

    Sudan ta zargi ƙasar ta UAE da ba RSF tallafin soji da kuɗi da goyon baya a siyasance, inda ta buƙaci kotun ta hana ƙasar daga shiga al'amuran ƙasarta.

    Sai dai UEA ta musanta zargin, inda ta buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, wadda ta bayyana da mara tushe.

  4. Birtaniya ta cire wa bankin Syria takunkumi

    Syria

    Asalin hoton, AFP

    Birtaniya ta cire takunkumin da ta ƙaƙaba wa babban bankin Syria da wasu hukumomi sama da 20 na ƙasar.

    Gwamnatin Birtaniya ta ƙaƙaba takunkumin ne a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasar, Bashar al-Assad, wanda aka hamɓarar.

    Birtaniya ta ce an cire takunkumin a ɓangaren kuɗi da makamashi da sauran wasu ɓangarori masu muhimmanci.

    Sai dai gwamnatin ta ce ba a cire takunkumin hana tafiye-tafiye da aka saka wa wasu jami'an gwamnatin al-Assad ba.

    A watan jiya ma tarayyar turai ta cire wasu takunkumi da ta sanya wa ƙasar ta Syria.

    Sabuwar gwamnatin dai tana ta ƙoƙarin nuna wa ƙasashen duniya cewa ba jihadi ta zo yi ba, inda take ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ce ta masu sauƙin ra'ayi.

  5. Ƴanbindiga sun kashe ƴan sa-kai biyu a jihar Jigawa

    Namadi

    Asalin hoton, Namadi/Facebook

    Ƴanbindiga sun kashe mutum uku, ciki har da jami'an tsaron Najeriya biyu a wani da suka kai a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Jigawa ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙaramar hukumar Ringim a jiya Laraba da marece.

    Hukumar ta ce ƴan bindigar sun buɗe wa wasu jami’an sa-kai masu yaƙi da masu garkuwa da mutane wuta a ofishinsu.

  6. IMF ya buƙaci gwamnatin Najeriya ta ɓullo da hanyoyin rage raɗaɗin talauci

    IMF

    Asalin hoton, AFP

    Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya roƙi gwamnatin Najeriya da ta fito da wasu hanyoyin samar wa al’umma yadda za su rage tasirin raɗaɗin da suke ji sakamakon matakan da ta ɗauka domin inganta tattalin arzki.

    A cewar IMF duk da matakin da gwamnatin ta ɗauka na cire tallafin man fetur ya zama wajibi, amma kuma ya haifar da wahalhalun rayuwa ga ƴan Najeriya da dama.

    Bankin lamunin ya ce a yanzu tsananin talauci a ƙasar ya ƙaru ya zuwa kashi 47 a cikin shekarar 2024 da ta gabata.

  7. 'Amurka na ruguza tsarin tabbatar da daidaito a duniya'

    Ukraine

    Asalin hoton, Ukraine Army

    Jakadan Ukraine a Birtaniya, Janar Valerii Zaluzhny ya zargi Amurka da ruguza tsarin tabbatar da daidaito a duniya.

    Janar ɗin ya bayyana haka ne a daidai lokacin da yake magana a wani taron manema labarai a birnin Landan, tsohon babban hafsan tsaron Ukraine ɗin ya ce fadar white house tana shakku kan haɗin kan ƙasashen yammacin duniya.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa ƙungiyar tsaro ta Nato na cikin haɗarin rugujewa.

  8. Jami'ai daga Nijar da Mali da Burkin Faso na ziyara a Najeriya

    Jam'iai daga ƙasashe uku da ke fama da hare-haren masu ikirarin jihadi a yankin Sahel sun kai ziyara Najeriya domin tattauna ayyukan yaƙi da ta'addanci.

    Wannan ne karo na farko da jam'iai daga Burkina Faso da Mali da Nijar su ka kai ziyara a hukumance zuwa wata ƙasa da ke cikin ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, tun bayan ficewa daga ƙawancen a watan Janairu.

    Tawagar ta kai ziyarar ne cibiyar nazarin yaƙe-yaƙe ta ƙasa da ke Maiduguri a arewacin Najeriya, wani birni da ya sha fama da hare-haren ƙungiyar ta'addanci masu ikirarin jhadi na Boko Haram.

    Zuwa yanzu dai ba a san ko za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar soji ba.

    Ƙasashen uku na yankin Sahel sun kawo ƙarshen haɗakar soji da Faransa da Amurka, yayin da suka kuma ƙulla alaƙa da Rasha da China.

  9. MDD ta yi gargaɗin cewa Sudan na fuskantar barazanar ƙara rabuwa

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargaɗin cewa Sudan na fuskantar barazanar ƙara rabuwa saboda sabuwar yarjejeniyar da dakarun RSF da ƙawayensu suka sanyawa hannu na kafa gwamnatoci biyu a yankunan da ƴan tawayen ke da iko.

    Mambobin kwamitin sun ce wannan mataki zai ƙara ta'azzara yaƙin wanda zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane kuma ya janyo matsalar jinƙai mafi muni a duniya.

    Sun yi kira ga ɓangarorin biyu da ke yaƙi da juna su kawo ƙarshen tashe tashen hankulan su kuma nemi maslahar diflomasiyya.

    Yaƙin - wanda aka soma shekaru biyu da suka gabata - ya raba Sudan gida biyu, inda sojojin Sudan ke iko da arewaci da gabashi, yayin da dakarun RSF ke da iko da yankunan da dama na Darfur da ke yammaci da wasu yankuna da dama a kudanci.

  10. Barazanar Trump za ta sa Isra'ila yin watsi da yarjejeniyar tsagaita wuta - Hamas

    Hamas ta ce barazanar da Shugaba Trump ke yi wa ƙungiyar za ta ƙarfafa wa Isra'ila ficewa daga yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

    Ƙungiyar na mayar da martani ne kan kalaman Mista Trump a shafinsa na sada zumunta da ke cewa ko dai Hamas ta miƙa sauran waɗanda ta ke riƙe da su a Gaza da gaggawa ko kuma ta ɗanɗana kuɗarta.

    Hamas ta nanata cewa dole sai Isra'ila ta fara mataki na gaba na yarjejeniyar tsagaita wutar - wanda ya haɗa da Isra'ila ta janye daga Gaza.

    A karon farko fadar White House ta amince cewa Amurka na da hannu kai tsaye a yarjejeniya da Hamas.

    Majiya daga Masar na cewa an samu cigaba a ƙarshen tattaunawar daren laraba.

  11. Kwamitin ladabtarwa ya bayar da shawarar dakatar da Sanata Natasha

    ...

    Kwamitin ladabtarwa na majalisar dattijan Najeriya ya bayar da shawarar dakatar da sanata Natasha Akpoti daga majalisar bisa zargin karya dokar majalisar ta hanyar bata sunan daya daga cikin yayan majalisar.

    Wannan na zuwa ne bayan kusan mako biyu da aka kwashe ana zazzafar muhawara kan ruɗanin da ya shiga tsakanin sanatar da shugaban majalisar, Godswill Akpabio, lamarin da ya kai ga cewa Akpoti ta zargi shugaban majalisar da yunƙurin cin zarafinta ta hanyar lalata.

    Sauran matakan da kwamitin ya bayar da shawarar ɗauka a kan Natsha su ne:

    - Majalisar ta janye ko rage tsawon lokacin dakatarwar idan sanatar ta nemi afuwar majalisa a rubuce.

    Za a haramta mata shiga duk wasu hidimomin Majalisar daga ranar 6 ga watan Maris, 2025.

    - A rufe ofishinta a tsawon lokacin sannan ta mika duk wasu kayan majalisar da ke hannunta

    - A tsawon wata shida da za a dakatar da sanatar, za a haramta mata shiga harabar majalisar.

    - A dakatar da albashinta da na ma'aikatanda ke taimaka mata na tsawon wata shida na dakatarwar da aka yi mata. Sai dai wasu sanatoci sun buƙaci a sassauta wannan matakin, inda daga baya majalisar ta amince cewar za a ci gaba da biyan hadimanta albashinsu a tsawon lokacin dakatarwar.

    - Kada ta bayyana kanta a matsayin sanata a tsawon wata shida na lokacin dakatarwar.

  12. Fasinjoji sun kama mutumin da ya shiga jirgi da bindiga a Australia

    Jirgin Australia

    Asalin hoton, Getty Images

    Fasinjoji da ke cikin wani jirgi a Australia sun yi nasarar fin karfin wani matashi da ya shiga jirgin ɗauke da bindiga.

    Rahotanni na nuna cewa matashin mai kimanin shekara 17 ya shiga ne bayan ya tsallako ta wani shinge a filin jirgin sama na Avalon da ke kusa da Melbourne.

    Bidiyon da aka wallafa a shafukan intanet na nuna lokacin da ma'aikatan jirgin suka buge bindigan daga wurin yaron.

    Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ne ya riƙe shi ta kai har lokacin da jam'ian ƴansanda su ka iso.

  13. Koriya ta Arewa ta dakatar da shiga ƙasarta yawon buɗe ido

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Koriya ta Arewa ta dakatar da shiga ƙasarta yawon buɗe ido, matakin da ke zuwa ƙasa da mako biyu da ta amincewa rukuni na farko na baƙi daga ƙetare shiga ƙasar a karon farko bayan shekaru biyar.

    Kamfanonin da suka shiryawa mutane tafiya zuwa birnin Rason da ke arewa maso gabashin kasar - kusa da iyakar China - an shaida musu cewa an soke shigar mutanen kasar zuwa nan gaba.

    Gwamnatin Pyongyang dai bata bayyana dalilanta na daukar wannan matakin ba.

    Tun a farkon shekarar 2020, a lokacin annobar Korona ƙasar ta kulle iyakokinta daga masu yawon buɗe ido.

  14. Najeriya ta ƙara yawan man da take haƙowa - Rahoto

    Gangar man fetur

    Asalin hoton, Thinkstock

    Najeriya ta ƙara yawan man fetur da take haƙowa zuwa ganga 70,000 a kowace rana fiye da adadin da ƙungiyar OPEC ta sanya mata, kamar yadda nazarin kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nuna.

    A cewar nazarin, man da ƙasashe mambobin ƙungiyar OPEC - ta masu arzikin man fetur - su ka fitar a watan Fabrairu ya ƙaru, inda Iran ke kan gaba, duk da ƙoƙarin da Amurka ke yi na daƙile fitar da man.

    Najeriya ta ƙara adadin man da take fitarwa da ya zarce adadin da ƙungiyar ta ware mata.

    Ƙungiyar ta OPEC ta haƙo gangan miliyan 26 da 74,000 a kowace rana a watan da ya gabata, inda aka samu ƙarin ganga 170,000 a kullum idan aka kwantanta da watan Janairu, a cewar nazarin na Reuters.

    Ƙungiyar OPEC+ - wadda ta haɗa da ƙasashen OPEC da Rasha da sauran ƙawaye - na son rage yawan man da suke haƙowa a watan Maris sakamakon hasashen raguwar buƙatar man da kuma wayan fitar da man daga ƙasashen da ba sa cikin ƙungiyar.

    To sai dai a ranar Litinin, ta yanke shawarar dakatar da shirin nata, inda take sa ran ƙara yawan man da take haƙowa a watan Afrilu.

    Nazarin ya gano cewa ƙasar Iran ce kan gaba a wajen haƙo man, inda take haƙo ganga 80,000 a kowace rana, a cewar nazarin Reuters.

    Fitar da ɗanyan mai daga Iran ya farfaɗo lokacin gwamnatin tsohon shugaban Amurka, Joe Biden duk da takuntuman Amurka, sai da ƙarkashin shugaba Donald Trump, Amurka na sabunta ƙoƙarinta na katse fitar da man baki-ɗaya.

  15. Zargin Natasha: Me zai faru da Akpabio idan aka kama shi da laifi?

    ...

    Asalin hoton, FB/Godswill Akpabio

    Wani tsohon ɗan majalisar dattijan ƙasar Sanata Bala ibn na-Allah na ganin cewa zai yi wuya a kama Shugaban majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio da laifin da Sanata Natasha ta shigar na ya nemi yin lalata da ita saboda Sanata Akpabio ne ya naɗa kwamitin binciken.

    Ya ce bisa doka bai kamata a ce wannan kwamitin ne zai yi binciken ba, inda ya ce a majalisu na wasu ƙasashen duniya, ana kafa kwamitin wucin gadi ne da zai haɗa da mai tsawatarwa na jam'iyya mara rinjaye, da mai tsawatarwa na jamiyya mai rinjaye, da shugabanni duk wata jamiyya da take majalisar wanda ake ganin su ne za su yi adalci.

    Sai dai sanata Bala ibn na-Allah ya ce idan aka bi ƙai'ida aka kafa irin wannan kwamitin kuma ya gano shugaban majalisar na da laifi, domin a ceto majalisar, ya kamata a kirashi ne a bashi shawarar ya sauka domin dawo da martabar majalisar da kuma maye gurbinsa da wanda ake ganin zai iya cigaba da shugabanci.

    Ya kuma ce idan kwamitin binciken ya kama Sanata Natasha da laifin yin kazafi, a doka za a dakatar da ita na wani tsawon lokaci, sai dai ya ce bisa wata shari'ah da akayi a baya wanda ya hana korar Sanata mai ci saboda hakan na nuna ''ba wai shi aka kora ba, mutanen da ya ke wakilta aka kora'', inda ya kara da cewa saboda wannan hukuncin ba za iya korarta ba.

    Tshohon ɗan majalisar ya ce majalisa ta na da doka kuma kowani dan majalisa na da hakki, inda ya ce tun farko ya kamata a ce ta bayyana korafinta a gaban majalisar kafin ta fita waje, wanda ya ce hakan kamar 'riga malam massalaci ne' kuma hakan zai bata sunan majalisar.

  16. MDD ta ce za ta ware dala miliyan 110 domin cike giɓin tallafi a duniya

    Hukumar Unicef

    Asalin hoton, UNICEF

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za ta ware fiye da dala miliyan 100 domin cike giɓin abin da ta kira ''katse tallafin da ake baiwa duniya ba tare da nazari ba''.

    Hakan na zuwa ne sakamakon matakin gwamnatin Trump na kawo ƙarshen akasarin tallafin jinƙai da take bayarwa.

    Shugaban kula da harkokin jinƙai na Majalisar, Tom Fletcher ya ce buƙatun ƙasashen da ke fama da rikici, da sauyin yanayi da kuma matsin tattalin arziƙi suna nan ba su kau ba.

    A ranar Laraba rahotanni sun bayyana cewa ana rage adadin abincin da ake bayarwa a sansanonin ƴan gudun hijiran Rohingya a Bangaladesh, saboda rashin isassun kuɗi.

  17. Ƴansandan Kenya sun tsare ɗan siyasar adawar Sudan

    ƴansandan kasa da kasa

    Asalin hoton, INTERPOL

    Ƴansandan Kenya sun tsare wani ɗan siyasar adawa a Sudan bisa sammacin kamu na rundunar ƴansandan kasa da kasa wato Interpol.

    An tsare Yassir Arman ne a lokacin da ya iso Nairobi, a inda zai gudanar da tattaunawa kan yaƙin Sudan.

    Zuwa yanzu dai ƴansandan Kenyan ba su faɗi dalilin tsare shi ba, sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama na zargin gwamnatin Sudan da amfani da dokokin ƙasa da ƙasa wajen musgunawa ƴan adawa.

    A kwanakin baya ministan Shari'ah na Sudan ya sanar da cewa ya na bibiyar ƴan siyasa da ke kiran a kawo ƙarshen yaƙin da akeyi a koma mulkin farar hula, inda ya zarge su da aiki tare da dakarun RSF masu faɗa da sojojin Sudan.

  18. Sojojin Koriya ta Kudu sun jefa bam a coci cikin kuskure

    jirgin saman yakin koriya ta kudu

    Wasu jiragen saman yaƙin Koriya ta Kudu sun jefa bama-bamai takwas bisa kuskure kan wani yankin fararen hula a yayin wani atisaye.

    Kafafen yaɗa labaran ƙasar sun ce lamarin ya yi sanadiyyar jikkata mutume 15.

    Lamarin ya faru ne a birnin Pocheon, kusa da iyakarsu da Koriya ta Arewa.

    Rundunar sojin saman ƙasar ta ce tana bincike kan lamarin, kuma ta nemi gafara kan kuskuren, inda ta ce za ta biya diyya ga waɗanda abin ya shafa.

    Harin kuskuren ya lalata wani Coci da wasu gidaje a yankin.

    Rundunar ta ce matuƙin jirgin ne ya yi kuskure wajen sanya bayanan kai harin wanda ya sa bama-baman suka sauka a yankin fararen hula.

    Masu bincike na ƙoƙarin gano dalilin da ya sa jirgin yaƙin na biyu shi ma ya jefa bama-baman a cewar sojojin, inda su ka ce za su dakatar da duk wani atisaye da ake amfani da makamai.

    A yayin da tarkacen bama-bamai da ake amfani da su lokacin atisaye kan faɗa yankin fararen hula, ba su fiya jikkata mutane ba.

  19. Mutum huɗu sun mutu a harin da Rasha ta kai mahaifar Zelensky

    Ukraine

    Asalin hoton, State Emergency Service of Ukraine

    Jami'ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih - Mahaifar shugaba Zelensky.

    Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine.

    Wannan hari na zuwa ne sa'o'i bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta daina musayar bayanan sirri da Ukraine -- wanda haka zai kasance ƙalubale matuƙa ga Ukraine wajen iya daƙile hare-haren Rasha.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce masu aikin sa kai daga wata ƙungiyar bayar da agaji daga Amurka da Birtaniya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya.

    Hakazalika, an kai wasu hare-haren birnin Odesa wanda ya yi sanadiyyar jikkata mutum biyu da lalata manyan gine-gine biyu, kamar yadda gwamnan yankin, Oleh Kiper ya tabbatar.

  20. Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin Natasha

    Majalisa

    Asalin hoton, Nigerian Senate/X

    Kwamitin ɗa'a da ladabtarwa da sauraron ƙorafin jama'a na majalisar dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita.

    Kwamitin ya bayyana ƙorafin da cewa ''ya zo gaban kwamitin a mace'', saboda rashin bin ƙa'ida wajen shigar da shi.

    A yayin zaman sauraron ƙorafin, shugaban kwamitin Sanata Neda Imasuen, ya karanto doka ta 40 cikin dokokin majalisar dattijai, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha ta sanya hannu kan ƙorafin da kanta maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya lalace.

    Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su.

    Tuni dai shugaban majalisar Sanata Godswill Akpabio ya musanta zargin cin zarafin da ƴar majalisar ta shigar kansa.