Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahima Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Aisha Aliyu Jaafar

  1. Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

    Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar ta tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman a faɗin jihar.

    Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ftitar, ta ce tallafin - wanda ya ƙunshi rabon kuɗi - zai shafi masu buƙata ta musamman duka ƙananan hukumomin jihar.

    Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce tallafin zai shafi cibiyoyi 27 na masu buƙata ta musamman a fadin jihar.

    Gwamnan kuma yi kira ga waɗanda za su amfana da tallafin su bayar da haɗin kai domin kauce wa turmutsitsi a wajen raba tallafin

  2. Macron ya zargi Rasha da neman zame wa Turai ƙarfen ƙafa

    Shugaba Emmanuel Macron ya yi gargaɗin cewa Rasha na neman zame wa Faransa da sauran ƙasashen Turai ƙarfen ƙafa, kuma ya zama dole su dau matakai kan kare kansu da tsaro.

    A wani jawabi da ya gabatar kai-tsaye ta kafar tabalijin, Mista Macron ya ce dole ƙasashen Turai su shirya da kuma sa wa ransu cewa ba lallai Amurka ta cigaba da mara musu baya ko taimaka musu ba.

    Ya ce kada su naɗe hannu makomar nahiyarsu ta kasance a hannun gwamnatin Washington ko Moscow.

    Wakilin BBC ya ce yana ƙoƙarin wayar da kan 'yan ƙasarsa domin ƙara yawan kuɗaɗen da ake kashewa fannin tsaro, ƙara kuɗaɗen haraji da kuma tabbatar da zaman lafiya a nahiyar Turai baki ɗaya, musamman a wannan lokaci da suke shirin gudanar da babban taro kan tsaro a Turai.

  3. Trump ya umarci Hamas ta gaggauta sakin duka Isra'ilawan da ta ke riƙe da su

    Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Hamas ta gaggauta sanin duka sauran Isra'ilawan da take riƙe da su a Gaza.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, shugaba Trump ya yi barazanar cewa ƙungiyar za ta ɗanɗata kuɗarta muddin ta bijire wa umarnin nasa.

    Ya kuma yi kira ga Shugabannin Hamas su fice daga yankunan Falasdinawa.

    Haka kuma shugaban na Amurka ya gargaɗi al'ummar Gaza cewa za su rasa rayukansu muddin aka cigaba da amfani da su wajen riƙe Isra'ilawa a yankin.

    Wani jigo a Hamas ya shaida wa BBC cewa an tattauna kai-tsaye tsakanin wakilan Fadar White House ta Amurka da Jagororin Hamas a Qatar kan sakin sauran mutanen Isra'ilar da ke hannunsu.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a masu bin shafin kai-tsaye na BBC Hausa barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhmis.

    Sannunmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku kasance da mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara game da labaran namu