Ronaldo ya yi alfahari da ɗansa ya buga wa Portugal tamaula
Cristiano Ronaldo ya ce yana alfahari da ɗansa, wanda ya buga wa tawagar Portugal ta matasa ƴan kasa da shekara 15 tamaula.
Ɗan gidan Ronaldo ya shiga karawar a minti na 54 a wasan da Portugal ta doke Japan 4-1 a wata gasa a Croatia ranar Talata.
Yaron mai shekara 14 ya buga wasan, inda kakarsa, Dolores Aveiro itama ta kalli wasan jikan nata.
Ɗan Ronaldo yana takaleda a Al-Nassr ta Saudi Arabia.

Asalin hoton, Getty Images








