Yoro da De Ligt da Heaven ba su yi atisaye a Man United ba

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labarin wasanni kai tsaye daga sassan duniya daga ranar Laraba 14 zuwa 16 ga watan Mayun 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Ronaldo ya sake zama kan gaba a jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya

    Ronaldo

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A watan Disamban 2022, Ronaldo mai shekara 40 ya koma ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya

    Cristiano Ronaldo ya sake zama kan gaba cikin jerin ƴanwasan da aka fi biya a duniya.

    Shekara uku a jere kenan ɗan wasan na Portugal na samaun wanann matsayi, da fitacciyar mujallar nan da ke ƙiyasin dukiya ta Forbes.

    Mujallar ta ce sau biyar Ronaldo yana samun matsayin a sana'arsa ta ƙwallon ƙafa, inda ta ƙiyasta kudin da aka biya ɗan wasan da kimanin dala miliyan 275.

    Adadi kudin da ɗan wasa ɗaya ne a tarihi ya taɓa zarta su, wato ɗan wasan dambe ne duniya, Floyd Mayweathe, wanda a 2015 a ysamu kimanin dala miliyan 300.

    A watan Disamban 2022, Ronaldo mai shekara 40 ya koma ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a wani ciniki mai gwaɓin gaske.

    Mujallar ta ce ɗan wasan ya samu kuɗi sakamakon wasu tsarabe-tsarebe da yarjejeniyarsa ta ƙunsa da kuma wasu tallace-tallace da kuma yawan mabiya a shafukansa na sada zumunta, da a yanzu suka kai miliyan 939.

    Ƴanwasa 10 da aka bi biya a duniya a 2025

    • Cristiano Ronaldo, ƙwallon ƙafa dala miliyan 275
    • Stephen Curry, ƙwallon kwando, dala miliyan 156m
    • Tyson Fury, wasan dambe dala miliyan 146
    • Dak Prescott, ƙwallon ƙafa dala miliyan 137
    • Lionel Messi, ƙwallon ƙafa dala miliyan 135
    • LeBron James, ƙwallon kwando dala miliyan 133.8
    • Juan Soto, kwallon baseball dala miliyan 114
    • Karim Benzema, ƙwallon ƙafa dala miliyan 104
    • Shohei Ohtani, ƙwallon baseball dala miliyan 102.5
    • Kevin Durant, ƙwallon kwando dala miliyan 101.4
  2. Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta fitar da jerin masu horaswa mafi bajinta a bana

    Masu horarwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta zabi masu horarwa biyar da za su iya lashe kyautar wanda yafi bajinta a kakar wasa bana a gasar Premier League.

    Sun hada da Nuno Espirito santo na Nottingham Forest, da Arne Slot na Liverpool, da Vitor Pereira na Wolves, da Thomas Frank na Brentford, da kuma Eddie Howe na Newcastle.

  3. Nick Krygios zai buga French Open karon farko bayan shekara takwas

    Nick Krygios

    Asalin hoton, Getty Images

    Daga karshe, dan wasan Tennis Nick Krygios zai buga gasar French Open a karon farko bayan shekara takwas.

    Dan wasan na kasar Australia zai yi wasa tare da Jordan Thompson a gasar ta mutum biyu-biyu.

    Dan wasan ya yi fama da munanan raunuka a baya bayan nan, lamarin da ya hana shi buga wasanni da dama.

  4. Vardy zai yi ban kwana da Leicester a ƙarshen wannan makon

    Vardy

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Leicester City Jamie Vardy zai yi ban kwana da kungiyar ranar Lahadin nan mai zuwa, inda zai buga wasansa na karshe wa kungiyar a karawarsu da Ipswich a gasar Premier League.

    Vardy ya shafe shekara 12 a Leicester, inda ya buga mata wasanni 500 , tare da zura kwallo 199 ya kuma lashe kofin Premier League a 2016.

  5. Son ya dawo taka leda bayan jinyar da ya yi

    Son

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham na farin cikin dawowar kyaftin din ta Heung min Son bayan ya gama jinyar raunin da ya ji.

    Koci Ange Postecoglu ya tabbatar da cewar dan wasan zai buga wasansu da Aston Villa gobe juma'a, sai dai bai bayyana ko zai fara wasan da shi ba.

  6. Real Madrid za ta ɗauki Huijsen kan fam miliyan 50

    Huijsen

    Asalin hoton, Getty Images

    Real Madrid za ta biya fam miliyan 50 kan dan wasan bayan Bornemouth Dean Huijsen.

    Tana sa ran dan wasan zai magance matsalolin ta take fuskanta a ɓangaren masu tsaron baya.

    An zura wa Madrid kwallo 38 a wasanni 37 a La Liga kaidai a bana, kuma yan wasanta na baya Alaba da Militao da Rudiger sun shafe tsawon lokaci a kakar wasan bana suna jinya.

    Tuni dai Huijsen ya nuna sha'awarsa ta taka leda a Madrid.

  7. Yoro da De Ligt da Heaven ba su yi atisaye a Man United ba

    Ɗan wasan Manchester United, Leny Yoro da Matthijs de Ligt da kuma Ayden Heaven ba suyi atisaye ba, bayan da ƙungiyar ke shirin buga wasan karshe a Europa League da Tottenham a makon gobe.

    Ranar Juma'a United za ta je Stamford Bridge domin karawa da Chelsea a Premier, amma dai hankalinta yana wasan da za ta kara ranar Laraba a birnin Bilbao.

    Yoro ya ji rauni ranar Lahadi a wasan da West Ham ta doke United 2-0, shi kuwa De Light a wasan Brentford ya ji rauni.

    Shi kuwa Heaven ya yi atisaye shi kaɗai, sai dai Jonny Evans da Toby Collyer sun yi atisaye tare da ƴan wasan United.

    Diogo Dalot ya motsa jiki shi kaɗai, wanda ke fatan buga wasan karshen, amma dai Lisandro Martinez da Joshua Zirkzee sun gama buga wasannin kakar nan, sakamkon jinya.

    Man United

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Za a fara kakar tseren Formula 1 ranar Lahadi

    Ranar Lahadi za a fara kakar tseren motocin Formula One a Imola, yayin da Lewis Hamilton zai fafata a karon farko a Italiya a matakin direban Ferrari ba na Marsandi ba.

    Ya yin da ɗan Italiya Kimi Antonelli zai fara tsere a gida a karon farko tare da Marsandi.

    Motar McLaren na fatan lashe tsere na shida a kaka bakwai, yayin da Lando Norris ke fatan rage tazararsa da Oscar Piastri a tseren da za a yi a Emilia-Romagna Grand Prix.

    Formula One

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Labaran da jaridu ke wallafawa kan cinikayyar ƴan ƙwallo

    Manchester United ce kan gaba wajen siyan Liam Delap, Nottingham Forest za ta sayi akalla 'yan wasa biyar a bazara, Arsenal da Liverpool na fafatawa kan Dean Huijsen.

    Manchester United ce ke kan gaba wajen neman dauko dan wasan Ipswich dan kasar Ingila Liam Deap, mai shekara 22, wanda zai yi farin ciki matuka da komawa Old Trafford a wannan bazarar. (Sky Sports)

    Nottingham Forest za ta sayi yan wasa akalla biyar a bazara, inda dan wasan tsakiya na Manchester City James McAtee mai shekaru 22 dan Ingila da dan wasan Ipswich Deap ke cikin wadanda suke nema. (Telegraph)

    Arsenal da Liverpool na zawarcin dan wasan bayan Bournemouth dan kasar Sipaniya Dean Huijsen, mai shekara 20, wanda kuma Real Madrid ke zawarcinsa. (Sky Germany)

  10. David zai bar Lille, domin buga gasar Premier League a badi

    Ɗan wasan tawagar Canada, Jonathan David zai bar Lille a karshen kakar nan, bayan da ƙungiyoyin Premier League ke son zawarcin dan ƙwallon.

    Mai shekara 25 zai bar buga gasar Faransa, wanda ƙwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan.

    Wadan de ke son sayen ɗan wasan sun haɗa da Liverpool, Chelsea, Manchester United da kuma West Ham, saboda rawar da ya taka a babbar gasar tamaula ta Faransa da ake kira Ligue 1.

    David ya ci kwallo 109 a wasa 231 a Lille - har da guda 25 a fafatawa 48 a kakar nan.

    Lille

    Asalin hoton, Getty Images

  11. An kammala sayen Reading

    Dan kasuwar Amurka, Todd Troscliar da Rob Couhig sun kammala sayen kungiyar Reading.

    Couhig ne zai mallaki kasho 75 cikin 100 na kungiyar da ke Ingila .

    A yanzu haka Reading ce ta shida a gasar football league 1, wadda rabonta da Premier tun shekarar 2012.

  12. An yi waje da Draper daga Italian Open, Kwallon tennis

    Wanda yake na ɗaya a ƙwallon tennis a Burtaniya, Jack Draper, ya yi ban kwana da Italian Open, bayan da Carlos Alcaraz ya caskara shi ya kuma kai daf da karshe.

    Draper, mai shekara 23, ya yi rashin nasara da ci 6-4 6-4 a fafatawar da suka yi a birnin Rum.

    Draper, wanda shi ne na biyar a ƙwallon tennis a duniya, shi ne yake cin 4-2 a zangon farko, daga baya Alcaraz ya sa ƙwazon da ya lashe fafatawar.

    Draper

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Yadda jaridu ke labarin cinikin ƴan wasa

    Huijsen yana mafarkin komawa Real Madrid, amma kungiyoyin Premier uku Liverpool, da Arsenal da Chelsea sun shirya tsaf don jawo hankalin dan wasan da a kan fam miliyan 50 don cimma yarjejeniyar a wannan watan. (Fabrizio Romano)

    Dan wasan Bayer Leverkusen na Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 24, yana dab da komawa Liverpool kan fan miliyan 29.5. (Mail)

    Real Madrid na dab da sanar da daukar matashin dan wasan baya na kasar Ingila Trent Alexander-Arnold mai shekaru 26 daga Liverpool. (ESPN)

    Manchester United ta tattauna da dan wasan gaban Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, kan yiwuwar komawa kungiyar Bournemouth. (Talksport)

  14. Kulusevski ba zai yi wa Tottenham wasan karshe a Europa League ba, Tottenham

    Tottenham ta ci karo da koma baya a shirin da take na buga wasan karshe a Europa League da Manchester United, bayan da aka yi wa Dejan Kulusevski aiki, sakamakon raunin da ya ji.

    Kulusevski ya ji rauni ranar Lahadi a karawar da Crystal Palace ta doke Tottenham 2-0 a Premier League, sakamakon karo da ya yi da Marc Guehi - daga nan aka sauya shi a minti na 19 da take leda.

    Kociyan Tottenham, Ange Postecoglou ya yi karin bayani da cewar ɗan wasan ya gama buga wasannin bana.

    Dejan

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Ko za mu ga Frimpong a Premier a Liverpool a baɗi?, Ƙungiyar Liverpool

    Jeremie Frimpong ɗan wasan da ke Buga Bundesliga ya lashe kofin kasar Jamus a bara har da German Cup a Bayern Leverkusen, ya ci ƙwallo 23 a wasa 133, wanda ake alakanta shi da Liverpool.

    Ɗan kwallon tawagar Netherlands ya taɓa taka leda a Manchester City yana da shekara tara daga nan ya koma Celtic, sai kuma Bayern Leverkusen ta mallake shi a Janairun 2021.

    Frimpong ya fara buga wa Netherlands tamaula a wasannin neman gurbin shiga Euro 2024 da suka kara da Faransa a 2023, an kuma sa sununsa cikin ƴan wasan da za su buga kofin duniya, amma bai buga gasar ba.

    Liverpool

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Yadda jaridu ke labarin cinikin ƴan ƙwallo

    Brighton na tattaunawa da tsohon dan wasan tsakiya na Ingila James Milner, mai shekara 29, kan sabon kwantaragi da kungiyar. (Athletic)

    Dan wasan Brazil Rodrygo, mai shekara 24, ba ya son sake buga wa Real Madrid wasa saboda yana shirin ficewa daga kulob din a bazara. (Marca Espanya)

    Arsenal na son dauko dan wasan gaban Sporting Lisbon dan kasar Sweden Viktor Gyokeres mai shekaru 26, wanda ya kulla yarjejeniya da kungiyar ta Portugal cewa zai iya barin kungiyar idan wata kungiya ta amince ta biya kusan fam miliyan 60. (Mirror)

    Kazalika bayan Gyokeres, Arsenal tana zawarcin dan wasan gaban RB Leipzig na Slovenia Benjamin Sesko, mai shekara 21. (Sky Sports)

  17. Ƴan Premier da kwalliya ta kasa biyan kuɗin sabulu a cinikinsu

    Yayin da wani lokaci akan samu sa'a a dace wajen sayen ƴan wasa a gasar Firimiyar Ingila, sau da dama kuma wasu ƙungiyoyin kan yi ɗaukar kara da kiyashi.

    Bari mu duba wasu daga cikin musayar ƴanwasa da aka yi rashin sa'a a gasar ta Firimiya.

    Premier

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Chelsea tana da masu buga wasannin aro da yawa a wasu ƙungiyoyin

    Ƙungiyar Chelsea tana da ƴan wasa da yawa da ke wasannin aro a wasu kungiyoyin ciki har da fitattunta 12.

    Jerin wasu da ke wasannin aro daga Chelsea a wasu ƙungiyoyin:

    • Kepa Arrizabalaga - Bournemouth
    • Djordje Petrovic - Strasbourg
    • Ben Chilwell - Crystal Palace
    • Axel Disasi - Aston Villa
    • Renato Viega - Juventus
    • Carney Chukwuemeka - Borussia Dortmund
    • Joao Felix - AC Milan
    • Andrey Santos - Strasbourg
    • Lesley Ugochukwu - Southampton
    • Armando Broja - Everton
    • Raheem Sterling - Arsenal
    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Chelsea za ta yi wasa biyu ba tare da masu buga gurbin cin ƙwallaye ba

    Chelsea za ta kara da Manchester United da Nottingham Forest a saura wasa biyun da suka rage, kamar yadda take fatan samun gurbin Champions League.

    To sai dai kuma tana fama da rashin ƴan wasan da ke buga gurbin masu cin ƙwallaye.

    An bai wa Nicola Jackson jan kati a wasan Newcastle, kenan an dakatar da shi wasa uku.

    Kenan Maresca sai dai ya nemo wani ɗan wasan da zai buga masa gurbin mai cin ƙwallaye a wasa biyun da suka rage mata a Premier League.

    Chelsea na fama da ƴan wasan da ke jinya a gurbin da ya haɗa da Christopher Nkunku da Jadon Sancho, wanda ba zai fuskanci United ba.

    Shima Marc Guiu na jiya, an dakatar da Mykhailo Mudryk, kan zargin shan abubuwan kara kuzarin wasanni.

    Enzo Maresca

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Lewandowski zai koma taka leda a wasan Espanyol, Barcelona da Espanyol ranar Alhamis a La Liga

    Ɗan wasan Barcelona, Robert Lewandowski zai koma taka leda ranar Alhamis a wasan hamayya da Espanyol a La Liga, kamar yadda koci, Hansi Flick ya sanar.

    Da zarar Barcelona ta ci Espanyol, za a ba ta kofin La Liga na bana na 28 jimilla a tarihi.

    Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki bakwai tsakani da Real Madrid ta biyu, kuma saura wasa uku-uku a kare kakar nan.

    Lewandowski bai yi wa Barcelona wasa uku baya ba, har da fafatawar El Clasico da Barcelona ta lashe Copa del Rey da cin Real Madrid 3-2 ranar 27 ga watan Afirilu.

    Mai shekara 36 ya ci ƙwallo 25 da tazarar biyu tsakani da Kylian Mbappe na Real Madrid, wanda ke kan gaba a yawan cin ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

    Robert Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images