Labarin wasanni daga 20 zuwa 26 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 13 zuwa 19 ga watan Satumbar 2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Donnarumma ya ce bai so barin Paris St German ba

    PSG

    Asalin hoton, Getty Images

    Gianluigi Donnarumma ya ce ya so ya ci gaba da zama a Paris St Germain, wanda ya koma taka leda a Manchester City a ranar da aka rufe kasuwar cinikayyar yan kwallo ta Turai ta bana.

    Mai shekara 26, wanda ya koma PSG daga AC Milan a 2021 ya taka rawar gani da kungiyar Faransa ta lashe Champions League a karon farko a tarihi a bara.

    Shi ne ya karɓi kyautar Yashin Trophy a matakin golan da ba kamarsa a kakar da ta wuce a bikin Ballon d'Or ranar Litinin a Faransa.

    Donnarumma, wanda ya lashe Ligue 1 da French Cup da kaiwa wasan karshe a Fifa Club Worl Cup kan fara kakar nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a Etihad har ya tsare mata raga sau biyu, ya kuma ce an yi masa tarbar girma a Etihad.

  2. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon dan wasan Manchester City Julian Alvarez, mai shekara 25, ya na son ya bar Atletico Madrid a bazara mai zuwa inda Liverpool da Barcelona na sha'awar dan wasan kasar Argentina. (Fichajes - in Spanish, external)

    Barcelona na son ta kulla yarjejeniya da Manchester United don siyan dan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, kan fan miliyan 26 wanda ya yi kasa da fan miliyan 35 wanda shi ne abinda United ke so , (Star, external)

    A wani labarin kuma, United ta maida hankali wajan daukar sabon gola a bazara mai zuwa (Sun, external)

    Real Madrid ta kalli yadda dan wasan bayan Arsenal William Saliba mai shekara 24, ya yi wasa a karawar da suka yi da Manchester City a ranar Lahadi kuma ta ci gaba, da nuna sha'awar siyan dan wasan na Faransa.(TBR Football, external)

  3. Har yanzu Vinicius bai buga wa Real Madrid minti 90 ba a bana

    Vinicius

    Asalin hoton, Getty Images

    Har yanzu Vinicius Jr bai buga wa Real Madrid minti 90 ba a wasa a kakar bana, karkashin Xabi Alonso.

    Tuni dai ɗan wasan Brazil ke cikin damuwa kan halin da ya tsinci kansa, koda yake Real Madrid ta fara kakar bana da kafar dama.

    Sau 10 ana canjin mai shekara 25 a wasa 12 karkashin Alonso, wanda ya karɓi aikin horar da Real Madrid a watan Yuni, bayan maye gurbin Carlo Ancelotti.

    Vinicius ya fara da dumama benci a wasa biyu baya har da a Champions League da Real Madrid ta yi nasara a kan Marseille a makon jiya.

    Real Madrid za ta je Levante a wasan mako na shida a La Liga ranar Talata, ita ce kan gaba a teburi da maki 15, bayan lashe dukkan wasa biyar da fara kakar nan.

  4. Sunderland

    Asalin hoton, Getty Images

    Sunderland ta tabbatar da cewar ɗan wasan da ta saya mafi tsada kan fara kakar bana, Habib Diarra zai yi jinyar watanni, sakamakon raunin da ya ji. an kuma yi masa tiyata.

    Ya ji rauni ne ranar Lahadi a gasar Premier League da Sunderland ta tashi 1-1 da Aston Villa.

    Sunderland ta ce tana sa ran ɗan wasan tawagar Senegal zai koma taka leda a tsakiyar watan Oktoba.

  5. Barau FC ta naɗa Dominic Iorfa a matakin janar Manaja

    Barau FC

    Asalin hoton, Barau FC

    Barau FC ta gabatar da Dominic Iorfa a matakin janar Managa, yayin da Alhaji Kabiru Baita zai yi masa mataimaki

    An batar da su ranar Litinin a gaban shugaba Shawwal Barau Jibrin..

    Kamar yadda sanarwa ta fita daga jami'in dake magana yawun ƙungiyar, Ahmad Hamisu Gwale ta ce sun fara aiki nan take.

    Barau FC za ta ziyarci Kun Khalifa ranar Lahadi a wasan mako na shida a gasar Premier ta Najeriya.

    Ƙungiyar Barau FC, ita ce kaɗai ba ta ci wasa ba, shi ya sa take ta karshen tebri ta 20 da maki biyu da ƙwantan wasa ɗaya.

  6. Barcelona ta buɗe Camp Nou don ganin gyare-gyare da take yi

    Barcelona

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Barcelona ta buɗe Camp Nou ranar Talata don ganin gyare-gyaren da take yi a filin wanda ta fara tun daga 2023.

    An zagaya da ƴan jarida cikin fili da kuma wajen zaman ƴan kallo da tuni ta gama aikinsu.

    Sai dai har yanzu ba a kammala aikin wajen sauya kayan ƴan wasa ba.

    Mahukuntan Barcelona sun ce za su nemi lasisin daga shugabanin birnin da zai ba ta damar buga wasanni a filin duk da ba a kammala wasu gyare-gyaren ba.

    An buɗe filin Camp Nou a 1957, sannan an bayar da aikin yi masa kwaskwarima tun 2023.

  7. Kane

    Asalin hoton, Getty Images

    Kyaftin din Ingila Harry Kane, mai shekara 32, zai iya barin Bayern Munich kan kudi fan miliyan 56.7 a bazara mai zuwa sai dai idan ya bayyana aniyarsa ta barin zakarun na Jamus kafin karshen lokacin bazara. Teamtalk, external)

    Tottenham na ci gaba da zawarcin dan wasan Manchester City Savinho, mai shekara 21, kuma watakila ta sake kulla yarjejeniya da dan wasan kasar Brazil a watan janairun (Teamtalk, external)

    Haka kuma Spurs ta shirya ta yi wa dan wasan Real Sociedad Brais Mendez mai shekara 28 tayin fan miliyan 35 don siyansa a watan Janairu. (Fichajes - in Spanish, external)

    Chelsea na son daukar dan wasan Manchester City Nico O'Reilly, ya yin da Leeds United da Bayer Leverkusen da kuma Lyon duk suna zawarcin dan wasan mai shekara 20 (Football Insider, external)

  8. Real Madrid za ta kara da Levante ranar Talata a La Liga mako na shida

    Mbappe

    Asalin hoton, Getty Images

    Za a ci gaba da wasannin mako na shiga a La Liga da za a yi karawa hudu ranar Talata

    • Athletic Club da Girona
    • Espanyol da Valencia
    • Sevilla da Villarreal da wanda
    • Levante da Real Madrid

    Tuni Real Madrid ta bayyana ƴan wasan da za su buga mata karawar karkashin Xabi Alonso.

    Ƴan wasan Real Madrid:Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Sergio Mestre.

    Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Alaba, Asencio, Á. Carreras, Fran García, Huijsen, David Jiménez.

    Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos.

    Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Endrick, Mbappé, Rodrygo, Gonzalo, Brahim, Mastantuono.

  9. Wasannin zagaye na uku a Carabao Cup

    Ranar Talata, 23 ga watan Satumba

    • Barnsley da Brighton
    • Burnley da Cardiff
    • Fulham da Cambridge
    • Lincoln da Chelsea
    • Wigan da Wycombe
    • Wolves da Everton
    • Wrexham da Reading
    • Liverpool da Southampton

    Ranar LarabaWednesday, 24 ga watan Satumba

    • Huddersfield da Man City
    • Newcastle da Bradford
    • Tottenham da Doncaster
    • Port Vale da Arsenal
  10. Noni Madueke zai yi jinyar wata shida zuwa takwas

    Madueke

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal na sa ran Noni Madueke zai yi jinyar mako shida zuwa takwas, sakamakon raunin da ya ji a wasan Premier League da suka tashi 1-1 da Manchester City ranar Lahadi a Emirates

    Ɗan wasan tawagar Ingila mai shekara 23, sai canja shi aka yi daga karawar bayan hutu, daga nan aka yi masa gwaje-gwaje, domin tantance girman raunin da ya ji.

    Wannan labarin koma baya ne ga Mikel Arteta da Thomas Tuchel, bayan da Madueke ya fara kakar bana da nuna gwaninta.

    Kenan idan zai dade yana jinya zai kai cikin watan Nuwamba kafin ya koma taka leda, kuma ba zai yi wa Arsenal wasu wasannin Premier League ba da na Champions League.

    Ɗan ƙwallon tawagar Ingila ba zai buga wa kasar wasa da Wales da Latvia ba da kuma karawar neman shiga gasar kofin duniya da Serbia da kuma Albania a cikin tsakiyar Nuwamba.

    Arsenal za ta fafata da Sunderland a gasar Premier League ranar 8 ga watan Nuwamba.

    Idan har Madueke bai warke da wuriba, watakila sai a wasan hamayya da Arsenal za ta yi da Tottenham a Premier League ranar 23 ga watan Nuwamba zai koma taka leda.

  11. Dembele ne gwarzon Ballon d'or na 2025

    Ballon

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan tawagar Faransa mai taka leda a Paris St Germain, Ousmane Dembele ne shi ne ya lashe ƙyautar Ballon d'Or ta 2025.

    Ya ci ƙwallo 35 da bayar da 16 aka zura a raga da lashe Champions League da French Cup da kai wa zagayen karshe a Fifa Club World Cup da Chelsea ta lashe.

  12. Aitana Bonmati ce ta lashe Ballon d'Or

    Ballon d'or

    Asalin hoton, x/Ballon d'Or

    Wannan shi ne karo na uku a jere da Aitana Bonmati ta lashe Ballon d'Or.

    Aitana Bonmati ta lashe kofin duniya da Champions League uku, yanzu tana da Ballon d'or uku, mai shekara 27.

    Waɗanda suka lashe Ballon d'Or karo uku a jere, Lionel Messi da kuma Michel Platini.

  13. Paris St Germain ce gwarzuwar ƙungiya a bara

    Paris-St Germain ce ta lashe ƙyautar gwarzuwar ƙungiya da ba kamarta a kakar da ta wuce.

    Ta lashe Champions League a karon farko a tarihi da Ligue 1 da French Cup da kai wasan karshe a Fifa Club World Cup, wanda Chelsea ta lashe.

    Ballon d'Or

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Arsenal ce ƙungiyar ƙwallon kafa ta mata mafi ƙwazo

    Arsenal

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta mata ta Arsenal ita ce gwarzuwa a kakar da ta wuce, wadda ta lashe Champions League a kakar da ta wuce.

  15. Pajor & Gyokeres sun lashe ƙyautar cin ƙwallaye

    Ballon d'Or

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴar wasan Barcelona, Ewa Pajor da ɗan ƙwallon Arsenal, wanda ya taka leda a Sporting a bara, Viktor Gyokeres suna suka lashe ƙyautar cin ƙwallaye a ƙungiya da tawaga.

  16. Kyautar mai tsaron raga da ba kamarsa

    Man City

    Asalin hoton, x/Ballon d'Or

    Gianluigi Donnaruma ne gwarzon mai tsaron raga a kakar da ta wuce a Paris St Germain yanzu yana Manchester City.

  17. Kyautar mai tsaron raga da ba kamarta

    Ballon d'Or

    Asalin hoton, x/Ballon d'Or

    Mai tsaron ragar tawagar Ingila, Hannah Hampton ce ta lashe ƙyautar Yashin Trophy

  18. Enrique ne ya lashe Johan Cruff Trophy

    Ballon d'Or

    Asalin hoton, x/Ballon d'Or

    Kociyan Paris St Germain, Luis Enrique ne ya lashe ƙyautar fitatcen kociya da ba kamarsa ta Johan Cruff Trophy.

    Bai samu halartar bikin ba, saboda PSG tana buga kwantan wasan Ligue 1 da Marseille.

  19. Wiegman ce ta lashe ƙyautar Johan Cruff Trophy

    Ballon d'Or

    Asalin hoton, x/ballon d'Or

    Kociyar tawagar mata ta Ingila, Sarina Wiegman ce ta lashe ƙyautar mai horar wa mace da ba kamarta a bara, kenan ta lashe Johan Cruff Trophy.

  20. Lopez ce ta lashe Kopa Trophy daga Barcelona

    Barcelona

    Asalin hoton, x/Ballon d'Or

    Matashiyar Barcelona, Vicky Lopez ce ta lashe ƙyautar matashiya ƴar kasa da shekara 21 da ba wadda ta kaita kokari - tana da shekara 19.