Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya -Talata 03/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye -Talata 03/12/2024

Taƙaitattu

  • Hukumar alhazan Kano ta nuna damuwa kan rashin sayen kujerun aikin Hajjin bana
  • Birtaniya na tsaka-mai-wuya kan zaɓin danganta da Amurka ko Turai idan Trump ya hau mulki
  • Manyan ƴantakara biyu da suka gwara kan ƴan arewacin Ghana
  • Sabon ƙudurin haraji ba zai soke wasu hukumomi ko talauta Arewa ba - Fadar Shugaban Ƙasa
  • Tudun Biri - 'Raina yana ɓaci idan na ga raunin ƴata'
  • Birtaniya na fama da hare-haren intanet - Hukuma
  • Trump zai hana cinikin sayar wa Japan kamfanin ƙarafa na Amurka
  • Yarjejeniyar Isra'ila da Hezbolla na iya rugujewa - Rahoto
  • 'Yansanda sun kama wani mutum bisa zargin satar yara biyar a Akwa Ibom

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad, Isiyaku Muhammad, Umar Mika'il

  1. Yarjejeniyar Isra'ila da Hezbolla na iya rugujewa - Rahoto

    Sojojin Isra'ila

    Asalin hoton, getty

    Akwai fargabar yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a Lebanon na iya rugujewa bayan da Isra'ila da Hezbollah suka kaddamar da hare-hare kan juna a jiya Litinin.

    Wakilin BBC ya ce Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wuraren Hezbollah a sassa daban-daban na Lebanon bayan ƙungiyar ta kai hari kan wani sansanin dakarunta.

    Ita kuma Hebollah ta ce ta kai harin ne bayan Isra'ila ta keta sharuɗɗan yarjejeniyar.

    A cewar ma'aikatar lafiya ta ƙasar Labanon, hare-haren da Isra'ila ta kai kan wasu ƙauyuka biyu sun kashe aƙalla mutum tara.

  2. 'Yansanda sun kama wani mutum bisa zargin satar yara biyar 'yan gida ɗaya a Akwa Ibom

    "yansanda tsaye na duba wata mota

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar 'yansanda ta jihar Akwa Ibom ta kama wani mutum bisa zargin satar wasu yara biyar 'yan gida ɗaya.

    Kwamishinan 'yansandan jihar, Joseph Eribo ne ya bayyana haka, jiya Litinin, a lokacin gabatar da wanda ake zargi mai suna Promise Boniface, tare da wasu tarin waɗanda ake zargi da aikata miyagun laifuka da aka kama.

    Jaridar Vanguard ta ruwaito an kama mutumin ne wanda ake zargin ya sato yaran daga wani gida a ƙaramar hukumar Obio Ibiono, bayan da haɗakar 'yan sanda da mutanen ƙauyen suka yi farautarsa.

    'Yansanda sun ce da ana bincikensa Boniface ya ce ya samu yaran ne suna gararamba sun rasa na yi a cikin ruwan sama sai ya ɗauke su.

    To amma kuma da aka matsa da bincikensa sai ya yarda cewa sato su ya yi, amma ya ce yanayin ayuwa ne ya sa shi haka, kuma wannan shi ne karon farko da ya taɓa yi.

    Kwamishinan 'yansandan ya ce tuni an damƙa yaran ga iyayensu cikin ƙoshin lafiya, kuma bayana kammala bincike za a gurfanar da mutumin d ake zargi da satar a gaban kotu.

  3. Sabon ƙudurin haraji ba zai soke wasu hukumomi ko talauta Arewa ba - Fadar Shugaban Ƙasa

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, Bola Ahmed Tinubu/Facebook

    Fadar shugaban Najeriya ta ce babu wani sashe na sabon ƙudurin haraji da ta gabatar ga majalisa domin samun amincewa da ya tanadi soke wasu hukumomi irin su TETFUND, da NASENI, da kuma NITDA.

    Haka kuma ta ce ƙudurin kamar yadda ake ta yaɗa maganganu ko alama ba zai jefa yankin Arewacin ƙasar cikin talauci ba.

    Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya bayyaa haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.

    Tun bayan da jam'a suka fara muhawara a kan ƙudurin a 'yan makonnin da suka gabata, 'yan siyasa da sauran masu sharhi na ta ɓoye gaskiya a kan ƙudurin, inda ya ce da gangan suke yaɗa ƙarerayi da kawara da jama'a daga fahimtar gaskiya a kan lamarin.

    Ya ce yawancin maganganun da ake yi na suka a kan ƙudurin ba ana yin su ne bisa wata ƙwaƙƙwarar hujja ba, illa shaci faɗi kawai.

    Onanuga ya ce yayin da wasu masu sharhin suka yi ƙoƙarin haifar da saɓani tsakanin jama'a da 'yan majalisar dokoki, wasu kuma sun raba kan ƙasar ne tsakanin wani sashe da wani.

    Kakakin ya ce ko alama wannan ƙuduri ba zai azurta jihar Lagos ko Ribas, ya kuma sa wasu sassan ƙasar su ƙara talaucewa ba kamar yadda ake yayatawa ba.

    Ya ce saɓanin wannan zargin ƙudurin zai taimaka ne wajen inganta rayuwar 'yan Najeriya, musamman ma masu ƙaramin ƙarfi.

  4. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Talata -03 ga watan Disamba, 2024.

    Ni Muhammad Annur Muhammad zan kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku yi muhawara

    A yi jimirin kasancewa da mu. Mu fara da wannan karin maganar - Shekara ba ta gadon shekara