Sai da safenku
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Talata.
Ku biyo mu don samun wasu sabbin labaran gobe da safe a wani shafin daban.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye -Talata 03/12/2024
Muhammad Annur Muhammad, Isiyaku Muhammad, Umar Mika'il
Nan za mu rufe wannan shafi na labarai kai-tsaye na ranar Talata.
Ku biyo mu don samun wasu sabbin labaran gobe da safe a wani shafin daban.

Asalin hoton, State House
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa ma'aikatar shari'a umarnin yin aiki tare da majalisar dokokin ƙasar wajen gyara abubuwan da mutane ke suka game da ƙudirin gyaran dokar haraji.
Ƙudirorin huɗu sun jawo suka iri-iri daga kowane lungu da saƙo na Najeriya, musamman arewaci, tun daga lokacin da aka kai su gaban majalisa domin neman amincewarta.
"Shugaba Tinubu na maraba da duk wani gyara da zai sauya duk wata saɗara da ke jawo cecekuce a ƙudirin," a cewar Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris cikin wata sanarwa a yau Talata.
Tuni rukunin 'yanmajalisa daga arewacin Najeriya suka ce sun yanke shawarar yin watsi da ƙudirin, wanda tuni ya tsallake karatu na biyu, a majalisar dattawa.
Amurka ta ce da damu matuka kan halin da ake ciki a Koriya ta Kudu.
Mataimakin sakataren harkokin waje Kurt Campbell ya ce kasarsa na sanya idanu a kan yanayin da ake ciki a Koriya ta Kudun, kuma suna fatan za a warware duk wani rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar cikin lumana.
A nata bangaren, Birtaniya ma ta ce tana nazari a kan halin da ake ciki a kasar tare da gargadin 'yan kasarta da ke zaune a can da su guji shiga duk wata tarzomar siyasa.
Ofishin jakadancin China a Seoul ya bukaci 'yan kasarsa da su zauna lafiya, su kuma kiyaye shiga abin da babu ruwansu.

Asalin hoton, Reuters
Koriya ta Kudu ta auka cikin wani rikicin siyasar da ba a fiya gani ba, bayan katsam shugaban kasar ya ayyana dokar soji.
Shugaba Yoon Suk Yeol na zargin 'yan hamayya da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa da aikata laifuka.
Sai dai kuma kasa da sa'oi biyu 'yanmajalisar dokokin kasar na jam'iyyar hamayya - wadda ke da rinjaye a majalisar - suka ki amincewa da matakin shugaban kasar.
Sun hallara a zauren majalisar inda suka kada kuri'ar da za ta dakatar da dokar.
Wasu daga cikin 'yan kasar da suka fusata da dokar sun haura shingayen da aka sanya yayin da wasu kuma suka tsallaka katanga don samun shiga cikin majalisar.
Sojojin Koriya ta Kudun dai sun ce za su tabbatar da umarnin shugaban kasar na amfani da dokar sojin har sai ranar da ya ɗage ta.
Dubban yan kasar Ghana na ci gaba da ficewa daga manyan birane zuwa garuruwansu na asali domin jefa ƙuri’unsu.
Sakamakon haka, ana samun karancin motocin sufuri da kuma cincirindon fasinjoji a tashoshin mota.
Lokacin da na ziyarci tashar Ghana Station da ke Kumasi - birni na biyu mafi girma a kasar - na lura da yadda tashar ta cika da fasinjoji da kayayyaki da ke dakon motocin da za su dauke zuwa garuwansu.

Asalin hoton, Reuters
Mataimakiyar shugaban kasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah, na dab da zama mace ta farko da za ta jagoranci kasar bayan zaben shugaban kasar da aka yi a makon da ya wuce.
Kawo yanzu ta samu fiye da kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kada.
Nasararta za ta kara bai wa jam'iyya mai mulkin kasar SWAPO damar ci gaba da jan ragamar kasar da ta fara tun shekarar 1990.
An samu matsaloli da dama yayin zaben, kama daga karancin takardar zabe, da dai sauransu abin da ya janyo har 'yan adawa suka fara zarge-zarge game da zaben.
Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta ce ba za ta amince da sakamakon zaben ba.
Ranar 3 ga watan Disamban 2023 ya kamata ta zamo ta farin ciki ga al'ummar Tudun Biri lokacin da suke bikin zagayowar Maulidi.
Sai dai wasu bama-bamai guda biyu da sojojin Najeriya suka jefa kan ƙauyen ya sauya batun.
Sama da mutum 83 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni.
Har yanzu mutanen ƙauyen na ƙoƙarin yadda za susake gina rayuwarsu bayan abin da ya faru.

Dubban yan kasar Ghana na ci gaba da ficewa daga manyan birane zuwa garuruwansu na asali domin jefa ƙuri’unsu.
Sakamakon haka, ana samun karancin motocin sufuri da kuma cincirindon fasinjoji a tashoshin mota.
Lokacin da na ziyarci tashar Ghana Station da ke Kumasi - birni na biyu mafi girma a kasar - na lura da yadda tashar ta cika da fasinjoji da kayayyaki da ke dakon motocin da za su dauke zuwa garuwansu.
“Za ni gida ne Tamale domin na jefa kuri’a, saboda zaben nan yana da matukar muhimmanci a gare ni," in ji Zainab - wata mata mai matsakaitan shekaru da ke sanye da rigar babbar jam’iyyar adawa ta NPP. "Idan ban je ba na cuci kai na."
Ta ce za ta je zaben ne domin taimakawa wajen samun canjin gwamnati a kasar sakamakon halin matsin da ta ce kasar ta shiga.
Amma wani magidanci mai suna Marwan Mustafa, ya ce zai niki gari har zuwa jiharsu ta North East ne domin jefa wa dantakarar jam’iyya mai mulki ta NPP ƙuri’a, "saboda ayukkan cigaba da gwamnatin ta yi musamman a yankunansu".
“A cikin ayyukan da suka yi, ɗana ya samu ilmi kyauta, ya gama makaranta har kuma an ba shi aiki," a cewarsa. "A da a garuwanmu babu hanyoyin mota, babu magudanun ruwa, amma yanzu duk an yi mana."
Bayanai sun nuna cewa tun kimanin mako uku da suka wuce ne aka lura da ƙaruwar kwararar mutane zuwa garuruwasu na asali domin yin zaben, wata manuniya ga yadda ‘yan Ghana suka dauki wannan zaben na bana da muhimmanci.
Wani abu da ya kara ba da gudunmuwa ga wannan ficewar shi ne yadda yan siyasa musamman daga manyan jam’iyyun NDC da NPP suke ɗaukar shatar manyan motoci domin jigilar magoya bayansu zuwa mazabunsu kyauta.
BBC ta yi nazari game da wani ɓangare na sabon ƙudirin dokar haraji da ke ci gaba da janyo zazzafar muhawara a tsakanin ƴan Najeriya.
Ga kuma bambancin tsarin raba harajin VAT na yanzu da kuma wanda ke cikin ƙudirin dokar da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa.

Asalin hoton, OTHERS
Majalisar dattawa ta amince da naɗin Laftana Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya.
Amincewar da majalisar ta yi yau ta biyo bayan nazarin rahoton kwamitinta mai kula da harkokin rundunar sojin ƙasa, wanda Sanata Abdulaziz Musa Yar’ adua ke shugabanta.
Majalisar ta amince da murya ɗaya shawarwarin da kwamitin ya bayar a rahoton.
Shugaba Tinubu ne ya naɗa Laftana Janar Oluyede, a matsayin mai riƙon muƙamin shugaban rundunar sojojin ƙasa sakamakon rashin lafiya da kuma rasuwar mai muƙamin, Laftana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja,.
A ranar Asabar, 7 ga watan Disamba ne za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasar Ghana.






Wasu rahotanni na cewa gwamnatin Taliban ta Afghanistan ta haramta wa ɗalibai mata a ƙasar karatun ungozoma da aikin jinya.
Daman karatun kula da lafiya shi ƙadai ne fannin da Taliban ɗin ta bar mata su yi a matakin gaba da sakandire.
Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ce ma'aikatar lafiya ta bayar da umarni ga manyan makarantun da ke koyar da aikin ungozoma da aikin jinya da kada su yi wa mata ɗalibai rijista.
An ga wasu hotunan bidiyo da ake ta sanya wa a shafukan sada zumunta da muhawara da mata manyan makarantu da dama da ke nuna ƙin amincewarsu da matakin.
'Yan mata da dama sun koma ɓangaren karatun kula da lafiya saboda hukumomin Taliban ɗin sun haramta musu shiga makarantun sakandire da jami'a.

Asalin hoton, NIGERIAN SENATE
Iyalan gidan marigayi Ado Bayero sun musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa sun ɗauke bikin ɗauren auren 'yarsu, Maryam Nasir Ado Bayero da ɗan mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Jibrin (Abba) Barau I Jibrin, saboda dambarwar da ta biyo bayan gabatar da ƙudurin harajin Shugaba Tinubu da aka yi a majalisar.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin tsare-tsaren bikin, na ɓangaren iyalan amarya, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba na Kano, ya fitar a jiya Litinin, ya ce an sauya wajen ɗaurin auren ne, daga Kano zuwa Abuja, ba don tankiyar da ƙudurin harajin ya janyo ba.
Alhaji Aminu ya kuma ce wannan shawara ce ta iyayen amarya ba wai ta iyayen ango ba, kamar yadda ake yaɗawa.
Ya ce kamar yadda al'adarsu ta tanada, aihakin iyayen amarya ne zaɓar rana da wajen da za a ɗaura aure ba iyayen ango ba.
Ya ƙara da cewa tun makonin da suka gabata aka sauya wajen ɗaurin auren da za a yi ranar Juma'a 13 ga watan nan na Disamba, domin sauƙaƙa wa manyan baƙin da suka nuna sha'awarsu ta halarta daga sassan ƙasar da kuma waje.

Asalin hoton, OTHERS
Shugaban hukumar alhazan jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ya nuna damuwarsa kan ƙarancin sayen kujerun aikin Hajji mai zuwa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Talata yayin wani taron haɗin gwiwa tsakanin ma'aikatan hukumar da da kuma manyan jami'anta na ƙananan hukumomi, a ofishin hukumar da ke Kano, kamar yadda wata sanarwa da kakakin hukumar Sulaiman A. Dederi ya fitar ta bayyana.
Alhaji Lamin ya buƙaci shugabannin hukumar na ƙananan hukumomi da su tashi haiƙan su ƙara azama wajen ganin an sayar da yawan kujerun da aka ware wa yankunansu.
Haka kuma ya yi kira da a samar da dabaru na bunƙasa cinikin kujerun da cimma aikin da ke gaban jihar a kan lokaci.
Hukumar alhazan ta sanya ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai kamawa, 2025, a matsayin ranar rufe karɓar kuɗin ajiya na aikin Hajjin na bana daga maniyyata a jihar.

Asalin hoton, Victoria Police
Hukumomi a ƙasar Italiya sun tasa ƙeyar wani mutum da aka daɗe ana nema ruwa a jallo bisa zargin kisan kai a Australia.
Ana zargin Perry Kouroumblis da hannu a kashe wasu mata biyu a shekarar 1977.
Suzanne Armstrong da ƙawarta Susan Bartlett sun mutu ne bayan an daɓa masu wuƙa a gidansu da ke Birnin Melbourne na kasar Australia.
Ba a dai gurfanar da Mista Kouroumblis ba amma dai ya dage kan cewa ba shi ya aikata laifin da ake zarginsa da shi ba
BBC ta yi nazari game da wani ɓangare na sabon ƙudirin dokar haraji da ke ci gaba da janyo zazzafar muhawara a tsakanin ƴan Najeriya.
Ga kuma bambancin tsarin raba harajin VAT na yanzu da kuma wanda ke cikin ƙudirin dokar da shugaba Tinubu ya gabatar wa majalisa.
Ya kamata ranar 3 ga watan Disamban 2023 ta zamo ta farin ciki ga al'ummar Tudun Biri lokacin da suke bikin zagayowar Maulidi.
Sai dai wasu bama-bamai guda biyu da sojojin Najeriya suka jefa kan ƙauyen ya sauya batun.
Sama da mutum 83 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni.
Har yanzu mutanen ƙauyen na ƙoƙarin yadda za susake gina rayuwarsu bayan abin da ya faru.

Asalin hoton, Downing Street
Firaministan Biritaniya ya dage cewa ba lallai ne ƙasarsa ta zaɓi tsakanin kusanci da Amurka ko Tarayyar Turai ba bayan Donald Trump ya hau mulki.
A wani jawabi da ya yi a birnin Landan Keir Starmer ya ce yana da matuƙar muhimmanci gwamnatinsa ta yi aiki tare da ƙawayen nata biyu.
Starmer ya ce batun cewa dole ne Birtaniya ta zaɓi ɗaya tsakanin abokanta, cewa tana tare da Amurka ko kuma Turai, ba daidai ba ne.
Ya ce ba zai taɓa amincewa da haka ba.
Akwai rade-radin cewa Mista Trump zai ƙaddamar da wani yaƙin kasuwanci da Tarayyar Turai tare kuma da rage goyon bayan da ake bai wa Ukraine lamarin da zai iya sanya Birtaniya a tsaka-mai-wuya

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar tsaron intanet ta Birtaniya NSCS, ta ce hare-haren da aka kai wa ƙasar ta intaet sun ninka sau uku a cikin shekarar da ta gabata.
A dangane da hakan ne, a yau Talata, sabon shugaban cibiyar zai yi gargaɗi kan hatsarin da ke tattare da kutsen na intanet da ake samu daga ƙasashen waje da kuma ƙungiyoyi masu aikata laifuka.
A jawabinsa na farko tun bayan karɓar aikin, Richard Horne zai buƙaci ƙungiyoyi da hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen kare kansu.
Hukumar da Mista Horne ke jagoranta, NSCS, ta ce yawan hare-haren intanet da aka kai Birtaniya sun ninka sau uku cikin shekarar da ta gabata.

Asalin hoton, OTHERS
Shugaban Amurka mai jiran-gado Donald Trump ya ce zai daƙile shirin saye kamfanin sarrafa ƙaraffa na Amurka (US Steel) da kamfanin Nippon Steel na Japan zai yi a lokacin da ya hau mulki.
A wani sako da ya wallafa a dandalin sada zumunta na Truth Social, Mista Trump ya ce ba ya goyon bayan yunƙurin sayar da kamfanin na Amurka ga wani kamfani daga waje.
Ya ce zai yi amfani da tallafin haraji don tabbatar da cewa kamfanin ya tsaya da ƙafarsa.
A watan Disamban bara, Nippon - wanda shi ne kamfanin sarrafa ƙarafa mafi girma na huɗu a duniya ya cimma yarjejeniyar sayen kamfanin US Steel a kan farashin dala biliyan goma sha biyar.